Sashe 105
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jiki a sanyaye ya fara karanta abinda yake rubuce. _Assalamu alaika Abiyna. Na san lokacin da message in nan zai same ka na jima da zuwa Kano, kayi ha uri Abiy ban tafi dan ata maka rai ba, na tafi ne saboda na samarwa kaina kwanciyar hankali da nutsuwar zuciyata. Abiy Ina son Omar, Ina so nayi rayuwa dashi, babu namijin da nake ji zan iya rayuwar aure dashi sai shi kawai. Hakan ba laifina bane Allah ne ya ora min ban kuma isa na cire da kaina ba. Abiy zan iya rasa raina in kace bazan auri Omaar ba, zan kuma iya rabuwa da kowa dan nayi rayuwa dashi Abiy. Na tafi wajan dangin Ummana, na san su baza su iyi min abinda nake so ba, duk da Omaar ya kasance ba irin wanda ake so bane amma na tabbatar zasu san yadda zasu yi wajan samar min da farin ciki. Na san su zasu bani farin cikin da ka kasa bani Abiy, dan wallahi in ba a aura min shi ba sai na shiga duniya!. Da wannan nake shaida maka Abiy Ina Kano wajan Hajja, Ina son Omar Abiy, Ina matu ar sonsa, na kasa jure abinda kai da Yayanmu ku ka cewa shiyasa na yanke hukuncin tafiya Kano ko dan na samu nutsuwa. Ka yi ha uri in na ata maka rai Abiy, sai anjima._ Ahmad gumi ya wanke masa jiki da yar ya kai arshen sa on, ya ago a hankali kafin ya yi magana Abiy ya ce, "akwai wani ma, duba Ahmad." Bai musa ba ya sake scrolling asa ya sake ganin wani message in kamar haka; _Abiy in dai baka amince na auri Omar ba wallahi Allah sai na shiga duniya, sai na ata maka suna, sai na yi video na ora a social a media na ce ka hana ni auren wanda nake so, wallahi Abiy sai na lalata tarbiyyata yadda baka yi tunani ba. In har ba a aura min shi ba zan shiga duniya na lalace, in na shiga duniya bazan sake dawowa gare ku ba har abada. Inda ace mahaifiyata tana da rai da hakan bazai faru ba, ita ai tana sona baza ta wula anta ni ba. Abiy zan aikata abinda nace akan soyayya, zan iya kashe kaina a kan son da nake masa. Ka yi ha uri Abiy, na san zaka ji babu da i, zaka ga kamar ni Nayla da ka ke cewa Mamanka kamar na yi disappointing in ka ne, ba haka bane Abiy, soyayyar Omar ce. Zan zauna dashi ko da zai dinga yankar naman jikina kullum, a haka nake sonsa nake aunarsa. Ka yi ha uri!._ Ahmad ya ago a sanyaye suka ha a ido da Abiy, Abiy ya kar i wayarsa yana nuna Mama ya ce, "Duk aikinta ne, ita ta saka aka yi hacking account in Nayla aka turo min wannan." Ajiyar zuciya ya yi mai nauyi ya ce, "Na rasa me ya shiga kaina a lokacin har na amince Nayla zata iya rubuta wannan sa on ta turo min, na kasa yarda ni da kaina ni ne na amince Nayla ta rubuta wannan sa on ta turo min. Ban yi mata adalci ba, bai kamata na yankewa Nayla hukunci akan abinda nake da tabbacin bazata aikata ba. Ba tarbiyyar da na bata ba ce, ba halinta ba ne. Amma addarar aurenta da Omar ta gifta, shiyasa na amince lokaci aya ba tare da tunanin komai ba." Ya kalli Mama da ake jin sautin kukan ta a akin ya ce, "da kin kwantar da hankalinki baki ha a wannan makircin ba Omar dai shine mijinta, da kin tsayar da hankalin ki waje aya ko baki nemo auren ba zai kawo kansa saboda shine mijinta. Amma sai ki ka yi shigar sauri, ki ka auki alhakin marainiyar Allah wacce bata tsare miki komai ba. Kin bani kunya, kin bani mamaki wallahi!." Shiru ya ratsa akin, babu abinda yake tashi sai kukan Mama wanda take yin sa cike da dana sani da kunya mai yawa. Abiy ya kalli anta ya ce, "Ku yiwa mahaifiyar ku fa a, ku nusar da ita duk ladan da ta samu na kula da Nayla wallahi ya zube, ta bar shi ya bi rariya saboda banzan ku urin da yake zuciyarta. Ku yi mata fa a ta canja hali ko dan saboda Jalila da bata aurar ba. Jidda ma da ta aurar bata tsira ba indai bata wanke zuciyarta ba. Sannan ku fa a mata in sha Allah zaman Nayla da Omar baza ta yi kuka ba, zata yi farin ciki fiye da wanda ta yi a gidan nan, zata samu walwala wacce bata so ta samu. Na yi shiru da maganar ne saboda bana so Nayla ta san babarta ce ta shirya komai na auren nan, ita Nayla umarninta kawai take bi saboda ta yarda da ita a matsayin uwa ta san baza ta cuce ta, ashe ita da biyu take yin hakan. Bana son Nayla ta ji maganar nan balle danginta, baban abin kunya ne a gare mu gaba aya ace