Sashe 28
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta dawo da ciwon kan jikinta haka take ji. Duk da ba wani shiri suke yi dashi ba in yana da lafiyar hakan bai hanata ta ji kamar ta rage masa ciwon ta hanyar kawo shi jikinta ba. Yana kallon ta ta asa ido yadda ta marairaice fuska tana kallonsa, alamun tausayawa ya bayyana arara akan fuskarta. Mamaki ta bashi ganin yadda ta damu da ciwon sa haka, sai ya ji da i a ransa ko babu komai bayan Didi ya samu wacce ta damu da rashin lafiyarsa a karo na farko. Har aka fara kiran sallar i sha suna a haka, bayan an gama kiran sallar ne ya mi e zaune sosai ya bu e ido ya mi e ya fita. Sai sannan ta iya tashi ta yi sallah kasancewar babu tarawee tunda ga watan sallah. Tana idarwa shafa i wutir ta yi, bayan ta idar ta dawo falon ta zauna dan ya dawo a kan idanunta. Ba jimawa sai gashi ya shigo ta amsa sallamar da ya yi ta mi e tsaye tsaye ta ce, YaMar ya ciwon kan? Ka samu ka ci abinci zaka fi jin da Ganin ya yi shiru ya araso inda ya zauna ya auki wayarsa da ya bari a wajan da kuma wani abun a leda. Nayla ta arasa ta zuba masa fried rice da kazar wacce ta rage zata ci, ta araso a lokacin zai bar wajan ta ce, don Allah ka ci abinci. Kallon abincin ya yi ya kalle ta ya ce, na ji sau i, na gode abinda ya ce kenan ya wuce ta. Nayla sai taji da i ya mamaye mata zuciya, ko bai ci abincin ba iya wannan godiyar da ya yi mata ta fi ya biya mata aikin hajj saboda yadda ta ji da i har cikin zuciyarta. Murmushi tayi cikin jin da i ta ajjiye plate in ta shiga ciki zuciyarta cike da farin ciki. KRB3P014 Arewabooks@nanahaleema11. Washe gari da wuri Nayla ta tashi tayi wanka ta shirya cikin aya daga cikin lace in da ya bata. inkin ya yi mata kyau inkin doguwar riga mai fa i kuma mai kyau sosai, daga ciki wajan irji an kama rigar ka an amma daga asa sai tayi fa i, daga baya kuma a bu e take bata kamata ba ko ka an. Kallon kanta take yi a madubi dan tayi kyau lace in ya amshe ta. Waya ta auka a lokacin arfe bakwai da wani abun na safe, ta yi selfie tana murmushi. "In dai akwai masallaci a kusa gaskiya zan je sallar Eid" ta fa a ita ka ai tana kallon kanta a madubi tana murmushi. Key in motarta ta ke nema tana dube-dube bata ganshi ba sai ta fito falo tana dubawa. Turus Nayla tayi ganin Omar ya fito daga aki cikin men lace fari mai ananun zane, kansa auke da hula rantsatstsiya mai shegen kyau sai yalli take yi, gashin kansa ya kwanta a baya sai kyalli yake yi ya sake yin ba i sosai. Fuskarsa a washe yana murmushi da waya a kunnensa, hakan da ya yi sai ya bayyanar da kyau da kwarjinin da Allah ya yi masa. Hatta takalmin afarsa fari ne, ya haska afarsa sosai ya fito sak a matashin Alhaji, in ka ganshi, ka kalle shi sai ka so ka sake kallonsa. Nayla zuciyarta narkewa tayi a kallonsa ganin yadda ya yi mata kyau fiye da kullum a duniya. Ya yi kyau matu a wanda ya wuce tunaninta har bata san ta tsaya cak tana kallonsa ba. Cikin sanyin murya taji yana cewa, "Eid bana ya shiga tarihi, Didi bata tashe ni zuwa masallaci ba na tashi har na shirya zan tafi." Maganarsa ce ta dawo da Nayla hankalin ta, ganin yadda yake amsa wayar ya tabbatar mata da Didi yake yin waya shiyasa yake murmushi. Juyowa ya yi suka ha a ido, shima sai ya yi sak yana kallonta ba tare da ya san ya tsaya in ba. Yadda ta ga ya yi mata kyau shima abinda ya gani kenan a tare da ita, bai lalace a kallonta kamar ita ba taji ya ce, "Gata nan." Jin abinda ya ce ta san Didi ce take tambayarta, bata gama mamaki ba taga ya mi a mata wayarsa irar iPhone 14 pro max. Nayla kallon wayar tayi ta ga seconds suna tafiya ga sunan Didi a rubuce a jikin wayar. Hannu ta saka ta kar a ta saka wayar a kunne Nayla ta ce, "Didi Ina kwana." Didi ta ce, "Kin tashi lafiya Nayla? Ya Shirin zuwa sallah, amma dai zaki je masallaci ko?." Nayla ta ce, "Ina tunanin zuwa." "Ya kamata dai ki je in, ai rai ne ya kawo mu. Da farko da na tambaye shi ya ce min bai san kina ina ba, ashe kuna tare." "Yanzu na fito na ganshi." "Na kira na tuna masa yau fa da masallaci, duk da na san aikin ki ne. Ayi ha uri na tuna waccen shekarar ne shiyasa na kira shi." Murmushi Nayla ta yi ta ce, "kin kyauta Didi. Babu