Sashe 115
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ki bari bana jin da in wannan maganar da ki ke yi, Kuma ai Allah ne ya addara faruwar komai baki da hannu a cikin duk abinda ya faru. Don Allah ki daina bana so." Mama zata sake magana Nayla ta ce, "don Allah Mama ki bar maganar nan, ki yi ha uri ki bar maganar bana son ji ko ka an" ta fa a tana toshe kunnenta tana kuka. Abiy da yake jinsu ya ce, "Zo Mamana." Ba musu ta koma kusa da Abiy ya share mata hawaye ya ce, "Ki nutsu." "Abiy kana ji me Mama take cewa fa, in ma laifin ta yi min ba uwata ba ce meyasa take neman afuwata? Wanne laifi Mama zata yi min da zata ce kunyata take ji har na dinga kiranta ta auka?." Abiy ya ce, "neman afuwarki yana da kyau tunda laifi tayi miki Nayla, amma tunda kin ce bakya son ji shikenan." Nayla cikin muryar kuka ta ce, "Ni bana so." "To ai an bari" Abiy ya fa a cikin rarrashi dan ya san halinta. Jawad dai bai ce komai ba sai ma tashi da ya yi ya fita Jalila ma ta tashi ta bar wajan. Nayla ta kalli Mama ta ce, "Mama ni baki min komai ba don Allah ki daina fa a, in kina so nayi farin ciki ki daina cewa na yafe miki." Mama ta yi murmushi ta ce, "Na daina Nayla." "Baza ki sake aukar wayata ba?." "Bazan sake ba Nayla." "Kuma a akinki zan kwana." "To Nayla" ta fa a da murmushi tana kallonta amma a zuciyar ta gaba aya babu da i, ta rasa me ya kai ta har ta yi arin cutar da Nayla wacce ta raina da kanta. Ina ta tuna hakan sai zuciyarta karye ta fara zubar da hawaye. Nayla tashi ta yi ta shiga aki, Mama ta kalli Abiy ta ce, "na san ban kyauta ba da na biyewa zuciya, amma yanzu wallahi na yi nadama bazan sake arin aikata abinda na yi ba, ka yi ha uri. Tun ranar da aka yi maganar nan ban samu arfin guiwar baka ha uri ba sai yau." Abiy ya ce, "ta ya zaki bani ha uri kin koma wasan uya da mutanen gidan?." Mama ta kalli Abiy tana hawaye ta ce, "Kunya ce Abiy, kunyar ha a ido da kai nake yi, kunyar su Jawad lullu e ni take yi da zarar na ji maganarsu balle na ha a ido dasu. Nayi kuskure, na so na aikata abinda zan bar baya da ura, duk da na aikata in amma na gane kuskurena wallahi. Ka yi ha uri ka yafe min." "Ni baki min laifi ba ai, in ma kin yi Allah ya hukunta ki tun ba a je ko ina ba, iya kunyar anki da ki ka ji babbar jarabawa ce a gare ki, baza su ta a mantawa da wannan abun da ki ka aikata ba har abada. Na aga miki afa tun farko saboda na san ke ar adam ce, dole ki yi kuskure a wani angaren. Amma in aka duba alkhairan ki ga Nayla sai alkhairin ya shafe kuskuren da ki ka aikata. Tunda kin gane abinda ki ke arin yi ba mai kyau bane ai shikenan, Allah ya yafe mana gaba aya. Kar ki sake yiwa Nayla maganar ki yaleta kawai, bata fahimce ki yadda ya kamata ba kawai ki bar maganar. Mijinta kuma duk ranar da ku ka ha u ki yi arin wanke laifin da ki ka aikata." Mama ta ce, "in sha Allah, Na gode." Bai ce komai ba ya tashi ya hau sama ita kuma ta shiga aki. Nayla tana akin ta wanda aka gyara mata daga zuwanta, ta auki waya da niyar kiran Omar ta ga kiransa har sau biyar tun tana bacci. Murmushi tayi zata kira shi kenan wayar ta yi shutdown. Dafe kai ta yi da sauri ta auko charger ta saka sai ta bar wajan ta tafi akin Mama da niyar ta dawo. Da ta je akin ta zauna ta dinga jan Mama da hira har ta an sake ka an suna hira da dariya kafin ta koma nata akin. Number Omar take kira amma bata shiga ta gwada yafi sau goma amma bata tafiya. Ta yi masa text message ta fita zuwa akin Mama a can tayi kwanciyarta. Washe gari tana tashi Omaar ne yazo ranta, ta auki wayar ta duba ga mamakin ta babu kiransa ko aya. Ta kira shi ji tana ringing, ta yi murmushi saboda ta yi missing voice insa tana jira ya auka amma sai ta ji an katse kiran, abin ya bata mamaki ta sake kira aka sake katsewa arshe sai wayar ma ta daina shiga. Tunani ta tsaya yi me hakan yake nufi kenan? Yana sane yake katse kiran ko kuma network ne?. Tunanin ta ya bata network ne kawai dan ta san babu wani abu mai mahimmacin da zai saka ya katse mata kira. Bayan sun karya sun yi wanka suka fita ita da Jalila. Shagon su ita da Tiwny suka fara zuwa, Nayla taga shagon