Sashe 67
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shawara kawai, in dai kuna so na cigaba da zama cikin nustuwa ku bani shawara." Didi ta ce, "Dole ka yi ha uri na wani lokaci, kamar yadda iyayenta suka ce zasu bata dama to ka yi ha uri ka ji me zata ce. In ta amince da kai daman abinda mu ke so kenan, in bata amince ba sai mu ha ura." Omar ya yi mata banzan kallo yana harararta cike da fa uwar gaba ya ce, "a ha ura da me?." Didi ta ce, "mu ha ura da ita mana." "Mtsw! wani lokacin kamar kina shaye-shaye. Yanzu kina tunanin akwai abinda zai saka na rabu da ita a kaf duniyar nan? Ko meye zan yi ya i dashi wajan ganin na yi nasara a kansa. Ai wallahi ko iyayenta ne zasu ce na rabu da ita a yadda nake jin zuciyata bazan rabu da ita ba. In kaf duniya ne zasu taru a kaina a saka min wu a a wuya ace na rabu da ita wallahi sai dai su kashe ni, in suka kashe ni su kawo miki gawata." Zata yi magana ya katse ta ya ce, "Don Allah kar ki ata min rai, ki bar ni da iya abinda yake raina ki adana kalamanki bana so, kar ki sake tarwatsa min tunani. Kar ma ki sake saka min baki, da mijinki nake magana ba ke ba." Abdulhamid shi dai dariya yake yi sosai, saboda dramar Didi da Omar abar dariya ce, umarni yake mata kamar shine yayan itace anwa. AbdulHamid ya ce, "ka yi ha uri Omar, ka bada lokacin kamar yadda akace, ni na tabbatar baza ta i dawowa gareka ba. Kaine fa Tiger, ga kyau, ga aji, ga nutsuwa, ga kuma soyayyar da ka ke yi mata, ta ya zata bari wannan damar ta ku uce mata?." Wani irin kallo Omar ya yi masa ya ce, "Matar ka bata fa a maka bana son zuga ba? Haushi take bani, na tsani a zuga ni, ka fa a min gaskiya ba abinda zan ji da i ba." Abdulhamid ya sake yin dariya mai sauti ya ce, "ba zuga ba ce Omar, amma tunda baka so shikenan. Maganar gaskiya sai ka jira tukunna, sannan ka yi ari kana ganinta ko kana waya da ita, hakan zai sake nuna mata da gaske kana sonta." Omar ya an yi shiru yana jin nauyi a zuciyarsa sannan ya ce, "Bani da number ta, kuma ni babban tashin hankalin ban san me zance mata ba, ban iya magana da ko wacce mace ba a duniya sai Didi, ban san ta ya zan fa i maganar da zata amince ba." Didi ta ce, "Da ka fara maganar zaka ji tana fitowa daga zuciyarka Omar. Wai kamar baka so Narma ba? In kana waya da ita da wanne irin kalamai ka ke amfani wajan yi mata magana?." Ya kalle ta yana bu e idanu ya ce, "Ai na ce ki daina saka min baki ko? Kuma ita Narma ban ta a rarrashinta ba, ban ta a tsayawa na yi wani abu dan faranta mata ko dan nuna ina sonta ba, ko yaushe itace take takura min da waya, na kan manta da ita in ba kirana tayi ba. Ki daina sakata a maganata. Magana ake ta wacce nake so ba waccan sharar ba, ki daina ha ata da matata kamar cin fuska ne a gareta." Didi ta ce, "yi ha uri, amma ya kamata ka koyi yadda ake tafiyar da soyayyar mace, musamman kai da ka fa a mata kalamai marasa da i. Ka nemi class na koyar da tattalin mace ka shiga" ta arasa fa a cikin sha iyanci tana dariya. AbdulHamid ya ce, "Omar ita soyayya wani lokacin sai ana ha awa da arya tafi armashi, zaka iya fa a mata wani abun wanda kai kanka ka san arya ka ke yi itama tasan arya ne amma zata ji da i a zuciyarta." Omar ya hakimce yana wara idanu yana kallon Abdulhamid ya ce, "Oh to ke kin ji Didi, daman can wasu kalaman na sa ba na gaskiya bane arya ya dinga jera miki har ki ka aure shi." Didi tayi aramar dariya dan bata jin da in jikinta dauriya kawai take yi. Omar ya kalli AbdulHamid da yake ta dariya ya ce, "Ban tsara rayuwata akan arya ba, dan haka bazan tsara aurena a kan arya ba, duk kalaman da zan fa a zan tabbatar da na gaskiya ne zan sanar da ita. Dukkan ku taron tsintsiya ne babu shara, dana sani ma ban zo ba" ya fa a yana shafa kansa. Didi ta ce, "Ka ga ka yi duk abinda ka ga ya kamata, amma sai ka yi ha uri gaskiya, wannan gaggawar bazata saka ta dawo ba. Kuma ya kamata ace an ha a mata lefe, tunda yanzu kana son aurenta ya kamata ayi mata lefe kamar ko wacce mace." Ya kalli Didi ya ce, "kin san da hakan ki ka saka na kwashe ku ina na siyi waccan motar?." "Yanzu abin ya zo raina ne Omar." "Ana kashe nawa?." "Iya arfin ka iya