Sashe 46
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
us, ya zuba mata ido kawai yana kallo bai kar a ba kuma bai yi magana ba. Numfashi ya sauke ya mi a hannu ya ya kar i key in, sai tayi murmushi tana goge hawaye ta ce, "na gode." Yana fita ta biyo shi ya kira Tk da yake ofar gidan ya saka ya bu e masa gate in gidan. Kallon motar yake yi shi bai shiga ba kuma bai koma ciki ba, ga kuma gate in an bu e, juyawa yayi ya kalle ta ya ga itama shi take kallo sai ya auke kai yana ji ko dai ya bawa Tk ya kaita ne?. Ji ya yi bazai iya yin hakan ba ya danna remote in jikin key in motar, ta bada sautin bu ewa ya shiga mazaunin driver. Tana tsaye ya fita da motar Tk ya kulle gate in, ita kuma ta fito ko rufe ofar gidan bata yi ba kawai jan ofar ta yi dan ta san key in gate in yana jikin makullin motar. Har tuntu e take yi wajan shiga motar saboda sauri, ta zauna a mazaunin gaba a arare cikin bugawar zuciya. Motar ya ja suka tafi, ta kalle shi ta gefen ido ta ga glass in gabansa kawai ya ke gani ba ita ba. Nayla tayi murmushi cikin jin da i ta ce, "Asibitin getting better zamu je, a nan cikin nasarawa gra." Tafiya suke yi kawai bai ce komai ba ita kuma sai satar kallonsa take yi zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Ba su ta a zama na wani lokacin tare dashi haka ba, dan zaman da suke yi ka an bashi da tsaho shiyasa take jin tafiyar motar tayi mata da i sosai. Har suka je asibitin babu wanda ya yi magana, suka shiga gate in asibitin ya ajjiye motar ba tare da ya ce komai ba. Kallon sa ta yi ta ce, "zan shiga ciki?" ta fa a a sanyaye duk da ta san amsarta. Bai amsa ba kuma bai motsa ba yana kallon gabansa, sai daga baya ya ce, "ba driver ki ka ajjiye ba, ki san zaman da zaki yi." Nayla ta ce, "to" ta fa a tana bu e motar ta fita zuwa ciki tana kiran wayar mijin Jidda. Da shi suka ha u ya rakata akin da Jidda take tana shiga ta arasa inda Babyn ta ke tana kallo ta ce, "Ma sha Allah! Wannan Babyn kamar na auke ta twiny." Jidda da take zaune ta yi murmushi ta ce, "ta baby kike yi ba tani ba ko?." Nayla da take yiwa Babyn hoto ta ce, "ni na isa? Jira na gama yi mata hoto na yi posting tukunna." Hoton ta tsaya kalla bayan ta gama ta tabbatar da ya yi kyau sannan ta tura family group insu sannan ta saka a status. Kafin ta gama orawa a status Abiy ya yi reply a group in da Allah ya rayata bisa sunna. Murmushi tayi ta ce, "kinga har Abiy ya yi reply." Jidda ta ce, " araso na ji uminki ar uwa, Wallahi na auka she awa zanyi saboda azabar haihuwa." Nayla ta arasa inda take ta ri e hannunta ta ce, "Sannu Twiny, amma kin samu lafiya ko?." "Tun magriba fa na haihu, bai miki waya ba sai bayan na farka daga bacci." Nayla ta ce, "Allah sarki Twiny, sannu kin ji." Jidda tayi dariya ka an ta ce, "wai an yi min inki, ko dariya na yi sai naji a jikina." "Sannu my love, wallahi tausayi ki ke bani." Jidda ta sake yin murmushi ta ce, "Ke ka ai ki ka zo a daren nan? Sai da na ce masa kar ya fa a miki na san zaki ce zaki zo ga dare yayi, shine ya ce ai in bai fa a miki ba ya ci amanarki." Nayla ta yi murmushi ta ce, "wallahi kuwa ya ci amanata. Ba ni ka ai na zo ba ai." "Drivern Hajja?." "A'a." "Waye ya kawo ki to?." "YaMar mana." Jidda ta wara ido ta ce, "Mijinki wai?." Nayla tayi murmushi tana sake ri e hannun Jidda ta ce, "shi mana." Jidda ta ce, "yaushe aka fara shiri haka babu labari? Nayla kina so ki ce komai normal yanzu?." Nayla ta girgiza kai a sanyaye ta ce, "kawai dai ya ga dare ya yi ne shiyasa ya kawo ni." Jidda ta dafa ta ta ce, "tabbacin komai ya fara zama normal in kenan, in ba dan haka ba Ina ruwansa dake ma?." Nayla tayi murmushi ta ce, "ba a gane kan shi ne gaba aya Twiny, yau fari gobe ba i, yau kirki gobe masifa." "Na fa a miki hanyar da zaki kamo shi ko baya so amma kin i ji, wallahi da yanzu abubuwa sun fara daidaita." "Twiny a haka ma alhamdu lillah, tunda har yana saurarena nayi magana ya bani amsa, in bani da lafiya ya tambayi lafiyata, ko hana ni fitowar nan yayi ya ce dare yayi yanzu kulawa ce mai girma wacce na ke girmamata a zuciyata. A hankali komai zai daidaita, amma ni bazan iya jawo hankalinsa da jikina ba Twiny, saboda zan ga kamar ba ni in