Sashe 68
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai ya yi tare da cize baki bai ce komai ba Didi dai tana lura dashi. AbdulHamid ne ya shigo ya ce, "Sun bada sallama, zamu iya tafiya gida." Omar ne ya mi e ya fita aka fara ha a kaya suka fito gaba aya. Sai da suka shiga mota har iyayen nasa sannan suka tafi a motar AbdulHamid. Omar shida Goje suka tafi dan gida zai wuce, a hanya ya ga wani baby shop sai yayi tunanin bai siyawa Didi da babyn komai ba ya zo ransa, nan take ya saka Goje ya tsayar motar suka shiga ciki. Duk abinda ya gani ya burge shi sai ya auka, a haka suka yi siyayya mai yawa suka biya ku in aka saka a bayan mota suka wuce gida. KRB3P038 Arewabooks@nanahaleema11. Nayla bata san Didi ta haihu ba, da safen bayan sun kammala breakfast suka wuce gidan Daddy kamar yadda ya ce su zo. Lokacin da suka je su Abba da Baba har sun zo aka zauna a falo ana tattaunawa akan batun Omar kafin a kira Nayla. Nayla gabanta fa uwa yake yi, ta shiga falon da sallama aka amsa ta nemi waje ta zauna. Daddy ya ce, "Hauwa kamar yadda na fa a a kwanakin baya, zamu bashi lokaci in ya zo da kansa zamu kar e shi mu tattauna, in bai zo ba zamu kai maganar kotu a raba auren. Jiya ya zo ya same mu, kuma mun gamsu da dukkan bayanansa. Kamar yadda na ce jiya yau zauna dake domin ki fa a mana abinda yake zuciyarki akan mijinki. Ya zo jiya har kun gaisa dashi, abinda nake so dake ki fa i abinda yake ranki babu wanda zai yi miki dole a cikin mu, kina da ra'ayin cigaba da zama dashi ko kuma a kashe auren kamar yadda ki ka ce da farko?." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba sai sunkuyar da kai da tayi, Abba ya ce, "kar ki cuci kan ki, ki fa i asalin abinda yake zuciyarki. Zaki iya cigaba da zama dashi matsayin mijin ko a'a?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "Abba a bani lokaci na yi tunani." Abba ya ce, "Lokacin me za a baki? Ba fa neman aurenki yake yi ba matarsa ce ke, kawai sai mu cigaba da ajjiyeki a gida da auren sa a kanki?." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba Daddy ya ce, "meyasa ki ke so a baki lokaci?." Nayla ta ce, "ina so na yi tunani ne." Abba ya ja tsaki ya ce, "ke ba wasan yara mu ka zauna yi a nan ba, mijin naki dan zaki koma masa sai kin yi tunani?. Kin ga malama ki tsayar da magana in zaki koma ki ce eh, in baza ki koma ba ki ce a'a, bana son shirme da ata lokaci." Mama Sa'adatu ta ce, "To Yaya Ali a bata damar tunanin mana, dan dai kwana biyu ai ba wani abun ba ne ba." Ya Harare ta ya ce, "Daman ai duk shirinki ne, har kin yanke ma kwana biyu ko?." Daddy ya ce, "A bata lokacin Ali. Mun amince an baki kwana biyun ki je ki yi tunanin ki dawo ki fa a mana." Abba ya ce, "Kai ka biye musu, tunanin me zata yi banda atawa kai lokaci?." Daddy ya yi murmushi ya ce, "yi ha uri ka yale su, tashi ki je Nayla." Ta mi e ta tafi a sanyaye. Abba ya bita da harara ya ce, "munafuka, tana son mijinta amma da yake ta samu goyan bayan uwar banza wai sai ta yi tunani, ko tunanin me zata yi ma oho." Mama Sa'adatu ta ce, "A bar mu mu yi abinda mu ke so, wancan lokacin ba mu samu damar yin kwalliyar amare ba, wannan mun samu sai abarmu mu yi ai. Kuma Yaya gaskiya ya kamata ayi mata lefe fa, yana da rufin asirin da zai iya yi mata lefe." Daddy ya ce, "Wannan ba dole ba ne ba ai, in yana da ra'ayi ya yi, in babu ni bazan ce ya yi ba saboda ba farilla ba ne. Kuma ko kayan dubu nawa zai siya mata kafin ya siya mata tana dashi, dan haka babu wani batun lefe. Gwajin jini kawai zai kawo min dan na tabbatar da lafiyarsa, itama kuma Nayla Khalid zai duba min nata dan tabbatar da lafiyarsu kafin ta koma gidansa." Hira dai suka cigaba da yi akan maganar kafin Abba da Baba su tafi. Nayla da ta shiga ciki babu awar hirarta Salma dan haka sai ta shiga aki tana danna wayarta. Kiran Didi ne ya shigo wayarta, ta auka da sallama suka gaisa Didi ta ce, "amaryar mu." Nayla tayi dariya ta ce, "Didi kina bani kunya." Didi ta yi murmushi ta ce, "Kin a fa." Nayla ta wara ido ta ce, "da gaske? Wai kin haihu kenan?." Didi ta ce, "na haihu Nayla, na haifi mace jiya da daddare." "Wayyo