Sashe 194
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kyauta yake so a dinga yi a islmiyyar, hatta uniform da littafai kyauta za a bayar. Ai kuwa haka ne ya kasance, ya zuba ma'aikata a islamiyyar wacce yake biyan su duk wata da aljihunsa, kuma albashi mai yawa wanda bazai saka ka ji koyarwa ta fita daga ranka ba. Bai amince a kar i ko wanne ku i a wajan alibi ba, littafi kawai alibi zai siya, shima in farkon zuwa ne za a baka na ajin da aka kai ka kyauta. an unguwar sun ji da in wannan islamiyya, domin karatu ake yi mai ratsa zuciya da yake ratsa unguwar sosai, ga tarbiyya, ga masallaci na maza da mata akwai a ciki. Babu ranar da za ayi karatu a tashi ba a yiwa Omar addu'a da ahlinsa ba, shiyasa Allah ya ke bu a masa ya ke ta ganin cigaba fiye da tunaninsa. angaren fitar da zakka curarriya mai kauri yake bayarwa, baya bada ka an-ka an, ya fi bayar da yawa yadda zai ishi mutum ya ja jari. Omar da kansa ya bawa Malam Salulu mai kiran sallah ku in zakka, ya dinga jin kunyar Omar dan shinr kan gaba a gulmar Omar da Yayarsa. Kamar ko yaushe Nayla tana zaune tana waya da Salma da ta kusa haihuwa, Omat ya shigo falon ya zauna kusa da ita yana kallonta a lokacin ta kashe wayar. Ta kalle shi tana fari da ido tare da aga masa gira sama ta ce, "Zuma ya dai?." Murmushi ya yi, ya kalli falon ya ga babu yaransa sai ya ce, "ina yaran suke?." Nayla ta ce, "Sun tafi gidan Hajja da Salima." "Na shiga na duba Hajja jiya, ya jikin nata?." "Da sau i sosai, jikin girma sai a hankali." "Gaskiya ne." Nayla ta ce, "yaushe za a saka interview in ka ne? Ni na agu na ga mijina ana hira dashi." Murmushi ya yi mai aji, kana ya ce, "ban sani ba, na je dai sun auka. Kin dame ni akan na je na kuma je in." Ta yi murmushi ta ce, "ina so mutane da yawa su koya daga gare ka." an sake murmusawa ya ce, "Zan yi tafiya zuwa Mexico." Ta kalle sa ta yi murmushi ta ce, "kai ka ai?." Ya girgiza kai ya ce, "kin ta a ganin inda harshe ya rabu da ha ori ne Ashiq..? Tare dake na nema mana visa, amma tafiya da yaran nan ne akwai damuwa gaskiya." Dariya ta yi ta ce, "To yanzu ya za a yi?." Ya an ta e baki ya ce, "tare zamu je dasu, kwana tara kawai zamu yi ai. Amma ni nafi so daga ni sai ke, nafi so na sake da matata babu kukansu balle su hanani abinda nayi niya, da Didi tana da rai ita zan tattarawa su mu yi tafiyar mu." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Dole dai tare zamu tafi in." Ya ce, "Gobe juma'a, in na je kabarin Didi sai na fa a mata anta suna hana ni sakewa da matata. Babu damar na ke e da ita sai su fara yi min kuka." "Nima ai zan je, kuma zan fa a laifin da ka yi min. Ka dinga yi min fa a kamar zata zane ni, har yanzu ban wuce fa a a wajanka ba." Ya an harare ta yana rausayar da kai ya ce, "wai bai wuce ba?." Ta murgu a baki bata ce komai ba. Ya yi dariya yana jan kumatunta ya ce, "Yau da daddare ki shirya zaki raka ni wani waje, tafiyar Mexico sai ranar Sunday, akwai inda zamu je mu kwana biyu mu dawo. Zan wanke laifina in sha Allah, duk fushin da ake yi dani zan gusar dashi." Nayla ta ce, "ina ne?." Ya bu e ido ya ce, "zaki gani ai, in na fa a miki ba mamaki bane ba kenan." Murmushi ta yi bata ce komai ba, ya ce, "ginin company ya kammala fa Ashiq, ni gani nake anya bai yi min ka an ba? Ma'aikatan da suke neman aiki sun yi yawa." "Bai yi ka an ba, ai kowa da angarensa. Wasu suna angaren sarrafawa, wasu gyara, wasu sakawa a kwali, wasu delivery." Ya sauke numfashi, ya ce, "haka ne, da mun dawo daga Mexico za a bu e in sha Allah. Ana ta saukar alkur'ani a islamiyya akan Allah yasa a bu e a sa'a." Nayla ta ce, "Amin ya Allah, Allah yasa a bu e a ko wacce jaha ta fa asa Nigeria." "Amin Zumata." "Ina al awarin mukamin personal assistant inka da ka ayi min?." Ya kalle ta yana an bu e ido tare da aga gira a tare, kana ya ce, "ni na yi miki al awari?." "Eh mana, lokacin da na ajjiye aikina na ce maka sai ka bu e company zan zama MD ka ce Allah ya kaimu." Ya ta e baki ya ce, "Dan na ce Allah ya kaimu sai ki ce nayi al awari?." Nayla da shagwa a ta ce, "eh kusan haka ne ai." "Kawai sai na tafi dake company da yake bani da aikin yi? Ko