yake so ba jikina yake so." "Waye ya fa a miki? Kawai zai fi saurin bayyana abinda yake zuciyarsa ne ta hanyar hakan. Wannan turaren da na baki da kina amfani dashi kina saka kaya masu aukar hankali, yadda ki ke da structure mai kyau da yanzu an wuce wajan." Nayla ta ce, "Twiny soyayyarsa nake bu ata ba s*x love ba, wannan dabarar ta ki kusancin kawai zata kai ga jikin mu ba da zuciyarsa ba.Wallahi Twiny ji nake yi a zuciyata indai zai so ni ya zauna dani da zuciya aya, ya bani kula da soyayyar zahiri ko kusancin mu bai ga ha a shinfida ba am okay. Allah ka ai ya san irin son da nake yi masa, Ina ari wajen oyewa ne saboda hakan ya zamar min dole amma Ina mugun aunarsa" ta fada hawaye na sakko mata, ta mi e tsaye ta auki Babyn Jidda ta ri e a hannunta. Jidda ta ri e hannunta cikin tausayawa ta ce, "komai zai are in sha Allah, zai furta miki kalmar so ina jin hakan a jikina. Lokacin da na fara labour na san na yi miki addu'a, amma da ta tankama ban sani ba ko na yi miki in ko banyi ban sani ba." Nayla ta ce, "a hakan ma alhamdulillah, shiryawa ta da Abiy kawai nake so Twiny, wai ni Naylan Abiy nice na kwashe sama da wata hu u ban ga Abiy ba, Ina azabtuwa da hakan sosai." "Ki yi ha uri, har yanzu bamu san me ya ata masa rai ba, amma komai duk zai wuce." Ajiyar zuciya tayi ta goge idanunta tana yiwa Babyn wasa da kumatu. A lokacin mijin Jidda ya shigo yana ta tsokanar Nayla tana mayar masa dan sun saba tun kafin auren hira suke yi dashi sosai. Nayla ta bashi Babyn ta ce, "Twiny zan koma, amma gobe na san kina gida ko?." Kai ta aga mata Nayla ta ce, "bara na je, zan shigo goben tun safe in sha Allah. Na san tare zamu shigo da Salma." Jidda ta amsa suka yi sallama ta fita da sauri tana fargabar ha uwa da Omar dan ita kanta ta san ta jima sosai. KRB3P024 Arewabooks@nanahaleema11. Omar yana zaune yana duba agogo yana mamakin zaman da tayi ta bar shi a mota kamar wani yaronta. Wayar da Bashir ya yi masa ce ta auke masa hankali suka jima suna waya akan abinda ya shafi kasuwancinsa yana basa umarnin abinda ya kamata da abinda ya kamata a bari. Yana wayar yana kallon agogon motar yana girgiza kai cike da zallan takaici. Haushin kansa ma yake ji da har ya kar i motarta ya kawo ta, to daman ba dole ma ta shanya shi ba tana ganin motarta ce kamar driverta yake a wajanta. Yanke wayar ya yi ya sake kalla ya ga mintina kusan arba'in kenan da shigarta. Murmushin takaici ya yi a bayyane ya ce, "Ni Omar aka bari jira a mota" ya fa a yan girgiza kai cikin tsananin acin rai. To ko Narma da mahaifinta ya biya shi yana kai arsa unguwa bai ta a zaman jiranta na tsahon wannan lokaci ba sai ita. Tunda ya hango ta fito ya tsaya yana jiran arasowa ta, yana gani tana sauri har ta araso yana jira ta shigo ya sauke mata kwandon masifar da take nu usar zuciyarsa, dan bai ga abinda zai dakatar dashi wajan nuna mata kuskurenta ba. Tana bu e motar ko arasa shiga bata yi ba ya fara cewa, "Ga banza an aikinki wanda ki ka raina, kin shiga sama da mintina arba'in kin bar ni zaune ina jiranki saboda ga yaronki. Biyana ki ke yi ko kuma a ashinki nake aiki? Ko dan motarki ce na taimaka na kawo ki sai ki ka saka a ranki ni driver ki ne!?." Jin yadda yake magana da fa a sosai jikin Nayla yayi sanyi kafin ta yi magana ya sake cewa, "Dan kin raina min hankali kin kuma raina ni ni zaki bari Ina jira har wannan lokaci? Saboda ga wanda ki ka ajjiye kina biyansa dole ya yi miki abinda ki ke so ko?." Nayla ido ya ciko da hawaye a sanyaye ta ce, "Don Allah ka yi ha uri, saboda kai nake ta sauri na fito nazo mu koma, babu kowa a tare da ita haka na barta. Ka yi ha uri YaMar, duk abinda ka ce ba haka bane, ni ban raina ka ba, ka yi ha uri don Allah" ta fa a a sanyaye hawaye na sakkowa daga idanunta cikin tsananin rauni. if ya yi kamar an tsayar da fa an na sa, ya zuba mata ido ganin yadda hawaye yake sauka aya yana bin aya, sai ya ji gaba aya fusatar da yake tare da ita tana gushewa a hankali. Yanayin da ta yi masa magana ya kashe masa jiki sosai, duk karsashin fa an da yake ji dashi duk ya gudu sai rauni da ya mamaye masa jiki, ya kafa mata ido kawai yana kallon yadda take kuka da alama akwai abinda yake zuciyarta. Kukan