← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 205

Sashe 70

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salma ta ce, "Barka." Kallon ta ya yi sarai kuma ya gane ta, da yar ya bu e baki ya bata amsa. Salma ta ce, "Mama ta ce ka shigo." Omar bai ce komai ba ya fita ya bi bayanta zuwa gidan. Salma sai gulmarsa take yi a zuciyarta har suka shiga cikin gidan. Yadda suka gaisa da Mama abin ya burge shi sosai itama ta saki fuska sun gaisa sosai, aka kawo masa ruwa da lemo da bowl wanda aka zubo cincin a ciki da kayan motsa baki. Ba jimawa Nayla ta shigo da sallama ya amsa ba tare da ya kalle ta ba, dan yana so ya yi mata warning akan fitar da take yi babu izininsa, in ya kalle ta tsaf zai kasa aikata abinda ya zo aikatawa. "Ina yini" Nayla ta fa a a sanyaye ba tare da ta kalle shi ba. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Baki tambayi waye ba amma kin fito, in da ba ni in bane ba fa?." Nayla ta ago ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba sai wani basarwa take yi fuskarsa a aure. Murmushi ta yi ta sunkuyar da kai ta ce, "Salma ta sanar dani." Omar babu walwala akan fuskarsa ya ce, "Meyasa ki ke fita ba tare da na sani ba?." Sai a lokacin ya kalli fuskarta ya ga abinda yake matu aukar hankalinsa akan fuskarta, yadda take kifta idanu kamar mai jin yaji a cikin idom, ganin motsawar idonta yana sakawa ya tsayar da idonsa yam a kanta. ago ido tayi ta kalle shi ta ga ita yake kallo, ya bu an idanunsa akan fuskarta ya ce, "meyasa?." Nayla ta sauke kai asa, ta daure ta jure dan tana son gwada yanayinsa ta ce, "har yanzu ai ban gama yanke hukunci zama da kai ba." Kai ya girgiza ya ce, "kafin ki yanke in har yanzu matata sunan ki, kinsan abinda zaki yi ai." Nayla tayi shiru bata ce komai ba. Omar ya zuba mata idanu dan gani ya yi ta ara yin kyau sosai, umarnin zuciyarsa kawai ya bi saboda ya kasa jurewa sai da yazo ya ganta, gashi ya zo sai wani shan hamshi take yi masa. "Yaushe zaki dawo?." Ba zata taji maganar kuma a hankali ya furta sai ta kalle shi ya aga mata gira alamun ina jinki. Nayla ta kawar da kai dan gaba aya fuskarsa babu walwala kamar ba shine ya je gidan Daddy yana murmushi ba. Nayla ta ce, "bana tunanin zan dawo saboda ka riga da ka gama cire min son zama da kai a zuciyata, gaba aya ka karya min zuciya." Kallon ta ya yi yana mamakin kansa, wai shine zaune a gaban wata mace tana fa a masa kalaman da ba su yake da ra'ayin ji ba. Lallai soyayya ta canja shi, abinda ta rage a halayensa ka an ne ya rage. Omar ya yi shiru bai ce mata komai ba, sai da aka an jima ka an sannan ya ce, "baki ha uri ba?." Ta aga kai ta kalle shi ta ce, "ha urin nake so na yi amma na kasa, tun daga ranar da ka je gidan Daddy baka sake koda nemana ba ta ya zan auka kalamanka na gaskiya ne?. Na kasa ha uri, ina so na ha ura amma zuciyata ta riga da ta....." Ha a ido suka yi sai ta kasa maganar ta auke kai daga kallonsa. Shi kam Omar bai san me zai ce mata ba kuma, tunda har tana aukar kalamansa na arya ne bai ga abinda zai mata wanda zata yarda ba, gwara kawai ya yi shiru kar ya furta abinda zai tarwatsa mata zuciya. Shiru ya sake ratsa tsakani kafin ya ce, "Kalaman nawa ki ke auka na arya? Kina tunanin zan zauna a gabanki na yi miki arya ne dan na burge ki ko dan ki dawo rayuwata?...Hmm." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba, ta ago ta ga ya zuba mata ido kawai yana kallon ta da alama ya rasa abinda zai ce mata. Shi kuwa acin rai yake ji a zuciyarsa, na farko tana fita bai sani ba, na biyu tana kallonsa tana cewa kalamansa na arya ne. Ba dan soyayyarta da yake ji a zuciyarsa ba da ku i aka ce ta fa a masa abinda ta fa a baza ta iya ba. Ya girgiza kai ya ce, "ba a haifi wanda zan yiwa kalaman arya dan na burge shi ba, haka ba a haifi wanda zan bawa hakuri ba tare da na san na yi laifi Ina so na gyara ba" mi ewa tsaye ya yi ya kalle ta ya ce, "ki yi tunani yadda ya kamata, ki yi tunani daidai da ra'ayinki da kuma abinda ki ke so. Abu aya zan sake maimaita miki bazan rabu da ke ba, amma in ki ka yanke hukuncin ki ka ji a zuciyarki kin gama zama dani zan yi abinda ki ke so" yana gama fa a mata haka ya fita dan ransa ya aci zai iya hargitsewa a gidan