Sashe 185
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ya ago ido ya kalle ta ya ce, "baza mu daina kuka ba, har abada!." Baba Adamu ya dafa shi ta baya ya juya ya kalle shi ya ce, "Sai ha uri Omar. Ka daure ka cinye wannan jarabawar, kar ka sare lokaci guda. Allah ya ji an Aisha ya gafarta mata, halinta na gari ya bita, Allah ya sa zaman kabari ya fi mata zaman duniya da "Amin .amin ya Allah" ya furta yana lumshe ido tare da ajiyar zuciya. Yana ji ashe haka ake jin da i in aka yiwa wanda ka rasa addu a?. Marmerh ya kalla da take ta tsokanar Musliha tana yi mata wasa. Omar ajjiye Marmerh ya yi ya ajjiye Musliha ya mi e tsaye Baba Adamu ya ce, "ina zaka je?." Omar ya ce, "ba nisa zana yi ba, zan dawo yanzu." "Amma baka da lafiyar da zaka iya fita kai ka ai." "Zan iya, bazan jima ba zan dawo." Mama Zainab ta ce, "A a Omar, kar ka fita wani abun ya same ka." Ya yi murmushi yana kallonsu yana jin wani iri a zuciyarsa, Didi da Nayla ne ka ai masu damuwa dashi, yau ssi ga dangin mahaifiyarsa suna tsoron kar ya fita wani abun ya same shi. Ya lumshe ido ya ce, "kuma tsoron kar nima na mutu ko? Suka kalle shi gaba aya cikin rauni, ya girgiza kai ya ce, Kar ku damu, Allah zai bani aron rai har sai na inganta rayuwar Marmerh" ya fa a yana fita daga falon. Nayla suka dinga bawa ha uri ita dai jinsu take yi amma da ta tuna wani abun sai kuka. Omar kuwa saboda ganganci da kansa ya ja mota, kai tsaye ma abarta ya wuce ya je kabarin Didi ziyara. Addu'a yake mata yana kuka yana ji kamar ya tone kabarin ya fito da ita. Ya fi awa aya a gaban kabarin sannan ya tashi ya shiga mota ya jima a zaune kafin ya tafi. Tafiya yake yana tunanin ya bar Didi a can shi kuma gashi a cikin mota yana tafiya, Didi bata duniya shi kuma yana duniya, sai ya ji kamar bai kyauta mata ba. Hawaye yake gogewa yana tafiya ya wuce gidan Didi. A ofar gidanta ya ajjiye motar ya tsaya yana arewa gidan kallo. Jikinsa ya shafa yana nemn wayarsa, sai ya tuna bashi da waya bai ma san inda wayar take ba gashi yana son magana da AbdulHamid, kuma bazai iya shiga cikin gidan ba. Ana haka sai ga AbdulHamid ya fito Omar ya zuba masa ido, shi kansa AbdulHamid in ya rame sosai kana kallonsa ka san yana cikin yanayi na damuwa. Omar ya sauke glass a sanyaye ya ce, "Mijin Didi." AbdulHamid ya kalli Omar sai ya yi murmushi duk da gabansa ya fa i, Omar ya fito daga motar yana kallonsa AbdulHamdi ya araso inda Omar yake. Hannu Omar ya bashi suka gaisa ya ji jikin Omar zafi zau ya ce, "Omar baka da lafiya me ya fito da kai?." Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "na jima a nan ina jiranka, bani da waya balle na kira ka, kuma bazan iya shiga gidan nan ba." AbdulHamid ya yi murmushi ya ce, "Allah ya gafartawa Aisha." "Amin ya Rabbi. Yanzu ma naje kabarinta na gaishe ta, amma ban ji ta amsa kamar ko yaushe ba. Tana cewa lafiya lau Alhaji Omar, da tana da rai da yanzu ta ce Omar me ya same ka, mu tafi asibiti" Omar ya yi murmushi hawaye na sake taruwa a idanunsa ya ce, "Amma yanzu ta tafi ta barni, ta bar duniya ni kuma ta bar a cikinta ko tausayin bata ji ba. Ko ta ya rayuwa zata yi min da i bata tare dani oho, bata yi wannan tunanin ba ta mutu ta bar ni. Sai kalamansa suka karyawa AbdulHamid zuciya ya goge ido ya ce, "Mutuwa bata bari wani dan wani ai Omar, dan ka rasa wani ba hakan yana nufin ka rasa farin ciki ba ne. Omar ya goge idanu ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Alfarma nazo nema a wajanka, ban sani ba ko zaka iya yi min." "Ko wacce irin alfarma ce zan yi maka Omar, ka fa i komai da yake zuciyarka. Yadda Aisha zata yi maka duk abinda ka ke so nima zan yi Omar. Omar ya girgiza ya ce, "Marmerh....! Marmerh nake so ka bar min ita ta dawo hannuna da zama. Na san abu ne mai wahala a gareka amma ka duba raunin da nake ciki na rashin Yayata, na san kai matarka rasa ni kuwa duniyata na rasa gaba aya. Ka san itace komai nawa, ka san bani da kowa sai Didi. Zaman Marmerh tare dani zai an rage min wani abu ka an daga cikin kewarta. Ka amince don Allah ka bani ita!." AbdulHamid ya yi ajiyar zuciya kafin ya yi magana Omar ya ce, "Don Allah kar ka ce a a, nayi maka alqawarin zan bata tarbiyya mai kyau, zan inganta mata rayuwarta ba dan kai