Sashe 126
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bakinta cikin salon soyayya da son kwantar mata da hankali. A hankali ya zare bakinsa da nata yana ri e da fuskarta ya ce, "ina sonki, ina aunar ki. Rabuwa da ke daidai yake da rabuwa da raina." Cikin shagwa a ta ce, "to shine ka ke wancan tunanin?." Ya sauke numfashi ya ce, "tsoron nake ji, da ace wani abun ya same ki ta dalilina gwara na mayar dake wajan Abiy kin cigaba da zama cikin kwanciyar hankali. Rashin ki zai yi min illa, rashin ki zai cutar dani, rashin ki zai zama ajalina Ashiq. Amma gwara na rasa raina da ace wani abun ya sake faruwa dake!." Ta sauke numfashi cikin son kwantar masa da hankali ta ce, "in sha Allah babu abinda zai faru, da izinin Allah komai ya are, ka daina damuwa. Kuma don Allah ka daina yi min magana irin wannan, bana so." Omar ya sauke ajiyar zuciya yana kallon ta cike da damuwa ya ce, "Dole na damu Jidda, kalli hannunki fa, ciwon yayi girman da sai da aka inke shi. Har abada da wannan tabon zaki rayu har ki bar duniya, iya kallon wannan tabon na hannun ki ba aramin ciwo zai saka min a zuciyata ba, saboda na san ni ne sila. Baki da tabo ko ka an a jikin ki, amma ta silata gashi kin samu tabo mai girma. Wallahi ban ta a jin na damu akan abinda na aikata a baya ba sai yanzu. Kuma nima haka nayi, matar mutum ko ar uwarsa da bata ji ba bata gani ba a kanta zan mu auki fansa, duk da ban ta a kisa ba, amma na..." sai ya kasa arasawa ya sake jan numfashi yana kallon ta ya ce, "ina hasashen yanayin da zan kasance in wani ya yi irin abinda nayi a baya Jidda, ban san a wanne yanayi zan kasance in aka sake cutar dake ba." Nayla ta ri e fuskarsa cike da damuwa ta ce, "Rauni nake gani a fuskar mijina, mijina bai yi kama da namiji mai rauni ba." Ya lumshe ido ya bu e ya ce, "Nayi rauni Jidda, raunin zuciyata ne ya bayyana akan fuskata Jidda, wallahi zuciyata tayi rauni sosai. In na tuna ta silata kika kwana a asibiti da ciwo a hannun ki sai naji duniyar tayi min zafi. Wannan shine dalilin da na kasa sakewa dake, gani nake kamar za a cigaba da cutar dake in na cigaba da amsa suna mijinki" ya fa a yana ri e hannunta gam. Nayla ta ce, "in sha Allah babu abinda zai faru, ka kwantar da hankalinka, Allah yana tare damu." Ya bita da kallo kafin ya auke ido daga kanta ya ce, "Rayuwarki bata dace da rayuwa a nan ba Jidda, ina jin tsoron kar wani abun ya sake samun ki, ina jin wannan tsoron a zuciyata. Sai yanzu na sake gasgata maganar Didi da take cewa baki dace dani ba!." Nayla a sanyaye ta ce, "YaMar ka daina fa ar haka, yana cutar dani." "Jidda har suma ki ka yi fa saboda tsoro, kika kwanta a asibiti saboda ciwon da aka ji miki. In aka sake cutar dake da wanne ido zan kalli Abiy?." "Babu abinda zai kuma samu na, ka daina damuwa don Allah." Ya lumshe ido ya bu e ya kalle ta ya ce, "Ki yi ha uri, na kasa kula da lafiyarki har aka wace miki waya, na kasa kula dake har aka yanke ki jini ya zuba daga jikin ki. Ki yafe min, aurena ne ya saka kika shiga yanayin da ki ka shiga, da baki aure ni ba da hakan bai faru ba." Ta saka hannunta a tsakanin kafa arsa ta ri e shi tare da kwantar da kanta a jikinsa ta ce, "Ka daina fa ar haka, bana jin da i ko ka an. Kuma ciwon da naji addara ce." Ya an lumshe ido ya bu e yana ji zuciyarsa na bugawa sosai. Nayla ta ce, "Ya jikin wanda suka jiwa ciwo?." "Ya ji sau i, yana gida." "An kama su ko?." "Uhum, amma bazai jima ba zai fito. Yana da manyan da suka tsaya masa, baza su bar shi ya jima a gidan yari ba." "Ko ya fito bazai yi mana komai ba, ka daina damuwa." Numfashi ya sauke baice komai ba, yana jin zuciyarsa babu da i akan abinda ya faru, ya san duk ta silarsa ta shiga yanayin da ta shiga. Sai yanzu yake jin ra in da iyaye da an uwan wasu suka ji a lokacin da yake cutar da yaransu. Sai da ya ga Nayla a kwance a gadon asibiti sannan ya tabbatar da ba aramin cutar da an uwan wasu suka yi ba. Gashi Allah ya fara saka musu, ya cutar da matar wani an cutar da matarsa, ya zama silar zubar jinin wata shima an zubar da na matarsa, ya zama silar kwanciya a asibitin matar wani shima ga tasa ta kwanta. Addu'a yake yi da fatan Allah yasa abun ya tsaya iya haka, in kuma sakayyar