Sashe 11
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi, wata rana na tabbatar zai amsa miki. Sai kin yi ha uri kin jure kin kawar da komai daga zuciyarki sannan zaki ji da in zaman auren. Nayla ta amsa Hajja ta cigaba da yi mata nasiha kafin ta bawa Salma wayar. Nayla ta ce, Salma zaki shigo?. Bazan so ba gaskiya Nayla, sai an kwana biyu. Shikenan. Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar. Wayar Mama ce ta shigo ta auka ta saka a kunne suka gaisa da Mama kafin Nayla ta ce, Mama Ina Abiyna?. Mama ta ce, Abiy yana Lafiya lau. Na kira shi azu bai auka ba. Wata ila lokacin bai tashi ba. Nayla ta girgiza kai ta yi shiru Mama ta ce, Komai dai lafiya ko Nayla? Ina nan sai tunanin ki nake yi. Nayla ta ce, Lafiya lau Mama. Kin tabbata lafiya?. Mijin na ki yazo?. Eh yazo Mama. Har na ji da i, Ina fatan dai komai Lafiya?. Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, lafiya lau Mama. To haka nake so, In akwai wani abun ki kira ni ki sanar dani. Nayla ta ce, To.. Daga nan suka yi sallama ta kashe wayar ta ajjiye wayar a gefe ta dafe kanta. Bata san adadin lokacin da ta auka a haka ba, sai kuma ta ago ta sake kiran Abiy a lokacin ya auka cikin hanzari ta ce, Abiyna, abiyana ina kwana. Abiy jin yadda muryar ta take rawa ssi ya tausasa murya ya ce, nutsu Nayla, nutsu ki yi magana. Sai kawai ta fashe masa da kuka ya ce, zan kashe wayata in kuka zaki yi min. Ta yi sauri ta share ta ce, na daina Abiy. Ina kwana. Lafiya lau, kin tashi lafiya?. Lafiya lau Abiyna. Ya gida?. Komai Lafiya lau ya bata amsa yana jira ya ji me zata ce. Nayla ta ce, Abiy ka daina fushi dani?. Abiy ya ce, ni ba fushi nake yi dake ba ai Nayla. Zata sake magana ya ce, Ina da ba i Nayla, zan kira ki in na samu space yana fa a ya kashe wayar. Ajiyar zuciya tayi ko babu komai taji da i tayi waya da mahaifinta. Haka ta yini a gidan nan shiru daga ita sai wayar ta har dare. Bayan ta idar da sallah ta yi wanka ta saka kayan bacci riga da wando dogaye masu laushi ta zauna tana shan tea. Tunawa tayi da ta bar kettle a kunne sai ta mi e da sauri ta nufi hanyar fita da mug in tea in da take sha a hannunta. Karo suka yi da mutum shayin ya zube masa a jiki sannan mug in ya fa i a asa ya tarwatse a kan tiles in wajan. KRB3P006 ArewaBooks@nanahaleema. Cak Omar ya tsaya saboda ruwan zafin da ya ratsa rigarsa ya sauka akan fatar cikinsa, ga karon da suka yi irjinsu ya ha u waje aya, ga ragowar ruwan tea in da ya zube a asa ya ta afarsa. Nayla a gigice ta ja baya sai kuwa santsin tea ya kwashe ta tayi baya zata kifa. Kamar ya yaleta ta fa i sai kuma ya ri o hannunta ya dawo da ita ta tsaya cak tana zare idanu. Hannunsa da ya ri e nata sai da walwarta ta je gutun rabon lokaci, bata auka haka zata ji hannun nasa da laushi haka ba, ta auka zata ji tauri kasancewarsa na tantari wanda kwalliya ma bata dame shi ba balle har ya san abinda zai saka a hannunsa ya yi laushi. Shima sai da yaji wani iri ri e mata hannu da ya yi, hakan ya saka ya saki hannun nata cikin sakanin da sanin da bai wuce biyar ba. Nayla jikinta rawa yake yi ka an ta bu e baki da