da yadda aka sake fa a shi komai ya yi kyau sosai kuma ana ciniki ma sha Allah. Daga nan sabon shagon Omar na Kaduna ta je ta ga yadda yake daga nan suka wuce gidan Yaya Ahmad da ya yake ya zo hutu yana Kaduna. Nayla gwada kiransa take ta yi amma bata shiga duk ta damu, ta yi message bai bata amsa ba gaba aya hankalinta ya dawo Kano cikin damuwa. Wayar Jalila ta kar a ta kira shi abin mamaki wayar ta shiga, bata gama mamaki ba sai da taga ya auka daga can angaren ya ce, "Hello." Nayla jin ya auka sai jikinta yayi sanyi da tunanin kenan wayarta ce bazai auka ba ko me?. Jin ya sake maimaita hello ya saka ta ce, "Rouhii!." it ya katse kiran ba tare da ya ce mata komai ba. Nayla hankalin ta ya tashi, ta kira ta ji ya saka number Jalila a inda ya saaka numberta. Nan da nan ta rubuta message ta tura masa a wayarta amma har suka baro gidan Yaya babu reply. Gaba aya ta shiga damuwa, koda ta dawo sai da Mama ta tambaya me yake damunta ta ce babu komai. Tana ji Abiy yana fa awa Mama ai Omar ya kira shi yana fa a masa sun bu e shago a garin, Nayla bata ce komai ba tana mamakin kenan itace dai bazai auki wayarta ba kenan ko me?. Gaba aya sai zaman ya dame ta, da yar ta iya kaiwa ranar juma'a da safe Baba Salisu ya auko ta zuwa Kano. Bai san zata dawo ba baya gidan ya fita, Allah ya taimaka da key in gidan a hannunta ta shiga ta tarar da komai tsaf kamar ko yaushe, ta shiga aki ta yi wanka ta yi sallah ta dafa abinci ta ci ta ajjiye masa nasa. Shiru babu labarinsa har dare, sai tara na dare sannan ta ji motsin shigowarsa. Da hanzari ta fito falon a lokacin da yake shigowa kawai ya ganta a tsaye. auke kai ya yi daga kallon ta ta ce, "YaMar!." Kallon ta ya yi ya watsar kamar bai gane ta ba, bai ce mata komai ba ya ra a ta ya wuce. Nayla ta shiga damuwa, jikinta a sanyaye kafin ta shiga ciki ta same shi a zaune yana amsa waya yana kuma rubutu da alama abinda ake fa a masa yake rubutawa. Yanke wayar ya yi ya ajjiye bai kalle ta ba ta ce, "Rouhii!." Banza ya sake yi mata bai kula ta ba, zata sake magana ya riga ta ya ce, "Ya isa! Fita ki bani waje bana son surutu!" Ya fa a fuska a aure. Nayla da mamaki take kallonsa jin abinda yace, ta ce, "Rouhii ni ka ke cewa baka son surutu?." "To ke in wace? Uwata...?" Ya fa a yana bu e mata ido. Nayla gabanta ya fa i, ta auke kai daga kallon sa ta ce, "Rouhi me ya faru?." Bai kula ta ba ya sake share ta, ta ce, "laifin me nayi maka haka?." "Baki ji me na ce ba kenan?." Zata yi magana ya ago ya watsa mata idanunsa yana an bu e su ka an a kan fuskarta, sai ta yi shiru ya nuna mata ofa ya ce, "ki bar akin nan." Nayla ta ha e fuska cikin shagwa e ta ce, "Ban san laifin da na yi maka ba, kuma...." Cikin murya mai kaushi da tsawa ya ce, "na ce ki fita ko?." Duk da ba tsawa ya yi mata sosai ba amma sai da jikinta ya yi rawa, domin kuwa ya canja mata daga Omar ya koma mata Tiger wanda ta sani a baya. A sanyaye ta fita ya yi aramin tsaki ya auke kai bai bari ya cigaba da tunanin ba ya cigaba da abinda yake yi. Ta jima da fita bai ji motsinta ba, duk sai ya damu da rashinta dan ya yi tsananin kewarta, yana so ya nuna mata kuskuren da ta aikata ne ko dan saboda gaba. Zuciyarsa umarni take bashi akan ya je wajanta, nauyin zuciya yake ji saboda kewarta da yake ji a jikinsa. Ajiyar zuciya ya yi tare da kulle idonsa, a lokacin ya ji ta bu ofar ta shigo akin. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke cikin farin cikin ganinta, bai nuna mata ba yana kallon ta ta gefen ido. Da ta shigo bata kula shi ba ta itama je ta kwanta a inda ta saba kwanciya, shi kuma yana daga zaune a inda ta bar shi. Jin bai yi mata magana ta gyara kwanciya amma hasken ya dame ta. Kukan shagwa a take yi asa- asa, tun baya ji har ta kai ga yana jin kukan, ya ago a fusace ya ce, "Ko ki daina yi min kuka ko ki tashi ki fita, dama ban gayyace ki ba ko!?." Shiru Nayla tayi ta rufe ido bata ce komai ba, irjinta bugawa yake yi dan ta saba da sabuwar rayuwar da suka fara, wannan abi'un nasa ta manta dasu, gashi yanzu ya dawo mata Omar in da ta sani a baya. Omar ya yi tsaki ya cigaba da abinda yake yi.