zata cigaba da bibiyarsa Allah yasa ta tsaya a kansa ba sai ta tsallaka kan Nayla ko Didi ba. Nayla ta kalle shi ganin ya yi shiru yana tunani, ta zame ta zube guiwa a asa ta ce, "zan iya ro ar ka alfarma?." Ya aga mata kai alamun eh, ta ri e hannunsa ta ce, "Don Allah ko me zai faru kar ka ce zaka koma rayuwar da ka bari a baya, ko meye zai tunkaro mu ka kar addara kar ka tunzura ka koma rayuwar baya Rouhi. Ko da zasu kashe ni, ka yi min al awarin baza ka cutar da kowa ba." Ya yi murmushin gefen baki yana kallon ta ya ce, "ke kin san bana yin kara, bana fa ar abu dan na burge wani ko wata. Wallahil azim duk wanda ya sake arin cutar dake sai dai a haifi wani ba shi ba, wannan da aka yi na yale tunda an kama wanda ya aikata, amma in aka maimaita wallahi bazan yale ba. Jidda ko ban kashe shi ba sai nayi masa abinda zai ji ina ma ya mutu. Daga ranar kundin laifukan Omar Tiger da aka rufe za a bu e sabo, domin kuwa laifukan da na yi a baya ba komai bane akan wanda zan yi. Hmmm kedai Allah ya kiyaye kawai, amma zancen alfarma indai wannan ce bazan yi miki ba Jidda!." Bata ce komai ba dan ta san bazai yi in ba, ta rausayar da kai ta ce, "ni kuma hakan bazai yi min da i ba." Bai ce komai ba ya girgiza kai kawai, ta ce, "sannan wannan wu ar da ka ke kwana da ita ta meye?." Ya kalli idonta ya ce, "ko a addini dan na kwana da makami ba laifi bane, tunda na tare a gidan nan take kusa dani, duk an iskan da ya kuma kawo min wargi sai dai uwarsa ta haifi wani. Na daina sharewa, na daina kai maganar ga hukuma, zan koma Omar in da suka sani a baya." "Baza ka koma ba in sha Allah, babu abinda zai sake faruwa balle har ka auki mataki." Shiru yayi bai ce komai ba, ta dawo ta zauna a kusa dashi. Fuskarta ya ri e ya ce, "Akwai abinda yake damunki? Akwai abinda yake yi miki ciwo?. Hannun yana ciwo har yanzu?." "Ba ya ciwo Rouhi, ya daina kamar ban ji ciwo ba. Lafiya alau nake." Yayi mata peck a goshi yana girgiza kai bai ce komai ba. Sun jima a haka a zaune kafin ya ce, "ki kwanta Jidda, dare yayi." Ta kalle shi ta ce, "ta ya zan iya bacci bayan mijina baya cikin walwala?." "Bana ciki Jidda, bazan ta a samun sukuni ba tunda aka fara haka. Tunani nake yi kar na fita na barki ke ka ai a gidan nan a sake cutar da ke." "Haba Rouhii, ya zaka bada ni? Don Allah ka nutsu, ka manta da komai mu cigaba da rayuwarmu. Tunda muna addu'a Allah zai cigaba da kare mu, kariyar Allah ce ta saka ciwon ya tsaya a iya hannu, mu cigaba da addu'a kawai." Ya zuba mata ido yana kallon ta kamar mai neman wani abu, sai ta ce, "Please!." Ya an yi murmushi da son kawar mata da damuwa ya ce, "kin daina jin tsoron nawa?." Ta yi murmushi ta ce, "Tiger nake jin tsoro ba Rouhii ba." Ya girgiza kai yana murmushi ya ce, "Ina sonki Jidda, ina aunar rayuwa dake. Ki yi ha uri a yadda kika same ni, rana ta farko da nake jin nadamar abubuwan da na aikata a baya, da ban aikata ba da na kasance miji na gari a wajanki!." Ta yi murmushi tana shafa gashinsa tana kallon idonsa ta ce, "Wallahi kai miji na gari ne Rouhi, babu abinda na nema na rasa a tare dakai akan me zaka dinga kiran kanka da wannan suna?." "Jidda na kasa baki kwanciyar hankali, har suma ki ka yi a irjina saboda tsoro, ga tabon da aka yi miki wanda na tabbatar dashi zaki je lahira. A hakan ne na samar miki da kwanciyar hankali Jidda?." "Suman da nayi firgici ne kawai, amma ba dan ka kasance akasin miji na gari a gare ni ba." Ya zubawa bakinta ido har ta gama kana ya ce, "zan saka miki da alkhairi in sha Allah, wannan acin ran da na saka ki, da firgici, da tsoro, da ciwon da kika ji zai maye gurbinsa da farin ciki in sha Allah Jidda. Ki cigaba da ha uri dani kawai, ina da abi'un da basa yi miki da i, na san ina juyewa na koma miki wanda bakya so, amma wallahi ke ce rayuwata. Ina sonki, ina aunar zaman ki cikin kwanciyar hankali, ina so na rayu dake, ina tsananin kishinki!. Dan a cikin haushin fitar ki da naji harda kishin Tk da ya ri e hannun ki, har yanzu ko magana bana iya yi masa, duk da ba da wani abun ya aikata ba, ya yi ne dan ceton rayuwarki amma na gaza fahimtar hakan!." Nayla ta yi murmushi ta ce, "ni shaida ce akan duk abinda ka fa a YaMar. Amma ka yi ha uri ka manta