Sashe 26
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bu e ta dawo a hankali hannunta ri e da mug na tea ta zauna a kan kujera. Shiru taji bai ce komai ba hakan ya saka ta ago ido ta kalle shi sai ta samu kallonta yake yi kamar mai son gano wani abu a tare da ita. Suna ha a ido ya auke idonsa da sauri kamar irin wanda aka kama yana kallo ba tare da ya so an ganshi ba. Ajiyar zuciya ya yi ya ce meye ma sunan ki?. Jin abinda ya ce ya saka ta wara idanu bata san tayi ba tana bin fuskarsa da kallo jin rainin hankalin da ya yi mata. Wai meye ma sunan ki, ita yake kallo yake tambaya meye sunanta dan bata da matsayi da mahimmaci a wajansa? Tana matsayin matarsa amma ya tsareta yana yi mata irin wannan tambayar ta rainin wayo. Cikin aramin lokaci wannan nisha in da ta yini dashi ya gushe, ta ji babu da i a zuciyarta. Omar ganin tayi masa banza bata amsa ba ya ce, Bana tambaya na sake maimaitawa, ki ri e wannan. Nayla ta daure a hankali ta ce, Ai na ga ka san sunana shiyasa ban ce komai ba. Idanu ya fiddo waje yana girgiza kai yana ayyana lallai yarinyar nan ta fara raina shi, dan yana shiga lamarinta yanzu har ta samu damar fa a masa haka?. In less than two seconds ya koma Tiger na asali wanda ta sani, ya sake tamke fuska matu a a kausashe ya ce, Koma meye sunan naki bai dame ni ba, waye ya baki izinin bada talla a gidan tv?. Nayla tayi shiru bata ce komai ba, shima bai sake magana ba amma tana jin irin kallon da yake jifanta da shi a jikinta, tana jin kaifin idanunsa a jikinta kamar shigar allura cikin tsokar naman jikinta. Wannan yanayi da take ji ya saka ta ce, Babu kowa. Na ce miki ina da bu ata ne?. Baka ce ba. Meyasa ki ka yi?. Haka kawai ta bashi amsa a hankali dan wallahi a tsorace take, bata jurewa zama a inda yake ko ka an, yanzu sai ta fita daga nutsuwarta. Ba a yin abu haka kawai dole akwai dalili, meye dalilin?. Nayla kamar zata yi kuka ta ce, na fa a maka babu komai. Karya ki ke! Ya fa a kai tsaye ba tare da ya kalle ta ba. Nayla ta ji babu da i a zuciyarta musamman yadda ya aryata ta lokaci aya, ta kawar da kai a raunane ta ce, Nayi ne dan na taimakawa kasuwancinka ya sake zuwa inda ba a yi tunani ba, bayan wannan babu komai. Gira ya aga zuwa sama yana ta e baki ya ce, a matsayinki na wa kenan?. ago ido tayi a lokacin da suka fara tara hawaye ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba, kafin ta janye idanunta ya kalle ta suka ha a ido ta sake mayar da kanta gefe. Hawayen ya sakko kan kuncinta ta goge ta ce, A matsayina na ar uwarka musulma. Kuma kana matsayin Yayana, tunda anin Didi ne kai ta fa a a sanyaye. a ni bani da anwa a duniya, iyayenmu mu biyu kawai suka haifa daga ita sai ni, ba a lissafo ki a cikin wanda suka haifa ba balle ki zama anwata. Gwara ki barshi matsayin ar uwa ta musuluncin, amma ba wai Yayanki ba. Ya fa a da wata irin murya mai nuni da gaskiyar sa yake fa a mata. Nayla ta yi murmushin takaici bata ce komai ba, amma jin zuciyarta take tana bugawa sosai. Omar ya share ta kamar bazai yi magana ba kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce, ko ita Didin baki san sai da izinina take shiga abinda ya shafe ni ba, balle ke mai kalen ar uwarta ce?. Zuwa lokacin hawayen da take ri ewa ya fara sakkowa kan kuncinta. Omar ganin tana hawaye ya zuba mata ido yana kallonta cikin mamaki, to me yayi mata da zata yi masa kuka? Duka ko zagi ko cin fuska? Raini ne ko kuma wula anci?. Murya ya na rawa ta ce, Allah ya baka ha uri. Ke in ina magana dake kina yi min kuka wallahi wata ran sai na saka kin ha iye ha orin ki, sa an ki ne ni?!. Yadda ya yi maganar a kausashe ya saka ta kuma tsorata sosai ta tuna lokacin ha uwar su a gidan Didi. Ni dai ka yi ha uri kawai ta sake fa a murya na rawa sosai. Ya kalle ta ya ce, Ko nan gaba ba a shiga lamarina in ba ni na saka mutum ba, ki kuma fa a min ku in da kika kashe na biya ki. Nayla ta aga kai alamun gamsuwa ta ce, ni ba sai ka biya Ki fa a min ku Ya fa a a tsawace yana zare idanu. Nayla ta ce, .zan fa a. Sai nayi lissafi na manta. Bar nan!. Ai da sauri ta mike tazo wucewa ta inda yake zaune yana