an fa a miki bani da hankali ne?." "Maza nawa ne suke zuwa aiki da matansu?." "Su daban, Omar daban." "Allah ina so, babu abinda nake yi fa, kullum ina zaune a gidan nan" ta fa a cikin shagwa a tana kallon sa. Ya bita da kallon up and down ya ce, "zaman gidan shine ya dace dake, ki yi wanka ki kwanta ki huta shine kawai aikin ki Jidda." Nayla ta ce, "to ba muna tare a can in ba?." Omar ya girgiza kai ya ce, "bazan iya barin ki ba Jidda, gwara miki gaskiya kar na yaudare ki, amma tunda naga aikin ki ke so za a san inda za a ra a ki." Ta kalle sa tana harararsa ta ce, "ra a ni ma za a yi kenan ko?." Ya yi dariya ya ce, "Eh mana." "To bana so." "Kin huta" ya fa a yana dariya. Harararsa take yi, ya yi mata kiss a goshi ya ce, "ina zuwa, ki fa shirya. In yaranki sun dawo ki shirya su." Ta aga kai ya fita ta cigaba da danna wayarta suna magana da Jidda akan kayan da aka siyo na shagon su. Kamar yadda ya ce bayan sallar i'sha suka fita a sabuwar motar da ya siya, Marmerh da Musliha suna bayan mota suna cin lays cheese da ya siya musu, duk sun ata motar sai zubar dashi suke yi suna takawa duk ya marmashe. Gab da zasu arasa inda zasu je ya kalle ta ya mi a mata wani ba yalle ya ce, "kulle idonki, kuma don Allah kar ki bu e." Da mamaki ta ce, "Meyasa?." "Mamaki nake so na baki." Bata musa ba ta rufe ido ta kalli su Marmerh ya ga sun yi bacci ya ce, "kun kyautawa kan ku da ku ka yi bacci." Tafiya suka cigaba da yi har ofar gidan, ya kallata ya ce, "Don Allah kar ki bu e, zan shiga dasu Marmerh na dawo." Nayla ta ce, "Allah bazan bu e ba." Ya auke su ya shiga ya kwantar dasu, sannan ya dawo ya bu e mata motar ya ri o hannunta, ya auki handbag inta da wayar ta zuwa cikin gidan. Ita dai ta ji suna shiga wani waje amma bata san ina ne ba, sai da suka gama shiga sannan ya kwance mata abin idon ta ya ce, "To bu A hankali ta bu e ido tana kallon inda suka zo, dariya tayi ganin tsohon gidan da suka tashi kuma cikin akinsa. Kallon akin take yi ganin komai da suka bari yana nan, frames ne kawai babu dan su ka ai ta cire ta tafi dasu, amma komai yana nan har gadon, an gyara shi an shimfi a masa farin bedsheet wanda aka inka shi da kalmar J da kuma kalmar O. akin take kallo tana murmushi, abubuwan da suka faru a cikinsa na farin ciki dana ru ani suna dawowa cikin kanta. Gefenta ta kalla ta ga atuwar banner a tsaye da hoton sa shida yayi bala'in kyau, dukkan su sun yi murmushi ya dafa kafa arta. akin ya yi matu ar kyau, duk da yana nan yadda yake amma ya burge ta, sai hamshi yake mai kwantar da hankali. Nayla ta kalle sa taga ita yake kallo, ta an yi murmushi shi kuma ya aga mata gira yana kallon idanunta. Nayla ta ce, "Kana kawo ziyara kenan?." Omar ya an bu e ido ya ce, "dole na, wannan akin ya camcani zama akin tarihi." "Gyara akin ka saka aka yi haka?." "Waye zai gyara? Da kaina na gyara. Wa zan bari ya shigo mana wannan akin? Kema kin san ai babu." Murmushi ta yi tana sake kallon akin, ta an girgiza kai ta ce, "Duniya labari, kamar ba a zauna ba." Ya matso kusa da ita sosai ya ce, "kin san meyasa nake son akin nan?." Ta girgiza kai alamun a'a, ya kalli idonta ya ce, "Duk lokacin da na shigo ina tu nawa da abubuwa da yawa da suka faru a cikinsa, ina da first night moment ina dake, ina tuna a wannan akin na fara sanin a mace a rayuwata, ina tuna a wannan akin na fara kwana da mace duniya, a wannan akin na fara iya rarrashin mace, a wannan akin na fara sanin matata itama kuma ta fara sani na a rayuwarta. Sannan a wannan akin na saka matata a ru ani har ta fara jin tsorona....." yayi asa da murya ya ce, "Shiyasa nake matu ar ji da akin nan, na kasa rabuwa da gidan nan balle kayan ciki Ashiq!." Nayla tayi ar dariya ta an sunkuyar da kai ta kalle sa ta ce, "Our first wahala dai." Dariya suka yi a tare shi da ita, ya yi mata kallon asan ido ta ce, "Allah kuwa, first wahala da tashin hankali zaka ce, ba first night ba." Ya ri e fuskarta da hannu biyu ya ce, "bakya alfahari da akin nan?." Ta aga gira sama ta ce, "Ina yi sosai, ai ko wacce mace tana alfahari da wannan dare a rayuwarta, balle ni da yazo min a haukace ta ya zan manta." Dariya