daga gidan nan aka ulla wannan kitumurmurar. Sannan ko dan Jawad da yake neman aure a ahlin babar Nayla!. Fitar wannan maganar babban abin kunya ne a gare mu baki aya!" Yana fa a ya fita ya barsu jiki a sanyaye duk suna kallon mahaifiyarta su zuciyarsu babu da KRB3P062 Ahmad da yake tsaye jiki a salu e ya kalli an uwansa ya kalli Mama ya ce, "Mama abinda mu ka ji bai dace da ke ba ko ka an." Mama ta auke kai bata ce komai ba. Jalila da take kuka ta ce, "Yaya sai da na cewa Mama ta bar abinda take fa a a gidan Anty Nayla, Anty Nayla tana kuka amma Mama bata daina fa awa mijinta magana ba." Jidda ta araso da Mihada a hannunta ta ce, "Mama me Nayla ta yi miki haka? Ta ta a yi miki wani laifi ne?." Mama ta goge idanunta bata ce komai ba dan bata san me zata ce musu ba, kunya ta gama rufe ta ko ha a ido bata so ta yi dasu. Jawad ya ce, "Mama Nayla ta ta a yi miki wani abu ne? Meyasa ki ka zama silar aurenta da Omar don Allah?." Mama bata ce komai ba dan kunyarsu take ji sosai. Ahmad ya ce, "Koma meye a zuciyarki don Allah Mama ki ajjiye shi a gefe. Meye laifin Nayla? In ma laifin marigayiya Umma ne ya shafeta sai ki yi mata adalci, lokacin da abin ya faru ba ma a yi tunanin za a samu Nayla ba, kuma matar nan kin ce kin yafe mata tun kafin ta bar duniya, to meye na dawo da maganar nan kuma Mama?." Mama bata ce komai ba sai kawar da kai da tayi, a tausashe ya sake cewa, "Ke ki ka raini Nayla, ki ka bata tarbiyya daidai da wacce ki ka bawa Jidda. In ba fa an aka yi ba babu wanda yake auka Nayla ba arki ba ce, saboda bakya banbanta ta da Jidda wacce ki ka haifa. Mama laifin da ki ke tunani an yi miki har zaki auki fansa a kan Nayla ita ta san anyi? lokacin da abin ya faru tana ina?. Kuma Mama kin ce kin yafe mata tun kafin ta bar duniya, ku ka cigaba da zama na aminci da jin da i da kuma walwala, meye na dawo da hannun agogo baya....?. Kina fushi akan abinda ta yi miki a gidan nan, daga arshe kuma ta mutu ta bar ki da gidan, da mai gidan, da kuma aya da ta haifa a duniya. Mama ko iya wannan ya ishi bawa ya yi darasi, amma ki ka zobe ladanki, ta hanyar son ganin Nayla ta wahala, meyasa Mama?." Yaya Ahmad ya sake cewa, "yanzu Mama wacce riba zaki samu in Nayla ta wula anta a gidan mijinta? Don Allah da me hakan zai amfane ki?." Jawad a sanyaye ya ce, "babu." "To meye amfanin hakan? Yarinyar nan tana kallon ki matsayin uwa a gareta, ta yarda da ke ta amince baza ki cutar da ita ba, ashe duk abinda ya faru a ashin umarninki ne, tana bin umarninki saboda yardar da ta yi dake meyasa haka Mama?. Yanzu Mama da kan ki kika rubutawa Abiy wannan dogon message in ki ka tura masa kawai saboda cikar burinki a kanta. Allah sarki baiwar Allah, shiyasa ta fita daga hankalinta, ta gigice, ta kasa gane me ta aikatawa mahaifinta ya yanke wannan anyen hukuncin a kanta. Mama ko ha inta da ki ka auka in bata yafe miki ba wallahi sai ya bibiyeki, bata san laifin da ta yi aka yanke mata hukunci cikin fushi. Kuma Mama ta ce miki ta ha ura da auren Omar ki ka ce a'a kar ta ha ura, saboda uwa ki ke a gare ta sai ta amince da duk abinda ki ka ce, saboda bata da mahaifiya ke take kallo a wannan matsayin. Mama anya Nayla ta cancanci wannan hukuncin daga gare ki kuwa?." Mama dai bata ce komai ba, ta sunkuyar da kai kamar tana saurarensa, yadda yake magana a tausashe ratsa zuciyarta maganar take yi. Ahmad ya ce, "Mama in aka cutar da Nayla akwai Jidda, akwai Jalila, in aka yi fatan ta auri wanda zai wahalar da rayuwarta muna da tabbacin rayuwar Jidda a gidan mijinta zai ore da farin ciki? Ko kuma muna da tabbacin ita Jalila zata je inda zata yi farin ciki?. Annabi Muhammad S.A.W cewa ya yi ka so wa an uwanka abinda ka ke so wa kanka. Yanzu gashi kin so rayuwar Nayla ta kasance cikin ba in ciki, sai gashi tun ba a je ko ina ba ta fara kasancewa cikin farin ciki da walwala a gidanta. A nan me Allah yake ke nunawa? Allah ya nuna mana shine yake da iko da bawansa a kan komai a kuma ko yaushe, duk yadda ka kai ga son cutar da wani sai Allah ya yarje maka, haka duk yadda ka kai ga son faranwata wani sai Allah ya yarje maka. Kuma inda mutum yake kai ka a rayuwa Allah ya kan canja in babu shi a cikin addararka. Tun farko