← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 205

Sashe 168

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Kwana biyu. Har aka kwana biyu Narma bata san labarin Omar ya i yarda ba, sai da ta samu lafiya sannan Dad yake sanar mata dan ya rasa me zai ce mata gwara kawai ya fa a mata a huta. Dad ya ce, "Bazan miki arya ba Daughter, Omar ya i amincewa, har wanda yake jin maganarsa na je na samu amma ya ce shi sam baya so. Kuma wanda na samu da maganar ashe in law insa ne." Narma a sanyaye ta kalli Dad ta ce, "Hakan yana nufin bazan zama matarsa ba?." Dad ya ce, "kusan hakan Narma, gwara ki yi ha uri ki bar wannan tunanin ya wuce a rayuwarki. Ki cigaba da addu'a, zaki tafi Saudia ki je can ki zauna kina fa awa Allah damuwar ki." Narma ta yi shiru tana kallon wani waje daban kafin ta mi e ta shiga aki. Ganin bata nuna wani tashin hankali ba sai hankalinsu Mum ya kwanta suke fata da addu'ar Allah ya sa ta bar komai ya wuce su huta da wannan tashin hankali. Safna ta kira a waya kasancewar ta zo Kano itama ta ce ta zo gidansu yanzu ta same ta. Ba jimawa Safna ta shigo akin Narma ta mi e tsaye ta saka mayafi ta ce, "Zo ki raka ni waje." Safna ta ce, "ina?." "Ki zo mu je." Tare suka fito falon Dad ya kalle su ya ce, "ina zaku je?." Narma ta ce, "yanzu zamu dawo Dad, mu je" ta fa a tana yin gaba dole Safna ta bi bayanta ta shiga mota Narma ta shiga gaba suka fita daga gidan. A wannan lokacin Omar yana zaune sanye da kaya track suit kalar purple, Nayla tana zaune a kusa dashi haka Didi ma tana zaune dan ta zo duba shi kwana biyu ya yi rashin lafiya. Marmerh na jikinsa a kwance, Musliha tana hannun Didi tana bacci. Falon yayi shiru babu mai magana dan ya ce kansa ciwo yake baya son hayaniya. Idanunsa a kulle suke kansa ya yi nauyi sosai ya yi shiru kamar babu shi a wajan. Bu e ido ya yi ya kalli Didi kamar zai yi magana sai ya fasa, ta ce, "me zaka ce?." aramin tsaki ya yi kawai bai ce komai ba ya mayar da ido ya rufe. Nayla dai tana gefe tana danna waya hankalinta gabadaya yana ga waya, Umma Saroot tana yi mata bayanin kayan gyaran da ta bayar aka kawo mata irin nasu na mutanen Chad. Didi ta katse shirun ta ce, "Omar zamu je Chad, akwai rasuwar da aka yi a can ya kamata a ce mun je mu ma." Bu e ido ya yi ya kalle ta ya ce, "Ina ne kuma Chad?." asar Chad mana, asalin asarsu Maman mu." Omar ya ta e baki ya ce, "A matsayinki na wa zaki je? Wa ki ka sani, waye ya sanki?. Didi kin cika shishshigi wallahi, ina guje miki shan duka wata ran" ya fa a murya a asa saboda kansa da ya yi nauyi. Didi ta ce, "ai har da kai zamu je ba ni ka ai ba. Kakanin mu duk a can suke, kafin Kakarmu ta bar duniya na ta a ganinta sau biyu da ta zo nigeria, amma kai baka ta a ganinta ba. Akwai danginta a can sosai, ana son a sake arfafa zumunci ne, zamu je a madadin maahifiyarmu." Ya zuba mata ido har ta gama bayanin sannan ya ta e baki ya ce, "Sai kin dawo, amma babu inda Marmerh zata je. Danginki ne ai ba danginta ba." Didi ta ce, "Sai mun dawo dai, ka daina batun Marmerh; har kai da Nayla da Musliha." Kallon baki da hankali ya yi mata, ko damar magana ma bata samu daga gare shi ba balle ya tanka mata, dan a ganinsa maganar bata da amfani. Didi a sanyaye ta ce, "Omar meyasa baza ka bari ya wuce bane? Ina guje maka ganin illar ri o wallahi. Me za a yi maka da zuciyarka zata yi sanyi? Me za a yi maka da zai saka ka manta baya ka fuskanci gaba?." Omar da mamaki ya ce, "ikon Allah, ya ki ke so nayi musu? Goya su zan yi ko me zan yi?. Kin ce bana magana dasu yanzu ina yi, to me zan yi?." "Ka saki jikinka dasu kamar kana tare da Mama, ka saki jikinka dasu Kawu kamar kana tare da Baba. Har Gombe mun je ziyara amma ka i zuwa. Don Allah ka yayyafawa zuciyarka ruwan ara ka ri e danginka, wallahi baka da kamarsu a duniya." Sake ta e baki ya yi, sai kuma ya ha e rai ya ce, "Har yanzu ina kallo wu alancin da suka yi miki a lokacin da muka je gidansu, mu mun je da arfin guiwa muna ji a ranmu mun je dangin mahaifiyarmu, ashe dukkansu taron tsinstiya ne babu shara...."ya sake cewa, "Su kuma tsofaffin munafukan har yanzu akwai shatin dukan da suka yi min a jikina, yadda wannan tabon bai ace daga fatata ba haka na zuciyata