← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 205

Sashe 44

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fried Chinese rice da kaza, ita da mai aikin ta suka zuba a packs guda hamsin, sannan aka ora ruwa da lemo da kuma naira dubu aya. Mai aikin ce ta auka ta fita dashi tana rabawa bayan ta gama ta dawo ta gyara mata kitchen in ta wanke kayan sannan ta koma gidan Hajja dan can ma aiki ake yi sosai. Nayla Bashir ta kira a waya ta ce yazo ya kar ar musu sa o. Kamar da aramar sallah tare suka shigo da Omar tana jin muryar Bashir ta san tare suka shigo dan da zata ji yana buga gate, da hijjab a jikinta fito falon, yana ganinta ya ce, "Antyn mu barka da yamma." Ta yi murmushi ta ce, "Barka dai Bashir, ga abincin iftar"ta fa a tana bashi manyan packs masu girma guda uku. Kar a ya yi ya ce, "godiya mu ke Antyn mu, Allah ya saka da alkhairi." "Amin ya rabbi" ta fa a tana juyawa ta koma shi kuma Bashir ya fita. Omar dai bai ce komai ba ta sake dawowa a sanyaye kanta na asa, ta so ta daure amma Allah ya sa tana son zuwa gidan Hajja shiyasa zata sake yi masa maganar. Nayla ta kalle shi ta ce, "YayaMar." Bu e ido ya yi ya kalle ta tare da mi ewa tsaye. Azumin ne yake an bashi wahala kasancewar ana rana sosai, duk da yamma tayi amma har lokacin da zafin rana. Ta ce, "Don Allah Ina so na je gidan Hajja." Kallon ta ya yi dan shi ba dan ya ganta ba ya auka ta tafi, ganin yadda take hawaye sai abin ya bashi mamaki ya ce, "zan hana ki ne?." Nayla hawaye ya sake sakko mata ta ce, "baka ce na je ba." Yadda take ifta idanu ne ya auki hankalinsa, duk da kuka take yi amma hakan ya burge shi sosai. Zuba mata ido yayi yana kallon yadda take motsa bakinta gashin idanunta yana sama da asa, ido ya lumshe ya bu e ido tare da yin ajiyar zuciya ya ce, "ki je, daman ai bakya tambayata ko?." Nayla murya na rawa ta ce, "Ka yi ha uri." Ya an ta e baki ya ce, "Laifi ki ka yi?." Nayla ta ago ta kalle shi ta ce, "Ka ce ina fita bana fa a maka." Bai bata amsa ba kiran waya yashigo wayarsa, bai auka ba ya datse kiran bai ce mata komai ba. Nayla ta ce, "in baka ce naje ba yau babu inda zan je." Yadda ta yi maganar a raunane ya saka shi ya sake kallon ta, sai ya yi murmushi wanda bai san dalili ba. Ita kuwa jin shiru bai yi magana ba kuma bata ji motsin wucewarsa ba sai ta ago kai suka ha a ido, janye idanunsa yayi ya ce, "daman in zaki je ai bakya jira na ce." Nayla ta sake raunana murya da shagwa a ta ce, "Yau zan jira" ta fa a tana sunkuyar da kai dan ta san baya jure doguwar magana, ta auka zuwa yanzu zai mata tsawa ne. Shi kam ya i katse maganar ne saboda yadda take maganar da shagwa a ba karamin burge shi hakan yake yi ba, shiyasa yake yin maganar da dole sai ta bashi amsa. an kawar da kai ya yi yana murmushi kafin ya juyo ya mayar da fuskarsa yadda ta ke ya ce, "ki je." Murmushin da ta saki mai sauti tare da yin aramin tsalle cikin farin ciki. Ba aramin tafiya da imaninsa hakan ya yi ba, ya zuba mata ido zuciyarsa na bugawa kafin ya auke kai ya juya zai fita. "YaMar!" Ta sake fa a cikin sanyin murya da dauriya kar ya yi mata masifa. Cak ya tsaya bai juyo ba ta ce, "Na bar abincin iftar, don Allah ka ci." Juyowa ya yi ya kalle ta suka ha a ido ta janye idanunta dan gaban ta fa uwa yake yi in tana kallonsa ta ce, "Don Allah." Bai tanka ba ya fita. Murmushi ta yi ta ce, "YaMar Ina sonka sosai, Allah ya saka maka sona a zuciyarka" ta fa a tana juyawa da sauri ta auki hijjab da abinda zata kaiwa Hajja ta fita a guje sai gidan Hajja cike da zumu KRB3P022 ArewaBooks@nanahaleema. Nayla a gidan Hajja ta sake tana ta harkokinta, kana kallon ta zaka ce bata da wata damuwa saboda ta shiga cikin an uwa ana ta hira ana dariya. Kaf in su a da jikoki suna tare da Hajja, mahaifiyarta ce kawai babu amma ita ta maye gurbinta. Haka aka sha ruwa cikin wasa da dariya an saka Hajja a tsakiya wanna ya ce wannan yace. Bayan an gama shan ruwa ne Nayla ta koma gefe Hajja ta kalleta ta ce, "Hauwa ya aikin sallah? Zaki iya kuwa?." Nayla ta kalli Hajja a shagwa e ta ce, "ni bazan iya ba, da yayi min maganar ma na ce a bayar sadaka kawai ni bazan iya aiki ba. Ban ma ta a yi ba fa Hajja." Hajja tayi murmushi ta kalli iyayenta maza da suma