Sashe 161
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abinda bana ra'ayi kuma bana so. Duniya gaba aya a kan hotonki take magana, ni ba banza ba ne da zan ji alfahari dan wani ya yabi matata ba......" ya auke ido daga kanta, kafin ya sake kallon ta ta ce, Ki ta shi ki bani waje na ce ko!?." Nayla zata yi magana cikin tsawa ya ce, "in kika yi min magana sai na fasa miki baki, ki bar wajan nan ko na nuna miki asalin waye ni!." A hankali ta mi e ta bar falon bata ce komai ba, ya yi tsaki ya auki wayarsa ya shiga TikTok, bai yi seconds biyar yana scrolling ba ya yi karo da video sa shida Nayla da kuma Musliha. Kishi da haushi suka sake kama shi ya furzar da iska ya cillar da wayar. A haka ya kwanta cikin takaici da acin rai, in dai zai farka sai ya duba wayarsa, amma baya jimawa yana scrolling zai ga ga abinda baya so, arshe kashe wayar ya yi cikin ba in ciki da takaici. Cikin wanda suka ga video Nayla da Omar harda Narma, Narma ta ru e ta saka hotunan a gaba tana kuka. Dad da yake zaune a kusa da ita ya ri e hannunta ya ce, "Haba Narma meye haka kuma? Baki yarda da abinda nace miki bane ba wai?." Narma ta ce, "Dad kalli matar shi, kalli yadda yake farin ciki kana gani ka san yana sonta. Dad ni ce baya so, Dad bazai aure ni ba, shikenan mutuwa zan yi." Ta fa a cikin kuka mai tsanani. Mum ta kalle ta cikin tausayi ta dafata ta tace, "ki yi ha uri Daughter, kin ga saboda ke mu ka zo Kano dan a same shi a yi magana, in kina wannan kukan sai ki saka mu ga kamar har yanzu kina ganin bamu kyauta miki ba." Dad ya ri e hannunta ya ce, "Zan je na same shi da kaina nayi masa magana, na tabbatar zai amince ya aure ki tunda yana sonki yana aunarki, na tabbatar zai amince ya aure ki in sha Allah, so don't be nervous." Ta kwantar da kanta a kan kafa ar Dad ta ce, "Dad da gaske zai amince?." Dad ya ce, "zai amince ya aureki, I promise you zan san yadda zanyi ya amince ya aure ki daughter. Kar ki damu ki kwantar da hankalinki." Ta goge idanunta tana cigaba da kallon hoton Nayla da Omar zuciyarta na bugawa sosai. Hankalinta ya gama tashi gani take yi bazai amince ya aure ta ba tunda yana da matarsa mai kyau gashi har ta haihu. Washe gari da safe Dad da Mum suna zaune suna breakfast Narma ta fito taja kujerar dining ta zauna, Dad ya kalle ta kafin ya yi magana ta ce, "Morning Dad." Dad ya ce, "Ya ki ka tashi Daughter?." "Fine" ta fa a tana ha a tea tana sha bata sake cewa komai ba. Dad ya ce, "nayi waya an tabbatar min da yanzu yana office, in na fita zan je na ha u dashi." Narma ta aga kai kawai bata ce komai ba. Mum ta ce, "ki kwantar da hankalinki dear, komai zai zama daidai." Kai ta aga bata ce komai ba ta mi e da mug in hannunta ta hau sama. Mum ta kalle shi a raunane ta ce, "Dear anya yaron nan zai amince da auren Narma?." "Zai amince in sha Allah, kar ka damu in sha Allah zai amince. In bai amince ba ya zamu yi da Narma? Ai sai ta samu heart attack." Mum ta yi tagumi ta ce, "wallahi na damu sosai, bana son wani abu ya samu Narma wallahi." "Saboda ita zan je na same shi amma bayan haka ke kin san bazan je ba, amma zan je saboda mu san abinda zai faru, Na san bazai i amincewa ba tunda yana sonta. Kuma a matsayin da yake dashi yanzu abin alfaharinsa ne ace yana da inlaw kamar ni." Mum ta girgiza kai ta ce, "to ba dole ma ya amince ba, ai dole ya amince ya aureta ko baya so." Shiru ya yi ya girgiza kai bai ce komai ba ya mi e ya fita. Omar da safe koda ya tashi shiryawa ya yi ya fito falo ya tarar an ajjiye masa kayan breakfast. Zama ya yi yana ci, a lokacin Nayla ta shigo da sallama hannunta auke da Musliha. Sallamar ya amsa ya kalle ta ya watsar kamar bai ganta ba, ya mi a mata hannu alamun ta bashi arsa. Ba musu ta bashi Musliha, sai ya yi murmushi yana kallonta domin kuwa Allah ya zuba baiwar kyau a fuskar Musliha. Nayla ta ce, "Ina kwana." Kallonta ya yi ya auke kai a da ile ya ce, "Lafiya." Daga nan ya yi shiru bai ce komai ba. Nayla ta ce, "YaMar har yanzu fushi ka ke yi?." Bai kula ta ba ya gama abinda yake yi, ya sumbaci goshin Musliha ya mi e tsaye ya zo inda take ya ajjiye mata ita a jikita, ya kalle ta suka ha