Sashe 179
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ciki bata dashi, ni na kasa fa a musu ina da ciki wallahi." "Saboda cikin ba na halak bane?." "A'a, ina yawan cika baki akan irin wannan haihuwar tun kafin na yi aure. Wata bakwai bama shekara ba, cikin ya yi wuri wallahi." "Sai Allah ya ha a ki da miji mai so kuma jarumi, jamuri daga waje jarumi daga ciki. Ai ba aikin ko wanne namiji bane zai iya samar da wani cikin bayan haihuwa da wata bakwai ba, sai wanda Allah ya za a ya yiwa baiwa irina, kamata ya yi ki yi sujjada ki godewa Allah Jidda." Kallon idonsa ta yi ya aga gira ya ce, "ko ba haka bane? Jarumi ne ko akasin haka?." Shiru tayi bata amsa ba kuma bata yi dariya ba, ya ce, "ki amsa min mana, jarumi ne ko rago?." an murmushi ta yi amma bata ce komai ba ya ce, "kin gani ba, murmushi ki ke yi alamun jarumtar kenan, inda akasin haka ne fuskarki zata canja zuwa akasin murmushi. Kina alfahari da jarumtar mijinki har a zuciyarki, mijinki baya ta a baki kunya a kan gadonsa, yana nuna miki jarumtar da take saka ki gigicewa har ta tayar miki da aljanu, sannan ta saka ki maga...." Dariyar da ta yi tana rufe fuska ya saka shi yin murmushi yana kallonta. Daman so yake tayi dariyar kuma ta yi. e fuska ta yi ya ifta idanunsa ya ce, "Ko ba haka bane?." Bata amsa ba ya ce, "to dan ance miji irin wannan ya sake yiwa matarsa ciki a cikin wata bakwai ai ba abin damuwa bane." Ya sake ri o hannunta cikin sigar rarrashi ya ce, "ki kwantar da hankalinki, zan taya ki rainon cikin, zan kuma taya ki rainon Musliha in sha Allah, in kuma kina da ra'ayi zaki iya auko mai kula da ita, zan iya biyanta ko nawa ne in sha Allah. Ni dai burina cikin nan ya rayu cikin aminci" ya fa a yana ora hannunsa akan cikinta. Ajiyar zuciya tayi ta ce, "Haihuwa fa da wahala Rouhii." "Allah yana tare da ke, zan ta yi miki addu'a har Allah ya sauke ki lafiya." "To Allah ya sa" ta fa a a sanyaye. "Ko kefa, amma kina son cikin ko?." "Ina so mana, abu a jikina ka tambaye ina sonsa? Tunda wanda nake so ne ya samar dashi ai dole na so." Yayi murmushi tare da jan kumatunta ya ce, "Na gode Habibty. Ki yi ha uri da fa an da nayi miki, kin san bana jure acin rai." Ta kalle shi a sanyaye ta ce, "to ya zanyi maka? Na ha ura." an bu e ido ya ce, "Babu dole, in baki ha ura ba sai ki rama, ki ta yi min fa a har sai kin gaji, in ma dukana zaki yi ki dake ni." Nayla ta ce, "Kaine dai iris ya rage ka zane ni." Ya bu e ido alamun razani ya ce, "ni Omar na daki matata? Har abada in sha Allah." "Amma ai ka ora min wu a a wuyana a gidan Didi." Murmushi ya yi mai sauti yana shafa wuyan nata ya ce, "itama wannan ta qaunarki ce Jidda." Ta an ta e baki kamar yadda yake yi ta ce, "Ya batun shari'ar da ka ce zaka yi da Didi? Wajan wanne alqali zaka je?." Kiss ya yi mata a lips inta ya ce, "Kotu zanje na cewa alqali matata da Yayata sun ha a kai sun zubar min da ciki, ya yanke mu ku hukunci kuma ku biya ni cikina." Ta yi da riya tana kallon sa ta ce, "ta ya zamu biya ka?." Ya kalle ta ganin tana murmushi sai ya aga gira sama tare da rage girman idanunsa ya ce, "Ta hanyar bani ke na saka ki a aki baza ki fito ba har sai kin yi cikin mana...." Bata ce komai ba sai murmushi da take yi, ya zuba mata ido ya ce, "Ke in ce ai dole ma ki yi ciki da wuri, kullum canjawa ki ke yi daga zuma zuwa zam zam, ance babu abinda ya kai zam zam da i da magani ba? To shi ki ke komawa Hauwa!." Ta yi dariya ta ce, "Da in baki." "Da gaske nake, kin san bana yi miki da in baki ai." "Da gaske nake, da anyi magana abinda ka ke furtawa kenan, wannan kalma ta zauna a wannan aramin bakin nan naka" ta fa a tana nuna bakinsa tana murmushi. "Yanzu me ki ke so ki ci?." "Tsiren kan titi nake so, sai gurasa ta masu tsiren mai yaji." Omar ya girgiza kai ya ce, "An gama ranki ya da e, yanzu za a kawo miki, In kin ci sai me?." Ta lumshe ido ta bu e ta ce, "Sai nayi bacci a jikin my hero." Ya aga kai ya ce, "duk kin samu, bani mintina ka an zan kawo miki" ya fa a yana tashi ya fita ta bishi da kallo tana mamakin wayonsa, duk yadda take jin haushinsa da haushin cikin ya kau daga zuciyarta. Duk yadda