mutane gwara ya kama kansa ya bar gidam hakan zai fi alkaihri. KRB3P042 Arewabooks@nanahaleema11. Yadda Nayla ta shiga a sanyaye ya saka Jidda da Salma tambayarta abinda ya faru. Zama tayi akan gadon ta kalle su ta ce, "Na fa a mu ku kamar baya sona ma gaba aya." Salma ta ce, "ya taso ya zo gidan nan saboda ke kuma kice haka? Wai kin manta waye Omar in ne? A ganina tunda har ya zo zancen so ya kamata ki rufe shafinsa." Nayla ta ce, "gaba aya babu karsashi da zumu in son dawowata a gare shi, na auka zan ga yana zumu in na dawo amma sai naga ba haka bane." Jidda ta ce, "me ki ke so ya yi miki a gidan sirikansa?." Nayla ta ce, "Amma yadda ya yi min magana a gidan Daddy daban da yadda ya yi yanzu. Sai aure fuska yake yi, wai ina fita ba tare da izininsa ba." Salma ta yi dariya ta ce, "ko a nan baki fahimci soyayya bace ba kenan?." Nayla ta ce, "ni kuma na ce har yanzu ban gama yanke hukuncin zama dashi ba, na auka zan ga ya cigaba da bani ha uri sai na ga akasin haka. Domin kuwa cewa ya yi in na gama yanke hukuncin na sanar dashi zai yi abinda nake so." Salma ta ce, "Wallahi kina da matsala, yanzu meye na dawo da maganar saki kuma don Allah?." Jidda ta ce, "da kin sani kin bari komai ya wuce, dole ya ce miki haka ai Nayla. Duk da dai zhima ya kamata ya nuna miki soyayya a bayyane." Nayla ta ce, "gaba aya son komawar ma ya fita yake daga raina." Salma ta ce, "Sai ki yi ai." Nayla dai ta yi shiru bata ce komai ba amma gaba aya zuciyarta babu da Shi kam Omar da matu ar fusata ya koma gidan. Ya tsani maganar sakin nan, ko kusa baya so ayi masa zancen saki, amma shi yarinyar nan zata saka a gaba tana yiwa batun saki dan ta ga ma yana saurarenta. Ko gidan bai je ba, gidansu ya koma ya zauna yana huci shi ka ai. Masifar da take zuciyarsa yake so ya saukewa wani shiyasa kawai sai ya kira Didi. Tana auka ya fara masifa ya ce, "Wai me yarinyar nan ya auke ni ne? Tana fita duk inda take so ba tare da na sani ba, tana yin duk abinda ta ga dama da aurena a kanta. Yanzu ni take kallo tana sake yi min maganar saki, dan wai tana ganin na je har inda take ne ko? Ni za a rainawa hankali ko Didi? Dan kawai ina sonta ina kuma so ta dawo rayuwata shikenan kuma sai raini ya shigo ciki!?." Didi da take jin yadda yake masifa da mamaki ta ce, "Omar to ai ba ni ce Nayla in ba ko? Wannan masifa da ka ke yi min kamar ni ce Nayla in?." "Ai fa a miki ke yi, na gaji da aukar wannan abubuwan da yake faruwa, tana yin abinda take so ne saboda kawai ta samu dama daga wajena. Na kasa sarrafa kaina na kasa tsayawa akan matsaya guda aya, ko yaushe cikin unar rai nake da damuwa duk a kanta. Har fa a min take yi wai kalamaina ba na gaskiya bane, ita an fa a mata ina yin arya dan na burge wani? Ko kuma Ina arya ne dan wani yaji da i?. Ni ban ce ta karya min zuciya ba itace zata ce na karya mata zuciya? Ya yi kyau. Ki zama shaida, daga yau bazan sake maganarta ba, in ta ga dama ta dawo, in bata gama ba tai ta zama har a tashi duniya. Rabuwa da ita ne bazan yi ba, duk inda taje babu sanina kuma ita da Allah" ya fa a yana katse wayar a fusace tare da cilar da ita. Fusata yake ji da ita har a jininsa, gaba aya kansa ya kulle, zuciyarsa na bala'in bugawa sai girgiza kai yake yi shi ka ai yana cize baki cikin zallan takaici da ba in ciki. Ranar ko fita bai yi daga gidan ba, a ciki ya kai har dare. Sai daren ya an samu zuciyarta sassuta ya fita zuwa shago, amma babu walwala ko magana tsoron yi masa ake yi saboda yanayin fuskarsa. Bayan kwana biyu da maganar Nayla da Jidda da Salma suka fita su a lallai yawon siyyayar komawar Nayla suke. Ta layin gidan Didi suka zo wucewa kawai suka tsayar motar a ofar gidanta suka shiga. Tana zaune da Marmerh a hannu suka shiga ta da fara'a ce, "barkan ku da zuwa." Suka zauna Salma ta kar i Marmerh ya ce, "masha Allah, Didi Marmerh tana kyau wallahi, amma ni sai nake ganin fuskarta kamar ta Omar." Didi tayi dariya ta ce, "indai kin ga fuskarsa sai kin ga tawa. Sannan ku da zuwa." Jidda ta ce, "Yauwa Didi. Hanya ce ta biyo da mu muka shigo nan." Didi ta ce, "Sannun ku da zuwa, ku sha ruwa akwai abinci in zaku ci." Umma Saroot ce ta fito ta ce, "Nayla ku ne tafe." Nayla ta
Chapter 70 · 0% Book details