a ido na wani lokaci kafin ya janye idonsa ya auki key na mota ya sauka daga saman. Ajiyar zuciya ta yi tana binsa da kallo ta ce, "na shiga uku kuma fa ai, shi bai san ayi abu ya wuce ba, yayi ta fushi kenan kamar tsohon arne. Zai yi ya gama ya dawo ya same ni." Tashi ta yi ta shiga nata falon dan bata san abinda zata yi masa ba kuma. Omar ko da yaje a ha en sabo office insa na kar ar manyan ba i ya zauna, office in yana da girma sosai, auke da kujeru set aya masu kyau da kuma kujeru na zaman office. Da awards da ya samu a jere akan wani dogon table, ga hotonsa da manyan mutanen nigeria da wajenta. Babu abinda babu a office in, tv, dispenser, fridge, kettle ta dafa tea, microwive da komai na amfani akwai. Buga ofar aka yi ya ce a shigo, aka shigo da sallama ya kalli yaronsa alamun arin bayani ya ce, "Boss akwai wani babban mutum da ya zo nemanka." Omar ya an yi jim kafin ya ce, "Waye?." "Kamar an siyasa ne." "Ya jira ni ina zuwa, ina wani aiki yanzu." Yarom ya amsa ya fita. Ya samu Sen a zaune ya ce, "Boss ya ce ka jira shi yana zuwa." Da mamaki yake kallon yaron ya ce, "ka fa a waye ya zo nemansa?." "na sanka ne da zan fa a masa waye?." "Ka koma ka ce masa Sen Sagir ne yazo." "Umarninsa nake bi ba naka ba, in kai shugaban asa ne ba sanata ba abinda yace shi zan yi" ya fa a yana wucewa ya bashi waje. Sen cike da unar rai ya bi yaron da kallo, sai yanzu yake dana sanin rashin tahowa da escort, da tare suke dasu babu abinda zai hana bai saka an yiwa yaron dukan tsiya ba. Sen ya gama zuwa wuya, sama da mintina talatin yana jiran Omar bai ce ya shigo ba. Sai wuci yake shi ka ai yana wafa, Allah ya taimaka wajan ba public waje bane da ya shiga uku da jin kunya. Narma ka ai yake hange a idanunsa, in ba dan haka ba da yanzu ya saka an tashi wajan, amma ita yake tunawa shiyasa yake yin sanyi. Bashir ne ya zo wucewa ya ga babban mutum kamar Sen yana jiran Boss insu. Ya bishi da kallon mamaki, bai yi magana ba ya shiga wajan Omar. A tsaye ya samu Omar yana aukar wayarsa da key da alama fita zai yi. Bash ya ce, "Tiger kana da ba o a waje." Omar ya an dafe kai ya ce, "na manta, ka ce ya shigo" sai ya kalli agogo ya ce, "duk da dai sauri nake yi." Bashir bai fa a masa waye ba ya auki abinda ya kawo shi wajan Omar in ya fita. P099 Da sallama aka shigo ya ago tare da amsawa idanunsa suka ha u da na Sen Sagir. Omar ya gyara zama yana kallonsa da matu ar mamaki amma bai ce komai ba, ya araso ya zauna yana kallon Omar kamar yadda yake kallonsa, Hannu ya mi awa Omar alamunsu gaisa, ba musu Omar ya bashi hannu suka gaisa. Yangance Sen ya ce, "Ya aiki? Ka barni ina jira for more than 40mints." Omar ya ce, "Alhamdu lillah.... Ban san da zuwan ka ba, so dole zaka jira na gama abinda nake yi." Sen ya yi ajiyar zuciya, bai bari maganar ta yi tasiri a ransa ba, Narma ka ai yake gani hakan ya saka ya ce, "Tiger nazo tun daga Abuja kawai saboda na ganka." Omar ya an ta e baki ya ce, "za e ya kusa ko? Kamar saura an kwanaki ka an na ji ana cewa ko?." Sen ya kalli Omar suka ha a ido sai Omar ya ce, "Yanzu ba wancan tiger in da ka sani ba bane, wannan Tigers Footwear ne. In ma kana neman wanda zasu yi maka aiki kamar yadda ka saba zaka iya zuwa bakin titi suna nan suna zaman jiran zuwanka, in maganar da ta kawo ka kenan ina da ba in da zan yi" Omar ya fa a yana cigaba da duba abinda yake gabansa. Sen ya daure ya ce, "Ba wannan maganar ce ta kawo ni ba." "Ina jinka, but don't waste my time, ina da ba i suna jirana." "Omar na zo ne akan batun Narma." Da sauri Omar ya kalle shi kana ya ce, "Driver take nema ne?." Sen ya kalli Omar jin ba ar magana yake fa a masa a fakaice, amma saboda Narma da halin da take ciki sai ya kawar da maganar Omar ya ce, "Omar wannan ya wuce ya kamata ka manta komai ya wuce. Narma ta shiga damuwa a kanka, tana matu ar sonka, in ta rasa ka zata shiga damuwa sosai. Please Omar ka amince ka kar i auren Narma, this the first time da nake ro on wani a rayuwata, i beg you for that, ka amince ka auri Narma in ba haka ba zata iya samun matsala." Omar ya zuba masa ido yana kallonsa cikin mamaki da al'ajabi, wato yanzu ya zama