baza ka iya ba. Ina so na nuna mata aunar da baza ta yi maraicin uwa ba, kuma ba dan kai baza ka iya ba. Ka taimaka min don Allah!." AbdulHamid ya kalli Omar yaga gaba aya ya canja, ya yi sanyi da rauni kamar bashi ba, gashi ya rame matu a. Ya ce, "Shikenan Omar, na baka ri on Marmerh." Omar ya yi ajiyar zuciya ya kalle shi ya ce, "na gode, na gode sosai." Ya yi murmushi ya ce, "babu komai, na san zaka kula da rayuwarta sosai, Allah ya baka ikon kula da ita." "Amin..amin Na gode sosai." "Sai batun gadon yayarka, na fara tartara abinda na san ta mallaka domin a sauke mata nauyi." Omar ya ce, "ka yi duk abinda ya kamata." AbdulHamid ya ce, "in sha Allah, Ka koma gida baka da lafiya." Omar ya aga kai ya shiga mota ya tafi. AbdulHamid ya bishi da kallo cikin tausayi, ya jima bai ga an uwan da ya fita daga hankalinsa saboda mutuwar yayarsa ba sai Omar. P117 Omar bai shiga gida ba sai da ya yi sallar magriba, a harabar gidan nan suka ha u da su Bashir suna jiran sa. Ganinsa duk suka taho suka gaishe shi ya amsa suna sake yi masa gaisuwa. Ya kalli Bashir da ya kasance shine manager, shine mai kula da komai in baya nan ya ce, "Bashir ka cigaba da kula da komai, duk abinda kaga ya dace ayi, in ya zama dole na sani sai ka kira ni." Bashir ya amsa a sanyaye, bai ta a ganin Tiger a cikin wannna yanayi ba, sai ya bashi tausayi ya wuce su ya shiga ciki. Da Umma Saroot suka ha u, tana tsaye da hijjabi ta juya baya tana magana da masu aikin gidan magana. Kallonsa ta yi a sanyaye ta ce, "Omar ka dawo? Ya jikin?." Ya girgiza kai ya ce, "naji sau i sosai. Fita zaki yi?." Tsayawa tayi tana kallonsa, sai ta yi saurin kawar da mamakinta ta ce, "Gida zan koma Omar, tunda ka samu lafiya." "Meyasa zaki tafi? Kafin ta bashi amsa ya ce, ko an ata miki rai?. Ta girgiza kai ta ce, Babu abinda aka yi min Omar, kawai zan koma ne. Omar ya ce, Ki zauna don Allah" ya fa a a sanyaye yana kallon ta. Zata yi magana ya ce, "don Allah!." Sanyi da da i ya mamaye zuciyarta tayi murmushi ta ce, "To Omar, zan zauna zuwa wani lokaci." "na gode Umma!" ya fa a yana wuce ta ya hau sama. Murmushin farin ciki take yi ta auki waya tana kiran an uwan tana basu labarin abinda Oamar ya yi mata. Bai iya kuma fita ba a aki ya yi sallar i'sha, Nayla ta kawo masa abinci har cikin akin ta zauna a kusa dashi ta ce, "ka ci abinci." Ya kalle ta ya ce, "har yanzu irjina bai daina nauyin nan ba, da na zubar da hawaye ya ragu amma akwai saura." "Sai a hankali ai zai daina, ka cigaba da addu'a. Ga wayarka azu Baba ya bani bayan fitar ka." Kar a ya yi ya ajjiye a gefe. Nayla ta ce, "ka ci abincin." Da kanta ta bashi ya an ci ka an ya ce ya ishe shi, bata matsa masa sai ya cinye ba ta bashi magani ya sha. Wuyanta ya ta a ya ce, "kema baki da lafiya, kin rame sosai." "Na samu sau i, rashin arfin jiki ne kawai da bani dashi." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Na je gidan Didi." Ta kalle shi ya aga kai ya ce, "Gidanta na gaskiya da gidanta na duniya, na kai mata ziyara kabarinta na gaisheta amma banga murmushinta ba, kuma ban ji sautin muryarta ba. Na yi mata addu'a ina kuma fatan addu ar ta iske ta." Nayla ido ya ciko da hawaye ta ce, "amma baka fa a min mun je tare ba?." Ya kalle ta cikin sanyi ya ce, "Zaki iya zuwa?." "Na ta a raka Abiy kabarin Ummana amma an jima sosai, shima yana zuwa ziyara duk ranar juma'a har yanzu. Nima zan je na yiwa Didi addu'a, in zaka je ka dinga fa a min." Ya ri e fuskarta ya share mata hawaye ya ce, "in sha Allah zan fa a miki." Nayla ta bi fuskarsa da ta koma arama da kallo ta ce, "ka tuna maganar Didi ta arshe?." Ya aga kai alamun eh ta ce, "ka cika mata burinta don Allah, ka yi abinda zata yi farin ciki a cikin kabarinta." Ya ce, "Zan yi Jidda! Wallahi zan yi!. Zan ri e kowa kamar yadda take so, zan bar komai ya wuce bazan sake tuna komai ba. Zan ri e su kamar iyayena, zan nemi shawararsu da albarkarsu da komai, zan kuma nemi su yafe min, zan cika birin Didi in sha Allah!. Da ace na san mutuwa zata yi da na bar komai ya wuce tun tana duniya, da ace na san zata mutu bazan i amincewa da abinda take fa a ba, da zan yi tun tana da rai ko dan na faranta mata rai. Haushin kaina nake ji da ban bar komai ya wuce tun tana raye ba, da