Sashe 74
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amma bai san me zai yi ba, bai san me zai fara yi wanda zai saka ta gamsu a zuciyarta yana aunarta ba. Yana ta tunani shi ka ai cikin kewa da tsananin aunarta, bai san me zai ce ba, bai san abinda zai yi ba. Nayla ma a angaren ta haka take, amma ita farin cikin bayyana mata yana sonta yafi mata da i har ta kwanta ita ka ai tana murmushi. Da asuba bata tashi ba kasancewar ba sallar zata yi ba, sai arfe bakwai da rabi ta farka saboda alarm in da ta saka. Wanka tayi kana ta fito ta shirya breakfast mai sau i sannan ta shiga ta shirya cikin tsadaddiyar atamfa irin inkin da ta saba, ta fito falon a lokacin yake fitowa cikin jallabiyya. Kallonsa tayi suka ha a ido, an tsayar da idonta tayi a cikin nasa na wasu sacanni kafin ta janye ido ta ce, "ina kwana." Murmushi yake yi yana jin muryarta har tsakiyar kansa kafin ya ce, "Kin tashi lafiya?." "Lafiya lau, ga breakfast na gama, na ji kace zamu fita da wuri." Kai ya aga mata ya ce, "da wuri zamu fita, amma abincin nan..." katse shi ta yi ta ce, "don Allah YaMar!." Zuba mata idanu ya yi na wani lokacin, kafin ya tafi da idanun kamar zai rufe sai ya fasa ya bu e akan fuskarta. Nayla ta ce, "gashi anan." Omar ya biyo bayanta ya zauna ta ha a masa tea daidai da ra'ayinsa. Babu yadda zai yi mata dole ya kar a, ji yake in bai kar a bazata ji da i ba shi kuma ba ya son aikata abinda zai saka ta ji babu da i a zuciyarta. Nayla ta zauna ta kafe shi da idanu, dole ya sha tea in tana zuba masa sauran kayan ya ce, "ki bar shi ya isa." Nayla ta kalle shi kamar zata yi kuka ba tare da ta yi magana ba, hakan da ta yi bai san lokacin da ya ce, "to zan ci." Sai da ya furta maganar sannan ya san ya yi, Nayla ta yi murmushi ya kar a ya an ci ka an ya kalle ta ya ce, "na gode" ya fa a yana tashi ya shiga aki. Murmushi ta yi tana na zaune itama ta ci abincin tana jiran fitowarsa. Ba jimawa ta ji ya bu ofa ta juya tana kallonsa. Sak ta yi tana binsa da kallo ganin kwalliyar da ya yi bata ta a ganin yayi irinta ba. Men lace ya saka black colour, ya saka hula da takalmin da suka haska afarsa. Ga agogon da ya aura a tsintsiyar hannunsa, ga azurfar da ta bashi tsaraba a hannunsa. Babban abinda ya fi tafiya da ita kamar babbar rigar da ta ga ya saka, bata ta a ganinsa da babbar riga ba sai yanzu, ko da bikin Didi bai saka babbar riga ba amma yau gashi ya saka, shiyasa ta tsaya cak tana kallonsa kamar ta sace shi ta gudu. Ganin yana tahowa inda take ya saka ta auke kai daga kallonsa ya ce, "mu je?." Nayla ta aga kai ta koma ciki ta auko mayafinta da jaka da wayar ta. Kafin ta fito har ya fita da motarsa, ta bishi da kallon mamaki tana tabbatarwa kenan itace motar da Didi take bata labarin ya siya. Da Tk suka gaisa ya kulle gidan, ta arasa ta bu e gaban motar ta shiga ya yi bismillah ya ja motar suka fita. Kallon ta ya yi yaga tana ta murmushi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Nayla ta ce, "motar da ka siya ce?." Kai ya aga ya ce, "uhum, lokacin bakya nan." Wayarsa ce tayi ara ya kalla ya ga Didi ce sai bai auka ba ya cigaba da tafiya. Sake kira ta yi ya an kalli Nayla ya ce, " auki wayar." Hannu ta saka ta auki wayar ta saka a speaker Didi ta ce, "Omar ka tafi ne?." Omar ya ce, "uhum. Ina Marmerh?." Didi ta ce, "yanzu baka tambayar ya na tashi kawai Mamerh ka ke nema." Murmushi ya an yi bai ce komai ba, zata yi magana ya ce, "zan kira ki." Jin hakan sai Nayla ta yanke wayar tana kallon screen in wayar. Hoton Marmerh ne wanda ya yi matu ar kyau tana bacci cikin shiga ta alfarma. Kallon sa ta yi kafin ta ajjiye wayar shi dai bai ce mata komai ba. Tafiya suke yi Nayla ta ga tafiyar ta arewa ta ce, "Ina zamu je haka?." Omar ya kalle ta ka an ya auke kai ya ce, "Ki yi bacci ki tashi." Nayla ta ce, "Ina zamu je to?." "Siyar da ke" ya bata amsa a ta aice ba tare da ya kalle ta ba. an murmushi ta yi shi ya ce, "da gaske nake." Nayla dai bata ce komai ba, ta an gyara zama dan zaman ya fara damunta ga pad in jikinta yanzu sai ta fara damunta. Shiru tayi tana kallon titi kamar yadda yake kallo shiru motar babu wanda yake magana. Wayar