suka yi murmushin, ko ba ta fa a ba sun tabbatar da ana samun canji sosai a zaman ta da Omar. Hajja ta ce, "Ashe ma ya tambayeki, ni na auka kawai sai dai ki ga an kawo namn sallah." Nayla tayi ar dariya, bata fahimci bugun cikinta Hajja take yi ba ta ce, "A'a ya tambaya zan iya nace a'a kawai in an yanka a rabar, in ina son ci zan turo nan." Hajja ta yi murmushi ta ce, "To ai shikenan, Allah ya taimaka." Aka amsa da amin kafin Nayla ta mi e tana amsa waya ta bar wajan. Mama Sa'adatu ta kalli Hajja ta ce, "Yanayin Nayla bai yi kama da wacce take cikin damuwa sosai ba, duk da har yanzu bata mayar da jikinta na baya ba amma walwalarta ya nuna bata tare da acin rai." Hajja ta ce, "Na fa a mu ku ni a jikina nake jin auren nan nata babu abinda zai raba shi sai mutuwa." Daddy ya ce, "Ni ta yadda hankalina ya kwanta da auren yadda gaba aya aka daina tashin hankali da mijin na ta, sannan sana'ar da yake yi Allah ya saka mata albarka lokaci ka an." Abba ya ce, "wannan shine kawai abin farin cikin, ni kaina in na tuna a yanzu ya dogara da kansa Ina jin da i. Amma ina ganin har yanzu zaman su bai wani daidaita yadda ake so ba." Baba ya ce, "In sha Allah komai zai wuce ya zama labari." Aka amsa da in sha Allah suka cigaba da hira har Nayla ta dawo ta zauna suka koma gefe ita da Salma suna hira. Sai kusan tara na dare sannan suka taho ita da Salma a asa suna hira. Nayla ta ce, "Salma kin san meye?." "Sai kin fa "A farkon auren mu YaMar ya ce in zan fita ba sai na fa a masa ba, babu ruwan shi da inda zan je, amma yanzu in na fita ban fa a ba sai naga kamar yana jin haushin hakan, ya ki ke gani, na dinga tambayarsa ko na share tunda ai shi ya fa a tun farko?." Salma ta ce, "canjin zaman naku da aka samu shiyasa yake jin haushi, ni fa wallahi gani nake kamar yanzu shima yana sonki Nayla, kawai shegen banzan halinsa ne ya hana shi ya bayyana. Ki yi ha uri kar ki ce na zagar miki miji, amma akwai abinda yake ji a zuciyarsa game da ke. Tunda ki ka bani labarin yadda ya dinga fa a akan afarki ake advert da ita na saka question mark akansa." "Kema wai tunanin ki kishina ya ke yi?." "To meye in ba kishi ba?." "Kawai ya tsane ni mana, baya so na shiga cikin abinda ya shafe shi." Salma tayi murmushi ta ce, "Nayla kenan, kin riga da kin saka hakan a ranki ne shiyasa. Amma ni yanzu gani nake yi yana jin wani abun a kan ki sosai." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "ban saka a zuciyata ba Salma, kar ma na saka yazo ya dame ni gwara na tsaya a inda ya ajjiye ni. Ina sonsa har gobe, babu abinda ya ragu daga son da nake masa. Ban saka a raina yana sona ko yana kishina ba, amma ya canja sosai daga zaman mu na farko zuwa yanzu. Kuma maganar Didi ce ta tabbata da ta ce bashi da saurin sabo ne, da zarar mu saba wani abun zai canja kuma gashi." Salma ta ce, "to da hakan, amma wannan ya wuce saurin sabo Nayla, kawai mu cigaba da addu'a, Allah ya kawo silar daidaitawar ku. Allah yasa ya so ki fiye da yadda ki ke sonsa." Nayla ta yi mumurshi ta ce, "Amin Sis." "Ki cigaba da tambayarsa duk inda zaki je in, daman ai mijinki ne." "Wani lokacin tambayar ce sai a hankali, Kamar wahainiya yake canjawa yake a ko yaushe. Yanzu zai yi kirki anjima ya birkice ya hauni da masifa." Salma ta yi dariya ta ce, "zai yi ya gama, akwai lokacin mu da zai zo mu wahalar da an banza." Dariya itama tayi har suka zo bakin gate in Salma ta koma ita kuma ta shiga ciki. Daman ta san baza ta same shi ba, amma babban abinda ya bata mamaki yau kam ya ci abinda ta ajjiye in duk da sai ka kula zaka fahimta bai ci da yawa ba amma ita da ta ajjiye ta san an ta a. Sosai ta ji da in hakan a zuciyarta ta kuma amince da yanzu Omar in ya canja sosai. Washe gari sallah ba su ha u da safe ba saboda baccin da tayi sai tara ta farka, ta ji haushi sosai dan ta so ta sake zuwa sallah amma Allah bai yi ba. Wanka tayi ta ci kwalliya cikin atampa inkin fitted gown. Gaba aya atamfar ta dame ta, saboda ita bata saba saka kaya fitted ba ta fi gane wanda zata sake sosai. Tana aura daknwali tana mita, Salma ce ta saka tailor in gaba aya ya yi mata wannan inki, daga fitted gown, sai straight, sai kuma riga da siket masu aramar riga.
Chapter 44 · 0% Book details