Sashe 151
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wancan Omar in da wanann ta ce, " warai shine. Tiger da ka sani a baya kenan, yanzu kuma C.E.O Exclusive Footwears by Tiger ne a gabanka. Dole ka yi mamaki gaskiya, wancan Tiger in daban, wannan daban. Ba ka auka rayuwarsa zata zo wannan matakin ba ko?." Sen ya bi Omar da kallon mamaki da firgici ya ce, "wait..wai kina nufin shine wanda aka yi signing contract dashi da asar China? Sannan kina so ki ce shine wanda na ga hotonsa da president?." "Shine Senator Sagir Sani, ai ba a mamaki da ikon Allah. Wanda ake ganin ba komai bane sai ya zo ya zama komai a lokacin da baka yi zato ba balle tsammani. Baka yankewa mutum hukunci tunda ba kai ka halicce shi ba." Ta kalli Narma da take kallon Omar ko ifta ido bata yi, ta an yi murmushi ka an ta ce, "Narma meet his lovely wife, Nayla.!" Ta fa a tana nuna mata Nayla da take kallonta. Gaban Narma ya yanke ya fa i, ta auke ido daga kan Omar ta ora a kan Nayla da ta ago ido tana kallon ta. Narma sai ta an ru e ta auke ido daga kan Nayla kafin ta sake kallon ta, bata ta a ganin macen da kallon ta kawai ya saka mata fa uwar gaban ba sai Nayla, bata ta a ganin macen da kyaunta ya burge ta a kallo aya ba kamar Nayla ba. Abin mamaki sai ta ga Nayla ta yi murmushi ta mi a mata hannu alamun su gaisa. Narma ta bata hannu a sanyaye suka gaisa ta ce, "nice to meet you." Nayla ta ce, "likewise." Daga nan ta zare hannunta bata sake kallon ta ba. Narma ta auke kai daga kallon Nayla dan bata damu da ita ba ta ce, "Omar don Allah ka ago ka yi min magana ko sau aya ne, meyasa ka ce min ba kai bane ranar da na ganka a aiport in nan?." A hankali ya ago ya kalle ta sai ya kalli Sen da yake ta kallonsa shima mamaki kwance a fuskarsa. Kafin Omar ya yi magana Sen ya ce, "Nice to meet you Mr Omar. If possible i'd like to discuss something important with you." Omar ya kalle shi yana aga gira fuskarsa a aure, kamar zai yi magana sai ya fasa ya mayar da kai yana danna waya tare da murza hannun Nayla. Sen ya zuba masa ido yana jiran amsa amma Omar yayi biris kamar ba dashi ake magana ba. Didi ta zira hannunta bayansa ta an ta a shi alamun ya bada amsa ya share kamar bai ji ba. Ran Sentor ya aci ganin wula ancin da Omar ya yi masa a gaban mutane. Ya an juya yana kallon wajan yaga ba a kallonsu amma escort insa suna jin abinda yake faruwa. Sen ya girgiza kai cikin unar rai yana arewa Omar kallo da ya har e a waje aya yana danna waya kamar ba shi ba. Sai da ya ga dama sannan ya kalli Sen ya ce, "can I know the details?." Da mamaki Sentor yake kallonsa jin ya mayar masa da amsa da turanci, sannan sai da ya gama ja masa aji sannan ya bashi amsa, amma sai ya danne mamakinsa ya ce, "If possible come and meet me at my house." Omar ya wara idanu yana sake are masa kallon wula anci da rainin hankali ya ce, "I think if you want to talk to me you're the one who should come over to my place right? So if you're ready, try to inform my PA to book an appointment.." Sen kallon Omar kawai yake yi cike da mamaki da al'ajabi jin yana yi masa magana cikin izza, ga turancin da yake yi. Narma ta ri e hannun Dad ta ce, "Dad!" Sai hawaye suka sakko mata ta koma wajan Omar ta ce, "ko a lokacin baya ka san ina sonka ko? Dad shine ya yi komai ba ni ba. Don Allah kar laifinsu Dad ya shafe ni, I'm ready to marry you wallahi. Na kasa nutsuwa, na kasa zama cikin hankalina saboda kai. Over one year kenan ina dakon soyayyarka, please Faruk ka taimake ni" ta fa a tana zubewa a wajan tana ha e hananyenta tana kuka sosai. Mum ce ta araso wajan da ta ga abinda yake faruwa ta ago Narma daga inda take ta ce, "meyasa ki ke haka ne? Meyasa ki ke embracing kanki akan soyayya ne Narma?. Oya jirginmu zai tashi, mu je ko?." Narma tace, "Mum bazan je ko ina ba, kalli Faruk ina, look at him Mum" ta fa a tana nuna mata Omar. ewa tsaye ya yi ya auki Marmerh da take jikin Nayla a zaune, ya ri o hannun Nayla ta tashi tsaye ya kalli Didi ya ce, "Didi mu je ko?." Mum ta bi shi da kallo ta ce, "wannan ba shine mai company Exclusive footwear ba?." "Yes Mum, and shine Faruk ina, ki tambayi Dad shine." Omar ya kalli Didi cikin gajiya da surutansu ya