Nayla ce ta katse shirun ta duba ta ga number ce wacce bata sani ba, sai ta share bata auka ba. Aka sake kira sai ta auka ta saka a kunne ta ce, "Hello." Shiru tayi alamun ana magana kafin ta ce, "Oh na gane, Ya aiki?." Shiru ta sake yi kafin ta ce, "Sai zuwa upper week zan dawo." Ta sake cewa, "Allah sarki na gode da kulawa." Tana fa ar hakan ta yanke wayar ta ajjiye a jikinta. Omar yana jin duk abinda ake fada har shi mai maganar yana jiyo me yake cewa, bai yi niyar magana ba ya ji ta ce, "abokin aikina ne." In ya tanka kujerar da suke kai ma ta tanka. Abokin aikinta ne da tambayar meyasa bata zo aiki ba? Ina ruwan shi da matarsa?, ita kuma har cewa take yi ta gode da kulawa, mutum nawa ne suke yi mata irin wannan kiran?. Nan da nan fuskarsa ta juya ta koma ta asalin Omar tiger da ta sani, bata lura da hakan ba sai da ta an kalle shi ta ga ya ha e fuska sosai. "Me ya ce miki?." Nayla ta tsorata dan wallahi bata auka zai yi magana ba, ga yanayin fuskarsa duk ta canja mata sai ta ce, "kwana biyu bai ganni a wajan aiki ba shine yake tambayar lafiya." Ya girgiza kai kamar ba zai ce komai ba suka cigaba da tafiya. Har ta cire kai da zai sake magana sai ta ji ya ce, "ya ji lafiya ki ke yanzu?." Nayla ta ce, "eh." "Ya yi." Daga haka bai sake cewa komai ba bai kuma saki fuska ba bai kuma kalle ta ba. Nayla ta ce, "i'm sorry." Bai ce komai ba sai ta yi shiru tana mamakin wai ina zasu je ne haka kusan awa aya ana tafiya. Nayla tun tana saka ran zai yi magana har ta cire dan bai ce mata ala ba. A Zaria ta gansu, abin ya bata mamaki sosai tana tunanin to ina zasu je haka?. Bata gama mamaki ba sai da taga sun shiga Kaduna kuma kai tsaye unguwar su Naylan ya nufa kamar yadda suka zo kwanaki. Idanu Nayla ta wara lokacin da ta ga sun shiga estate in gidan su ya kuma tsayar da motar a daidai gate in gidan. Nayla ta kalle shi murya na rawa ta ce, "me...zamu....yi....a...nan?." Bai kula ba, ta ga an bu e gate ba tare da ya yi horn ba ya shiga da motar. Nayla ta firgice tana kallonsa ta ce, "me muka zo yi nan? Abiy.......!." Hannunsa ya ora akan nata ya an matsa hannunta ka an ta kalli idanunsa ya ce, "ki nutsu, Ina tare da ke." Nayla ta ce, "meyasa baka fa a min nan zamu zo ba? Abiy fa ya ce....." Omar ya katse ta ya ce, "shiii na sani, kar ki damu." Nayla ta fara hawaye ta ce, "ni dai mu koma Kano don Allah, bana son atawa Abiy rai." Hannunta ya sake matsawa ka an ya ce, "Ina tare da ke, ki bar wannan kukan shagwa ar, Mu je" ya fa a yana bu e motar ya fito amma Nayla ta kasa fitowa. Zagayowa ya yi ya bu e mata yana kallonta dole ta fito a sanyaye tana kallon cikin gidan na su cike da kewa. KRB3P041 Nayla tana tsaye a jikin motar hawaye yana zubowa daga idanunta tana kallon gate na biyu wanda zai kaita cikin gidan. "Nayla!." Taji an fa a daga bayanta, da sauri ta juyo ta ga Ya J kawai sai ta fashe da kuka mai sauti. Da sauri ya araso inda take ta fa a jikinsa ta rungume shi tana kuka sosai. Jawad ya ce, "ke kin ga matsalata da ke wallahi, yanzu meye na kukan?." Ya kalli Omar da yake tsaye ya ce, "Omar haka ka ke fama da Nayla da shagwa at nan?." Fuskarsa babu walwala sosai amma a sake fuskar take bai ce komai ba. Jawad ya cire ta daga jikinsa ya ce, "ki bar kuka, tun azu nake jiran zuwan ku. Mu je ciki." Nayla ta ce, "Yaya J, Abiy." Ya ce, "Abiy yana nan, yau ko fita bai yi ba saboda zaku zo. Ki bar wannan kukan malama ki wuce mu je ciki, kin bar shi a tsaye bayan kun yi doguwar tafiya." "Hajiya Nayla barka da zuwa." Aka fa a daga bayanta, ta juya ta ga ma'aikatan gidan ne sai ta yi murmushi suka gaisa. Jawad wajan Omar ya koma suka gaisa da fara'a kamar sun saba da juna sannan ya yi masa iso zuwa ciki, ya kalli Nayla ya ce, "in kin ga dama ki ta zama." A hankali ta biyo bayansu kamar ba uwa a gidan. Gidan yana nan yadda yake sai dai a sake yi masa fenti ya sake fitowa kamar sabo. Apartment in Jawad ta ga ya bu e sun shiga da Omar, ta bi bayan su a hankali ta shiga itama. Sanyin ac ya ratsa ta an gyara shi sai hamshi yake yi, sannan ga abinci a tray babba an ajjiye da alama dai an shiryawa zuwan na su. Jawad ya kalli Omar ya ce, "Ku huta