facing inta, tsabar tsoro afar center table in wajan ta jata tayi gaba ta fa a kansa da yake zaune akan kujera. Babu zato yaji fa uwar ta jikinsa, ya rutse ido da sauri tare da jan numfashi jin lafiyayyen hamshin da ya kai masa ziyara hancinsa ya kuma zagaya ko wanne sashi na jikinsa. Nayla kuwa bata banbance a ina take ba sai bayan ta fa o kansa in sannan ta gane halin da take ciki, da sauri ta mi e bata iya magana ba ta wuce ciki a guje. Lumshe idanu ya yi bayan ta bar wajan, sai kuma ya ja tsaki tunawa da rainin hankalin da tayi masa kafin ta bar wajan, da kuma daren da ta kai a waje ba tare da ya san inda taje ba. Nayla da tana shiga ciki ta dinga mita ita ka ai a zuciyarta, shayin da ta ha a ma ta barshi a falon kuma ba iya komawa zata yi ta sha ba. In ta tuna kalmarsa ta meye ma sunan ki yana sakawa taji babu da i, amma bata bar damuwar tayi mata tasiri ba ta yi kwanciyar ta duk da tana ta tuna abinda ya faru. Mamakin sa take yi sosai dan yanzu yana iya yi mata magana mai tsaho, duk da ba alkhairi ne yake ha a su ba amma yana yi mata magana har ya amsa gaisuwarta. Sannan bai cika yi mata magana a kausashe ba sai dai ya yi kamar yadda yake magana da Didi ba kamar farkon zamansu ba. Washe gari ma da ta tashi daga aiki saloon in jiya ta wuce aka yi mata black henna sannan ta shiga store tayi siyayya dan akwai abinda take so tayi. Tun daga wannan maganar bata sake ganin sa ba ma gaba aya, sai dai taji motsin bu ofa da rufewa amma bata sake jin koda muryarsa ba. Tana mamakin rashin amfani da kayan gidan da ba baya yi, hana rantsuwa ta san yana shan ruwa bayan wannan ko lemo bata ta a gani ya auka ba duk akwai a fridge sosai har da yourgut amma baya sha. Ranar ashirin da tara ga watan ramadan ana e gobe sallah kenan kasancewar lahadi ce tana gida a kitchen ta shiga tana ta aiki tun safe. Tayi abubuwa da yawa wanda hakan ya kawo mata gajiya matu a. Da yake da wuri ta fara zuwa biyar ta gama duk abinda take so. Bashir ta kira a waya ta ce ya zo gida zata bashi sa Bata san tare suka shigo da Omar ba ta fito da hijjabi tana cewa, Bashir ance min an kai sa o Kaduna jiya, ashe Maganar ta tsaya ganin sa tare da Omar da leda a hannun Omar in. Wani irin dumm ta ji a zuciyarta, dan tun ranar ashirin da bakwai bata sake ganin sa ba kwana biyu kenan yau. Tana so tayi masa sannu da shigowa tana tsoron kar ya yarfa ta a gaban Bashir, ta daure ta basar ta ce, Sannu da shigowa, Bashir Ina zuwa ta fa a a ha e tana komawa ciki ba tare da ta bashi damar amsawa ba. Kallon sa Omar ya yi alamun arun bayani, da sauri Bashir ya ce, Ta yi min waya ne ta ce na zo. Ta yi maka waya!? Ya maimaita zahiri ba tare da ya sani ba dan abin haka kawai ya daki zuciyarsa, wai tayi masa waya. Bashir ya amsa da, Eh, ita ta kira ni ta ce na zo. Bai sake magana ba ya share Bashir ya zauna ya bu e masa ledar da ya shigo da ita. Kaya yake sakawa yana ha awa waje aya yana ware takalma. Omar ya ce, auki wanda ki ke so gida biyu ko wanne. Bashir ya murmusa ya ce, Godiya mu ke yi Damisa, bayan kayan sallah da ku inki harda takalmi? Allah ya ja da rai ya ji an su Mama. A iya baki ya amsa da amin a lokacin ta fito ta ce, Bashir gashi. Tasowa ya yi ya kar i manya-manyan foil packs har gida biyar. aya doya da wai ce mai yawa a ciki da wata lafiyayyar liver sauce, aya irsh potatoes ne aka soya, sai wai a kai da aka soya shima, aya tosted bread ne mai yawa wanda ya sha butter sai hamshi yake yi. Daya kuma milk cincin anannu mai yawa, na biyar in kuma lafiyayyar fried rice ce da gasashhiyar kaza guda a kai. Ta ce, Ku yi iftar kai da sauran. Murmushi ya yi y ce, Godiya mu ke Antyn mu, Allah ya biya. Wannan kayan da i haka? Godiya mu ke yi. Murmushi ta yi ta koma ta zuba lemo da yawa a leda ta kawo ta ce, ga drink. Ya kar a yana ta godiya kafin ya kalli Omar da kamar bai san me ake yi ba. Bash ya ce, Damisa Antyn mu ta yi mana kyauta, yau mu ka zan samu yi iftar dan da shan ruwa mu ke yi. Sautin murmushin ta ya ji hakan ya saka ya juyo kamar zai yi magana sai ya fasa ya sake auke kai. Bashir ya sake kallon ta ya ce, Antyn mu Boss ya yi