ku in da zaka kashe. Ba zaka yi abinda ya fi arfin ka dan a burge ba, duk abinda zaka bata tafi arfinsa dan kawai kayan aure suna da da i." "To ai baki da lafiya, waye zai yi wannan aikin in ba ke ba?.." Didi ta ce, "Zamu ga ni dai, bara mu ga zuwa yaushe zata dawo." Omar ya bita da kallo sosai cikin kulawa ya ce, "kina lafiya kuwa? Ni ban yarda dake ba, kin canja gaba aya." Didi ta ce, "na gaji ne kawai, kwanciya zan yi." Omar ya ce, "ki je ki kwanta, nima zan tafi yanzu." Wayar Didi ya auka ya auki number Nayla ya ce, "in wani yaji bani da number ta akwai raini a ciki, ko iya ganin number ta zai rage min kewa." Murmushi ta yi kawai suna hira da AbdulHamid ka an-ka an har ya raka shi ya tafi. Kusan raba dare Omar ya yi yana kallon number Nayla, ya rasa wanne suna ya kamata ma ya saka mata. In ya saka Nayla ya goge, in ya saka Hauwa ya goge, in ya saka Jidda ya goge ya rasa wanne ya kamata ma ace ya saka mata. Shi su my love, my world in nan duk basa burge shi balle ya saka. A haka ya yi bacci ba tare da ya yi saving number ba. arfe takwas na safe ya farka saboda arar wayarsa, da ya duba sai ya ga AbdulHamid ne auka da sauri tunawa da ya bar Didi babu lafiya a jiya. Yana auka AbdulHamid ya ce, "Omar Aisha ta haihu, ta haifi a mace." Wata wawiyar ajiyar zuciya Omar ya yi, farin ciki ya mamaye masa zuciya lokaci aya. Cikin zumu i ya ce, "Da gaske? Tana nan Lafiya? A wanne asibitin ta ke?." Abdulhamid ya ce, "Muna nan asibiti da yake kan kwanar layin mu, yanzu haka lafiyar ta lau." Omar ya ce, "gani nan" ya fa a yana kashe wayar ya tashi da sauri. A gaggauce ya shirya ya kira Goje a waya suka fita tare a motar. Asibitin suka je Omar ya ga AbdulHamid a tsaye suka gaisa ya nuna masa akin ya ce, "tana ciki." Omar ya arasa akin ya bu e ya shiga da sallama. Mata uku ne suka amsa masa har Didi, kallo aya ya yi musu ya kawar da kai gefe ya arasa wajan Didi yana kallon ta kamar yadda take kallonsa. Murmushi ya yi ya ce, "kin san zaki haihu baki fa a min ba tun jiya? Kina lafiya amma ko?." Didi ta yi murmushi ta ce, "ai nima ban san da haihuwar ba Omar, yadda suka rubuta na rage sati aya na haihu." "Kina lafiya dai ko?." "Lafiya lau Omar, na warware sosai, da yake ai tun jiya ne." Omar ya kalle ta ya ce, "Tun daren jiya kika haihu amma da yake an raina matsayina ba a kira ni ba sai yanzu?." Didi ta ce, "Cikin dare ne fa Omar." Omar ya ce, "Ina tsoron dare ne ni? Meye amfanina in ban zo ba? Da wani abun ya same ki fa?." Didi ta ce, "to ka yi ha uri, yanzu tunda lafiya lau nake ba shikenan ba?. Ga arka" ta fa a tana nuna masa gefen ta. Zubawa yarinyar ido ya yi tare da kai hannu ya shafi fuskarta sai ta motsa, ya yi murmushi yana kallon yarinyar. Didi ta ce, "ka auke ta mana." Ya girgiza kai ya ce, "A'a Didi, bazan iya aukarta ba, zan ga kamar zan karyata ne, yaleta kawai." Didi ta auke ta cak ta saka masa a hannunsa ta ce, "ta ya zaka ce baza ka auki arka ba? In ma ka karyata in ba arka ba ce? In baka auketa ba tana da wani Uncle in ne bayan kai?." Zubawa yarinyar ido ya yi yana kallonta idanunta a rufe, bai ta a jin son abu ya shiga zuciyarsa farar aya ba sai son yarinyar, ji yake sonta na shiga zuciyarsa sosai kamar shine mahaifinta. Ya yi murmushi yana kallon ta ya kalli Didi ya ce, "Kamar ku aya." Didi ta yi murmushi tana kallon sa shima yana murmushi yana kallon yarinyar. "Didi auke ta, hannuna yana rawa kar na ar da ita, ban ta aukar jariri ba sai ita." Didi ta auke ta ta ajjiye a gefe ya bita da ido yana murmushi. Karaf suka ha a ido Saroot anwar Mamansa, tunda ya shigo ya san sune a akin shiyasa ko kallon inda suke ma bai yi ba, amma sai da ta saka suka ha a ido. Mama Zainab ce ta ce, "Omar barka da safiya, ashe kuma anyi ar kuma? Allah ya raya ta." Tsam ya tsuke fuska duk murmushin da yake yi ya gushe lokaci aya. Didi ta kalle shi ta ce, "Omar ana yi maka magana." Bai saurare ta ba ya auke kai, baya son yayi abinda zai ata masa farin cikin da zuciyarsa take ciki da ya basu mamaki wallahi. Kuma da laifin Didin, dan ta raina masa hankali ace har sun riga shi zuwa inda ta haihu? Za su gamu ne da ita bara ta warware. Girgiza