ma bazai ace ba. Dan ma sun raina min hankali, a rasa yarinyar da za ace ina nema sai wannan ko iyar, na tsani ganin fuskarta wallahi, Tsaf zan talitseta da mota wata ran. Ki basu shawara, duk inda suka san zamu ha u su daina bi wallahi, kamminta suna nan tsaf a idona, in muka gauraya za a yi atacciya." Didi ta yi masa banza bata tanka ba, tana ro on Allah ya kawo ranar da zuciyar Omar zata yi sanyi, tana fa awa Allah ya kawo silar da Omar zai sauka daga wannan dokin zuciyar. Zata so taga ranar da zai yi sanyi ya kar i danginsu. Nayla kam bata ce tak ba kuma tana jinsu. ofar falon aka yi aka shigo da sallama, tunda aka yi haihuwa ba a saka lock ofar saboda masu zuwa barka, kuma gate in gidan ba a hana shiga sosai. A tare suka kalli wanda suka shigo gaba ayansu, gaban Nayla ya yanke ya fa i ta zubawa Narma ido tana kallon ta da tsananin mamaki. P104 Didi mamakin ganin ta take yi, shi kam auke kai ya yi ya mayar da ido ya rufe yana ji kamar ya tashi ya zaneta, sun takura masa ya rasa ya zai yi da su. Narma ganin Didi a zaune sai ta samu arfin guiwa ta araso kusa da Didi ta tsuguna ta ora kanta a cinyar Didi ta fashe da kuka. Dukkansu sun yi shiru babu wanda yake magana, sai kukan da take yi a hankali amma kana jin sautinsa. Omar gajiya ya yi da jin kukan, a fusace ya ce, "Ke!." Ba ita ka ai ba hatta Nayla da Didi sai da suka firgita, Musliha da Marmerh da suke bacci suka bu e ido a firgice. Cak Narma ta tsaya da kukan ta kalle shi ta ga ita yake kallo da alama ita yake yiwa tsawar, ya ce, "Meye na kukan!?." Shiru ta yi ta kalli Didi murya na rawa ta ce, "Didi ki taimaka min, ki taimaka min zan iya rasa hankalina." Didi ta kalli Nayla da take kallonsu ta kalli Omar da ya mayar da ido ya rufe ta sake kallon Narma ta ce, "Narma me ki ke so nayi miki?." Narma tace, "Didi Faruk!." Didi ta kalli Omar ta sake kallon Narma ta ce, "Narma ya kamata ki manta dashi, rayuwar da aka yi a baya baza a yi ta yanzu ba." "Amma Didi kin san ba laifina bane ba ko? Kin san bani da laifi akan abinda ya faru." "Na sani, na san da gaske ki ke sonsa, amma ina so ki san wani abun in ya wuce ya riga da ya wuce kenan har abada. Wata damar tana zuwa sau aya tak a rayuwa, da zarar ta wuce shikenan bazata dawo ba." Safna da take tsaye a sanyaye ta ce, "Didi ki taimakawa awata ki saka baki Omar ya amince da ita, wallahi har a asibiti ta kwanta saboda soyayyarsa. Yau ne kawai ta samu lafiya ta zo inda yake." Didi ta kalli Safna ta ce, "wanne irin taimako zan yi mata? Ga Omar a zaune ai, ni babu ruwana a cikin wannan maganar." Safna cikin dauriya ta kalli Omar ta ce, "Don Allah Omar ka amince da ita, wallahi tana tsananin sonka, ban ta a ganin Narma cikin rauni ba sai bayan ta fara sonka. Wallahi in ta rasa ka zata iya shiga wani hali, dan zuciyarta tayi rauni akan soyayyarka." Safna ta kalli Nayla da take kallonsu ta ce, "Ki yi ha uri Madam, mun rasa mafita ne, shiyasa mu ka zo gidanki ba tare da izini ba." Nayla bata ce komai ba Narma kawai take kallo, tabbas Narma ta canja itama ta gani, duk ta yi wani iri kamar ba ita ba, gayun nan da take ji dashi yanzu duk babu. Didi ta ce, "Omar ka yi magana." Bai bu e ido ba ya ce, "Me zan ce? Mahaifinta ya same ni na fa a masa bana ra'ayi, duk da haka bai ha ura ba ya sanar da Abiy, shima ya kira ni na ce bana ra'ayi" ya bu e idanunsa ya kalli Didi ya ce, "yanzu kuma an kawo maganar wajanki, to me ake so nayi?." Narma cikin rauni da sanyi ta ce, "Ina so na ji daga bakinka ne, dan na san baza ka guje ni ba." Ya tashi zaune sosai ya gyara Marmerh da take jikinsa, ya kalli Nayla ya ga ta zuba masa ido tana kallo, ya auke kai ya kalli Narma ya ce, "Gaskiya ki ke so na fa a miki?." aga kai alamun eh, ya an cize baki kana ya ce, "Ni Omar bani da ra'ayin ara aure a rayuwata, in ma ina da ra'ayi bakya cikin matan da zan iya aura. Ban so ki ba kuma bana sonki, kin shiga rayuwata ne saboda haka Allah ya ulla, tunda ki ka fita kuma komai ya are...." Ya nuna ta da yatsa ya ce, "Yadda nake rayuwata kema ki je ki yi taki, ki daina bibiyata, ki daina zuwa inda nake!" Ya fa a yana kallon ta. Didi ta kalle shi jin kalaman sun yiwa Narma tsauri, a cikin wannan
Chapter 168 · 0% Book details