inda zaki je anjima nazo?." "Zan je gidan su yalla ai, a ka'idar gidan su ana ha uwa duk ranar sallah. Sai dai gobe in Allah ya kaimu." "Allah ya kaimu Didi." "amin. Maza ki shirya ki tafi masallaci, nima yanzu zan tafi" ta fa a tana yanke wayar. Tunda ta fara wayar tana murmushi yake kallon ta, a rayuwarsa bai ta a ganin wacce murmushi ya ke yiwa kyau kamar ta ba, da zarar ta murmusa dimples inta sun bayyana akan kumatunta, siraran ha oranta masu haske sun fito waje sai yaga kamar duk duniya babu wacce murmushi yake amsar fuskarta kamar ta. Murmushi na awata fuskarta sosai, da zai iya da ya fa a mata ta cigaba da yi yana samun masauki mai kyau a fuskarta. Ga murmushin nata da arha ko yaushe yi take yi, amma in tayi sai ka sake kallo saboda yadda yake haska fuskarta. ago idon da tayi hakan ya saka ya auke ido daga kallonta, ta tako kusa dashi ta bashi wayar, ya kalli wayar da take mi o masa ya mi a hannu zai kar a idanunsa ya yi karo da zanen ba in henna da yake hannunta. Jiya ya kula dashi a hannunta, amma da yake bashi da lafiya bai kula sosai kamar yau ba. Kamar bai gani ba ya kar i wayar ta kalle shi ta ce, "Ina kwana, ya jiki? Ina fatan ka ji sau i." Bai kalle ta ba ya ce, "da sau i" ya fa a tare da motsawa zai bar wajan. Sai ya tuna bai auki sallaya ba, akin ya koma da niyar aukowa sai ya ga sallayar bata yi masa ba duk da babu abinda tayi, ba dau a ba komai amma bata yi ba. Fitowa ya yi yana kiran wayar Bash yana auka ya ce, "Fito min da sallaya zan tafi masallaci." Kafin ya arasa fita Nayla ta juya da sauri ta koma ciki, ta auko sallaya mai kyau da laushi harda feda mata turare ta dawo ta tarar dashi zai fita daga gate in gidan. Tsayawa tayi ta ce, "YaMar!." Sai dai ya kulle ido ya bu e jin sunan har walwarsa sai da ta harba. Kamar kar ya juya sai kuma ya juyo a hankali ta araso ta ce, "Ga sallaya." Kallon hannunta yayi da take mi o masa ya kalli fuskarta ta ce, "don Allah" ta fa a kamar zata yi kuka. Ganin ya i kar a sai ta tako gab dashi ta rataya masa a kafa a ta juya da sauri ta koma ciki har tana gudu. Murmushi ya yi ya kalli sallayar kafa arsa itama fara kamar kayan jikinsa, ya auke ta daga kafa arsa ya ri e ya fita daga gidan. Tana kallon sa ta window har ya fita tayi dariya ta shiga ciki a guje ta auko mayafi ta yafa akan ta kasancewar rigar jikinta zata yi sallah. Key in mota ta auka sai kuma ta tuna akwai babban masallacin juma'a a gaban layin ba za a rasa yin sallar Eid ba. Ajjiye key in tayi ta fito ko sallaya ita bata nema ba ta kulle gidan ta tafi a afa. Ai kam babu nisa daga gidan, ta tarar har za a tayar ta shiga sahu ta samu space na wasu mata da suke tsaye ta shiga ciki aka tayar da sallah. Bayan an idar tana ta gani ana ta hotuna amma ita murmushi take yi mutanen sun burge ta. Kowa ya sha kwalliya ana murnar sallah, ko iya ganin mutanen ma ai rahama ne. A hankali take takawa wasu mata su biyu baza su wuce sa'aninta ba suna bayan ta suna ta gulamarta. "Na rantse da Allah itace matar Tiger, kan bala'i daman haka take kyakykyawa?. Ita kuma an daba take so? Amma dai ta cuci kanta, ko da yake kyaun fuskarsa ta aura." Nayla tana jin su tayi murmushi tana cigaba da tafiya a nutse. Juyowa tayi ta kalle su duk sai suka auke kai cike da jin kunya bata ce komai ba ta saka key ta bu e gidan ta shiga ciki. Nayla hutawa tayi a gida kafin ta kira mutanen Saudia tana yi musu barka da sallah. Abiy ta fara kira bayan sun gaisa ta yi masa barka da sallah ya amsa daga nan ta kira kowa har su Hajja da Salma. Bayan ta gama ta koma ta zauna tana ajiyar zuciya tana tuna abinda mata nan suka ce, ta e baki kawai ta yi ta cigaba da danna wayar ta. Cousins inta ne suka zo hakan ya saka ta farin ciki suka zauna suna hira suna hotunan sallah. Omar ko da ya dawo ya zo shiga ya ji hayaniya zai ya koma ya fita daga gidan gaba aya dan shi baya son ba i Allah ya sani, ya fi son rayuwarsa shi ka ai kar wasu su dame shi. Sai dare suka tafi ta ji da in zuwan su sosai tare suka yi girki aka ci gaba aya. Har glaze donut suka yi mai da i ta saka sauran a fridge saboda ba Bayan sallar i'sha Omar ya shigo da sallama kai tsaye inda take zaune ya arasa yana kallonta.