Allah na! Amma shine baki fa a min ba sai yanzu Didi?." "Yi ha uri, da yake cikin dare ne sosai sai yanzu da muka dawo gida na samu wayar har na kira ki." Nayla cikin farin ciki ta ce, "Gani nan zuwa yanzu Didi, gani nan" ta fa a tana kashe wayar ta fito falo. Mama ta kalla ta ce, "Mama Didi ta haihu, zan je gidanta." Mama da fara'a ta ce, "yaushe? Me aka samu?." "Mace, jiya da daddare." "Ma sha Allah, Allah ya raya ta." "Amin Mama. Ni zan tafi gidan." "Waye zai kai ki?." "Da kaina zan je." "A'a bara a kai ki, ki ce mata ina yi mata barka kafin nazo." Mummy ma sa on da ta bayar kenan, Nayla a guje ta fita driver ya auke ta zuwa gidan. Nayla a can ta tarar da su Mama Saroot sun ji da in ganinta, suna zaune sai ga matan su Kawu da cousins insu mata ana ta yi mata barka da haihuwa. Didi ta ji da in ha uwar iyalansu, tana ji ina ma Omar yana nan shima ya shiga cikin an uwa, amma ta san koda yana nan bazai zauna a wajan ba. Umma Saroot ce zata zauna da Didi a gidan kamar yadda ake yi. Babu wanda yake maganar Omar sai hira da suke yi, Nayla sai hoto take yiwa Babyn. Har yamma Nayla tana gidan, zuwa lokacin dangin Babansu Didi sun tafi saura Umma Saroot kawai wacce zata zauna da Didin a gidan. Umma Saroot ta shiga aki itama ya rage daga Didi sai Nayla a zaune sai babyn da take hannun Nayla. Didi bata yi mata maganar Omar ba itama bata yi mata ba, hira kawai suke yi kafin su ji ana buga gate. Nayla ce ta tashi ta je ta bu e, ganin Bashir ne da Goje sai ta yi dariya suka gaisa suka shiga ciki. Kaya suke ta shigowa da su Didi ta bisu da kallo ta ce, "wa annan fa?." Bashir ya ce, "Tiger ne ya ce a kawo miki." Didi tace, "Nayla bu e min na gani don Allah." Nayla ta bu e kayan ta ja su ta mi awa Didi tana fitowa dasu ta ga gaba aya kayan jarirai na mata a ciki. Didi ta ce, "wa annan kaya kamar za a bu e shago haka? Ku ku ka siyo?." Goje ya ce, "da kansa wallahi, tun a hanyar dawowa daga asibiti azu muka ga wani shago na siyar da kayan ya ce mu shiga. Duk abinda ya yi masa sai da ya auka." Didi ta ce, "Omar yana da matsala wallahi, wannan kayan Allah ka ai ya san nawa ya kashe" ta fa a tana jawo waya zata kira shi. Su dai sallama suka yi mata ta yi musu godiya tare da basu tukwici. in kar a suka yi, sai da ta nuna acin rai sannan suka kar a suka tafi. Umma Saroot da ta fito a lokacin ta kalle ta ta ce, "To Aisha meye matsalar dan ya yi miki wannan siyayyar?." Didi ta ce, "Umma kayan sun yi yawa sosai, kalli fa don Allah, kamar wacce take siyar da kaya? Bara na kira shi" ta fa a tana kiran wayarsa a karo na biyu. Umma Saroot ta ce, "saka a speaker ina son jin dramar ku." murmushi Didi tayi ta saka a speaker, daga can angaren yana auka ya ce, "Didi." Didi ta ce, "Omar an kawo min kaya." "Uhum na ata ne." "Amma Omar kayan nan sun yi...." Katse ta ya yi ya ce, "sun yi ka an ko? Daman ai ban gama ba." Didi ta ce, "ni ban ce sun yi ka an ba, ka san kana da abubuwa a gaban ka, ka manta maganar da muka yi jiya amma ka kwashe ka yi wannan siyayar da ku in?." Omar ya ce, "Haka na ce miki ku in na kashe? Kuma in ma su in na kwashe nayi laifi ne? Ke kan ki azu cewa ki ka yi Omar ga arka, kenan nayi laifi dan na siyawa ata abinda na fi arfinsa?." Didi ta ce, "ba laifi ba ne." Omar ya ce, "in ma a wajanki laifi ne a wajena ba laifi ba ne. ata ce kamar yadda ki ka ce, a karo na farko a rayuwata na samu wanda zai ce min Uncle ko ta ce min Baba, na samu wacce zan fa awa duniya ata ce babu wanda zai yi musu akan hakan. A ganina ko abinda na mallaka na kwashe na yi mata siyayya da su ban fa i ba Didi." Didi hawaye ya sakko mata ta goge ido ta ce, "Omar!." Jin maganarta na rawa ya ce, "wai kuka ki ke yi? Didi kenan, wahala bata ishe ki ba. Baki fara kuka ba kuwa, tunda har ki ka haifi ata wallahi yanzu ki ka fara kuka Didi." "Omar na gode, Allah ya ji an iyayen mu ya bar zumuncin mu har abada." "Amin Didi. Amma ni ba ke na yiwa ba balle ki yi min godiya, in kuma na kika sake yi min godiya kin nuna min ar tawa da kike fa a bai kai zuciya ba." "Bazan sake ba." "Ya fi miki dai. Amma da ki ka tashi addu'ar kin yi mantuwa,