← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 204 OF 205

Sashe 204

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wata manufa ba ko ka an, Allah yana gani ba da wannan manufar ya yi maganar ba itace ta canja mata ma'ana. Ajiyar zuciya ya yi ya fita jin ana kiran sallar magrib dan ya je ya yi sallah. Da daddare bayan sallah i'sha suna zaune a dining room kamar ko yaushe suna cin abinci, bayan an gama Nayla ta ta saka aka yi azkhar kamar yadda suka saba, duk da arfin yin ita da Marmerh ne sai Musliha da take an taya su. Aka gama aka shafa ta ce a tafi aki aje a kwanta Sai da ta kai su har akinsu ta kwantar da Marmerh da Musliha akan gadonsu da yake gefe ko wacce da na ta. Ta kwantar da Mufty akan nasa, dan bai yi girman da za a ware masa aki ba. Tayi musu addu'a sannan tayi pecking insu a kumatu. Ko wacce ta maimaita abinda Nayla tayi musu sannan suka, "Good night Mummy." Ta kashe hasken akin ta fita zuwa akinta. Muhsin ta auka da yake ta dariya, ta yi dariya tana jan hancinsa ta ce, "kai dai akwai arhar dariya." Zaunar dashi tayi akan gado, ya fara rararafe. Ita kuma ta shiga wanka bata jima ba ta fito, ta canja kaya zuwa nightwear ta zauna tana danna waya. Dan fushi take da mai gidan balle ta je inda yake. Diaper ta canjawa Mushin, ta canja masa kaya ta kwantar dashi tana yi masa wasa yana dariya tana dariya itama. ofar aka yi aka auko, sai ta auka su Marmerh ne ta ago tana cewa, "Marmerh baki yi....." ganin baban Marmerh sai ta yi shiru bata arasa ba, ya kulle ofa ya tako zuwa inda take ya zauna a gefenta. aukar anta ta yi ta ri e a hannunta, shi kuma yana so gudu wajan babansa. Shiru ya tsara tsakaninsu na wani lokacin. Omar ne yayi breaking silence in ya ce, "I'm sorry Jidda, ban fa i abinda na fa a da wata manufa ba, ke kika fassarata a haka amma ba haka nake nufi ba Jidda. Har abada bazan ta a cewa kina nuna banbanci a tsakanunsu ba, ke uwa ce a gare su gaba da baya, ke mahaifiyarsu ce dukkan su Jidda. Ki yi ha uri, na ga ranki ya aci har kina cewa zaki yanke ni." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta share sa bata ce komai ba. Omar jin ta yi shiru sai ya ce, "Jidda!." Nan ma ta share shi bata ce komai ba sai kallom hannunta da take yi. Calmly ya ce, "Jidda please!." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Dole raina ya aci ai, ni ina ganin na ri e Marmerh daidai da Musliha ashe kai kana ganin banbanci nake nunawa. In na cutar da Marmerh wacce riba zan samu? Kuma na fa a maka ko ba auren ka nake ba ni mai ri ewa Didi Marmerh ce. Amma kai ganin ka ke ita nake duka bana dukan sauran, kace bana tausayinta, zaluntar ta nake yi. Baka san me ta yi ba kawai ka yanke min hukunci.." Ya wara idonu waje ya ce, "Ni Jidda? Yaushe nace kina zaluntar ta Jidda? Yaushe nace bakya jin tausayinta?." Ta kalli idanunsa yadda suke a waje sosai ya saka ta auke kai daga kallonsa ta ce, "in ranka ya aci daman kana fa ar maganar da baka san ka fa a ba ai." Ya ri e hannunta guda aya ya ce, "Shikenan naji, duk da na san ban fa a ba amma ki yi ha uri, na kar i laifin duk da ba haka nake nufi ba amma ki yafe min." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah na ji haushin kalaman ka sosai, raina ya aci matu a, na ji a raina ban kai wani matsayi a wajanka ba, tunda har ka ke zargina akan arin cutar da Marmerh. Raina ya aci, nayi kuka, na ji ciwon abinda kace min. Da gaske azu bana son ganin ka, haushinka nake ji da kai da kalamanka." Muhsin ya ajjiye a gefensa ya ce, "don Allah ki bar maganar nan, ki daina fa a babu da in ji. Sannan na ce ki yi ha uri ai, na fa a miki ban fa a da wata manufa ba, da na san zaki fassara zancen zuwa wannan da ban fa a ba" ya fa a yana sake ri o hannunta. Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "hmmm daman in ka yi laifi ka san kace min na bar maganar babu da in ji, in ni nayi kuma akwai da in ji ai." Omar cikin sanyi ya ce, "Bana so kina tunawa ranki ya cigaba da aci shiyasa. Tunda na bada ha uri ba sai ya wuce ba? Allah ke ka ai nake bawa ha uri a duniya, ko lokacin da Didi take da rai ban cika bata ha uri ba sai naga dama, sai na wahalar da ita sannan zan bata ha uri, wani lokacin sai na saka ta kuka...." Sai ya dakata yana an murmushi tunawa da wahalar da ya bawa Didi. Ya sake matse hannunta ya ce, "Ke kuwa ko yaushe cikin sauke kai asa nake ina rarrashi da ban ha uri, ko dan wannan ki kar i ha urin mana." Nayla ta sauke numfashi tana kallon wani wajan daban, ya matsa hannunta da yake cikin nasa ta aga ido ta kalle sa. Ganin ya zuba mata manyan idanunsa sai ta ce, "na yi ha urin. Amma wallahi in har baza ka bari a yiwa aya daga cikin su fa a ba zaka yi danasani a nan gaba." "Shima na bari, da kaina zan dinga tsawatar musu bazan so su tashi a irin rayuwar da na tashi ba. Yanzu na san da i da zafin a, na kuma san zafin soyayyar a da mahaifi, gaba aya bana yi musu sha'awar irin rayuwata ta baya, ina yi musu sha'awar ilimi da ingantacciyar rayuwa. Ki bar maganar kin ji...? Shima na daina, da kaina zan dinga saka su kuka in abin su yi kukan ya tashi." Nayla ta kawar da kai kana ta ce, "wannan shine soyayya ta asali, ba soyayya bace kace baza ka ayi musu fa a dan kar ransu ya aci ba." Ya girgiza kai ya ce, "yanzu dai komai ya wuce ko?." Ta ta e baki ta ce, "ya wuce, amma wallahi ina jin haushinka da haushin kalamanka." Ya bu e idanunsa waje ya ce, "Ina zan saka kaina ni Omar, Jidda tana jin haushina! Me zan yi ki daina jin haushina? Fa a min Jidda, bana so ki kwana da haushina a zuciyarki. Ko na auko miki wu ar ki soke ni a duk inda ya yi miki?" Ya fa a yana murza yatsunta. Ta kalle sa ganin yadda ya wani marairaice kamar mutumin kirki sai ta yi dariya tana jinjina arfin wayonsa, in shi yayi laifi ya san hanyar da zai bi dan ta huce, amma in ita tayi masa a nan zata tuna Omar Tiger take aure. Nayla ta ce, "Yanzu dai ba da ban ne, kana da babar ar shekara shida, ta biyun tana biye mata da shekara hu u da wani abun gab take da shiga biyar, na ukun yana biye mata da shekara biyu da watanni, na hu un kuma gashi nan a zaune. To ka daina marairicewa min, yanzu kai Daddy ne ba Rouhi ba, iris ya rage ka fara ajjiye farin gashi." Ganin ta yi dariya sai ya samu sake ya ce,"Koma dai meye a wajanki har yanzu ni baby ne." Ta girgiza kai ta ce, "ka ga Babyna nan" ta fa a tana nuna Muhsin tana murmushi. Ya matso kusa da ita sosai ya ce, "Ni dai ki ce ya wuce kin daina jin haushina, kin ji Jidda ta?." Kallon sa ta yi ta an yi murmushi tana girgiza kai, mamaki yake bata in yayi wani abun. In laifin sane wani lokacin sai ya koma kamar ruwan zafi, in kuma laifin ta ne sai ya koma mata kamar wutar da take ci. Nayla ta ce, "na daina Rouhi." Kiss ya yi mata a bakinta ya ce, "Na gode Ashiqaty." Ta kuma yin murmushi bata basa amsa ba. "Na ji kina lissafa yara hu u da kika haifa min, yaushe zaki haifi na biyar in Jidda?." Ta zuba masa ido tana kallo ta ce, "Jaririn ana bai gama wari ba Rouhi, don Allah ka bari na huta kar na kwararra "Ba abinda zaki yi, in ma kin yin in ni ina son kayata. Don haka ki haifo na biyar in kin ji Jiddana?." "Allah ya sani bana son yin ciki nan kusa a yanzu, na fa a maka gaskiya ko, na fi so sai Muhsin ya samu a alla shekaru uku sai na sake haihuwa." "Kin auki mataki kenan." Ta girgiza kai ya ce, "Allah ne shaidata, babu wani mataki da na auka, fa a masa kawai nake yi akan ya jinkirta min zuwa gaba. Ka riga ka ce baka yafe ba ta ya zan yi a bayan idanun ka?." Ya harareta ya ce, "gaskiya ki daina, daman ke addu'arki ta an baiwa ce da kin yi Allah yake amsawa. Ni wallahi bana so, ki daina addu'ar haka. Meye kin kuma haihuwar yanzu? Albarka ce fa ba wani abun ba." "Rouhi." "Ashiq." "Haihuwa fa da wahala, kuma na haifo har guda hu u. Marmerh, Musliha, Mufty, Musin. Ko haka Allah ya bar mu ai mun more ko?." Ya ri e fuskarta ya ce, "Tabbas Allah ya yi mana kyauta mai girma ko a haka ya bar mu. Amma ina son ari Jidda, ina so ki ara koda guda biyu ne. Yadda arzu ina da samuna yake aruwa ina son arzu ana su aru." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ya bani, amma ba yanzu ba gaskiya. Kar ma ka ga na jima babu ciki ka fara harare-harare, na fa a maka ba yanzu ba." Ya yi murmushi tare da pecking inta a goshi ya ce, "Na ji, amma meye sirrin?." "babu wani sirri, na fa a maka addu'a nake yi." "Na yarda, amma shekara biyu." Ta kalle sa tana murmushi ta ce, "yadda ka ke son yara Allah ya cigaba da baka ikon kula dasu bisa tarbiyya mai kyau."
Chapter 204 · 0% Book details