ce, "Didi mu je!" Ya fa a yana yin gaba, haka kawai ranar yaji ya tsani ganinsu gaba aya, tausayin Narma da yaji a kwanaki yanzu gaba aya ya gushe daga zuciyarsa. Wuce su suka yi yana ri e da hannun Nayla ita kuma tana tura jakarsa da tata da ta ha esu waje aya, Didi ma na turata ta. Fuskar Nayla a cushe matu a Didi ma ta kasa magana, bata so ta nuna ta ji tausayin Narma Nayla tayi kishi, in kuma ta ce bata ji tausayinta ba wallahi arya take yi. Ta kuma san halin Omar, indai ba tsananin kiran rabo ba babu dalilin da zai saka ya aga kai ya kalli Narma, ta san in ya wuce ya wuce kenan baya komawa, shiyasa take jin tausayinta dan ta san soyayyarsa bazata yi mata amfani ba. A first class flight suka zauna, kujerar Didi ce a jikin taga, sai ta Marmerh da take kusa da ita, sai Nayla sai kuma shi. Kallon Nayla yake yi yadda ta aure fuska bai ta a ganin ta haka ba, duk sai ya damu saboda ya san ba ita ka ai ba ce akwai babynsa. Har jirgi ya tashi Didi bata san inda suka nufa ba, kuma babu wanda yake magana a cikinsu. Abinci aka kawo ya kalli Nayla ya ce, "baza ki ci ba?." Kai ta girgiza bata ce komai ba. Ya kalli Didi da take mamakin cabin chew in da ta gani larabawa, sannan abincin bai yi kama da wanda aka basu a zuwa Abuja ba. Omar ya ce, "Didi ki ce mata ta ci, bata ci komai ba fa." Didi ta kalli Nayla ta ce, "kici Nayla, duk da ma mun kusa sauka." Nayla ta ce, "bana son ci ne Didi." Ajiyar zuciya Didi tayi bata ce komai ba, ta san kishi Nayla take yi kuma ya kamata daman ta yi. A gaban idanunka ace ana son mijinka ai sai inda arfinka ya are. Ita babban farin cikin ta da Allah bai tashi ha a Omar da Sen ba sai da rayuwarsa ta kai wannan mataki na alfahari, wannan abun ya yi mata da i ta kuma godewa ni'imar Allah. Tana tuna lokacin da suka zo Abuja neman alfarma, ya wula antata yana cewa gwara dabba a kanta. Amma yanzu gashi shine yake son magana da Omar shi kuma yana ja masa aji, Narman da aka wula anta shi ta dalilinta gata nan har yanzu haukan sonsa take yi, in ba Allah ba waye zai yi wannan?. Hannunta ya ri e ya ce, "wai akan abinda ya faru ki ke fushi?." Ta zame hannunta daga cikin nasa ta ce, "Don Allah ka yale ni." "Bazan yaleki ba, meye ya faru da zaki yi fushi ki i cin abinci huh? Kin san abinda yake cikinki yana bu atar cin abincinki." "Hmm, daman tunda aka samu cikin nan ai ba damuwa ka ke da ni na ci ba, ko yaushe saboda abinda yake cikina ka ke cewa ko yaushe. To bazan ci ba, ai na ga a cikina an yake ko? Ka yale ni." Didi ya kalla ta yi masa alama da ya yi shiru, ya an yi tsaki ka an yana kallon Agogo. Didi ta ce, "kai tafiyar nan tayi tsayi, har yanzu ba mu zo ba ne?." Nayla ta kalli Didi ta ce, "Lagos zamu biya." Didi tayi dariya ta ce, "ki ce kawai yawo muka taho, ko babu komai na shiga jirgi." Nayla ta an yi murmushi ta ri e hannun Marmerh da take kusa da ita. Duk yadda ya so Nayla tayi magana ta i, ta kuma i kallonsa dole ya yaleta har tayi bacci. Didi tana kallonsa yadda yake zuba mata idanu, da yadda zai mata kiss a goshi, da yadda zai du a yana matsa mata afa. Ita dai murmushi take yi kawai dan Nayla ta cancanci a yi mata haka. Sai da jirgi ya tsaya sannan Didi ta an yi mi a ta ce, "Tafiyar Lagos kusan awa takwas kamar mun bar Nigeria?." Nayla bata ce komai ba suka fito, Didi na ta kallon wajan suka auki jakarsu da pusher in Marmerh. Nayla ta ware pusher ta ora Marmerh a kai. Didi ta ce, "wai nan Lagos ne? Naga wajan da larabawa sosai." Sign board in da aka rubuta welcome to Madina Nayla ta nuna mata ta ce, "ba Nigeria ba ce Didi, kina asar saudia, a cikin garin Madina!." KRB3P092 Nana haleema. Didi ta kalli Nayla ta sake kallon sign board in ta sake kallon larabawan da suke ta aikin su a wajan. Omar ta kalla ta ga yana murmushi sai ta ce, Omar yau Nayla na zama abokiyar wasan ta. Ya yi murmushi ya ce, Didi ba wasa ba ne, wallahi da gaske a garin Madina ki ke. Jin ya ce wallahi ya saka ta tsaya cak ta zuba masa idanu, ta san halinsa indai ya ce wallahi to wallahi in ce baya rantsuwa akan arya kuma baya yi sai ta kama. Didi ta kalli Nayla ta ce, Wai da gaske?. Nayla ta mi a mata passport in hannunta ta ce, kin gani, daga Abuja mun taso mun sauka a ina