Omar zai yi ya auke hankalin Nayla daga kan samun cikin nan ya yi, tarewa ya yi a gida ko yaushe suna tare sai dole ce take firar dashi. Zamansu tare yana rage mata damuwa, amma duk da haka akwai zazzaa i da ciwon kai da take fama dashi. In ya gaji da zaman gidan ya auke ta su fita su ta yawo sannan su dawo duk dan ta samu nutsuwa a zuciyarta. Cikin kwana biyun Didi na ta fama da ciwon ciki suna yawon zuwa dubata gida har ta samu lafiya. Cikin Nayla yana da wata biyu yayin da Musliha take da wata tara da an kwanaki a duniya. Laulayin da take yi ya an ragu sai zazza i, amma yawan yin amai ta daina. Tana son zuwa Kaduna amma bata so ta je Mama ta gane tana da ciki, dan babu wanda ta fa awa, kunya take ji a ganta da wani cikin dole ta ha ura da zuwan. Suna zaune ita dashi suna hira akan abinda ya shafi kasuwnacinsa da irin cigaba da ake samu Didi ta zo gidan. Nayla ta mi e tana yi mata oyoyo harda hugging inta, Didi ta ce, "ya arfin jikin?." Nayla ta ce, "ke za a yiwa ya arfin jiki ai Didi." Didi ta ce, "kedai Nayla, ni kam ai na warware." Omar ta kalla da Marmerh ta tafi da gudu ta haye jikinsa yana bata hannu suna tafawa. Didi ta yi murmushi ta mi a masa hannu ta ce, "Omar mu gaisa." Yatsine fuska ya yi ya ce, "in na i fa?" ya fa a yana mi a mata hannu suka gaisa ta ce, "so nake na ji umin anina." Murmushi ya yi ta zauna a gefe ya kalle ta ya ce, "Amma kin warware ko?." "Alhamdu lillah, na ji sau i sosai." "Allah ya ara miki lafiya Didi." Ta amsa da amin suka cigaba da hira har da ita, kafin ta kalle shi ta ce, "Omar bikin annenka za a yi na gidan Baba Adamu, mata zai aurar guda biyu da jika guda aya, takanas na zo na kawo maka iv." Kallon iv da take mi o masa ya yi ya kar a ya a watsar a gefe ba tare da ya bu e ba ya ce, "Allah ya bani ikon zuwa." "Amin, amma ka saka niya." Ta e baki yayi ya ce, "zan duba na gani. Tsabar neman wajan zama da shishshigi irin naki wai annena, mtsww!." Tayi dariya ta ce, "Allah ya kawo ranar da komai zai wuce a zuciyarka, Allah ya nuna min ranar da zan ga zuciyarka da fuskarka sun yi rauni, wannan wacce irin zuciya ce haka? Abu kusan shekara sha kaza amma ka kasa mantawa." Bai ce komai ba, ya dai yi murmushi kawai yana cigaba da biyewa Marmerh da take ta yi masa surutu. Didi ta ce, "to ni zan wuce, abinda na zo na kawo maka kenan." Ya ago ya kalle ta ya ce, "Sau aya ki ka ta a kwana a gidan nan, har na gaji da yi miki magana." Da mamaki ta ce, "ikon Allah! Omar da aurena zan zo gidan ka na tare?." "Amma saboda ke aka yi wajan, ba sai ku zo da mijin naki ko sati aya ku yi ba?." Ta yi murmushi tana girgiza kai ta ce, "Wata ran zamu zo Omar." "Haka ki ke cewa kullum ai." Bata amsa ba suna magana da Nayla. Omar ya taso ya zo kusa da ita ya ce, "wai me yake damunki? Naga kin canja gaba aya." Ta kalle shi tana murmushi ta ce, "ka san ai bani da lafiya ko?." "Amma yanayin naki ba na ciwo bane, akwai abinda ki ke so ne?." "Me zan so a duniyar nan Omar? Na je Saudia har sau hu u, a shekara aya na ziyarci madina sau hu u. Sannan ka kaini dubai, ka kaini England, ka kaini China, ka siya min mota, ka kuma canja min mota, ka bani wannan, ka bani wancan, me zan nema kuma Omar?." an adam ai ba a rasa shi da buri Didi, wata ila akwai abinda yake zuciyarki wanda ki ke so ni ban san shi ba. Ki fa a min ko meye don Allah, ko meye shi a shirye nake nayi miki Didi." Didi ta yi murmushi tana kallonsa ta ce, "Babu komai Omar, bani da wani buri na irin wa annan abubuwan a yanzu. Burina kawai ka shirya da danginmu, shine abinda zaka yi min ya saka ni farin ciki mai tarin yawa. Bayan wannan bana bu atar komai, domin duk wani abu na duniya na jin da i wallahi ka gama samar min dashi, babu abinda nake so." Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ina ji a raina kamar akwai wani gurbi da ban cike miki ba, meye Didi?." Ta sake yin murmushi ta ce, "Omar babu komai, ka amince dani kawai. In ba akwai gurbin bai wuce maganar danginmu ba Yaya Omar." Ya sauke numfashi yana murmushi jin sunan da ta fa a masa, ya ri w kafa arta ya ce, "in dai akwai wani abun waya aya ta biya miki bu ata." "An gama