yar ta ce, ka yi ha uri ban san ka taho ba. Fuskarta yake kallo da idanunta da suke kiftawa gashin idonta na sama da asa kamar munafuka. Shiyasa ki ka ona ni kenan? Ya fa a a an kausashe yana kallonta. Nayla ta girgiza kai ta ce, ban yi ima sane ba, ka yi ha uri don Allah. Bai ce mata komai ba ya wuce ya barta a tsaye a wajan tana raba ido. Nayla ta yi ajiyar zuciya tavce, wai na sha da yar. Da sauri ta kwashe pieces in mug in da ya fashe, ta auko mopper ta goge wajan sannan ta kashe abinda zata kashe a kitchen in ta koma falo tana sauke ajiyar zuciya. Har lokacin zuciyarta bugawa take yi kamar yana gabanta, ita ta rasa meyasa take jin tsoronsa har haka a zuciyarta. In ta ganshi sai ta gigice ta rasa abinda yake mata da i, duk arfin guiwar da take ji da sun ha a ido sai ya kau daga zuciyarta ta fara tunanin Didi bata nan balle ta taimaketa. Bangarensa shima da ya shiga akin tsayawa ya yi yana tuna idanunta da suke kitfawa da yadda idanunta suka yi waje lokacin da ta zuba masa tea in. Ta e baki ya yi ya cire rigar yana kallon fatar cikinsa da wajan da tea in ya zube ya an yi ja. Tsaki ya yi ya ce, ban ta onewa ba ta ona min fata. Kaya ya canja kawai ya zauna a akin ba tare da yana yin komai ba. Yunwa ya ke ji sosai amma bai san abinda ya kamata ace ya ci ba, baya son za ewa da yawa balle ya shiga kitchen ya ce zai yi wani abun, shi da gidan su ya saba kawai, da can ne da ko tea ya dafa ya sha. Tsaki ya yi ya ce, ko meyasa ban je can nayi girki ba oho. Kulle ido ya yi ya bu e yana jin sa wani daban kamar ba shi ba. Fitowa ya yi har lokacin tana zaune jin motsi sai ta kalli wajan a sanyaye ta ce, ga abinci. Ba tare da ya kalle ta ba ya bar wajan ko amsawa ma bai yi ba. Nayla a bayyane ta ce, kema dai Hauwa akwai ki da shishshigi wallahi. Duk sai taji babu da i ta tashi ta bar falon zuwa aki. Shi kam fita ya yi ya kira Bash suka siyo masa fruit suka kawo masa ya zauna ya sha sannan yaji da i. Ya shiga akin yana kwaikwayon muryar Nayla yana cewa, Ga abinci, mtsww shirme ya fa a yana kwnaciya tare da rufe idanunsa. Washe gari ma haka ta kasance bata san ya fita ba, tana so ta shiga akinsa ta gyara amma tana jin tsoronsa hakan ya saka bata ma kalli hanyar akin ba. Bayan sallar azahar tana zaune ya shigo da sallama a ciki, ta amsa bai kalle ta ba ya wuce da kaya a hannunsa. Bai jima ba ya dawo ya zauna kamar bai ganta ba ya fito da kayan da ya zo dasu yana auka hoto da alama akwai wanda zai turawa. Nayla ta ce, sannu da zuwa. ago idanunsa yayi ya kalleta tayi saurin kawar da kai dan bata jure kallon idonsa, idanun nasa akwai girma da kwarjini. Bai amsa ba ta sake cewa, Ga abinci. Ajjiye abinda yake yi yayi ya har e hannayensa a waje aya ya kalle ta ya ce, ke ba a fa a miki bana son shishshigi a lamari na bane? Ina yini, barka da zuwa, ga abinci, na ce miki ina so ne? Ya fa a yana an bu e ido yana kallonta. Nayla jikinta ya yi sanyi ta girgiza kai alamun a a ya ce, to ki tsaya matsayinki, har gobe sunana Tiger ban canja daga yadda nake ba. Ki yi rayuwarki na yi tawa, babu lallai sai kin yi min magana nima babu lallai sai nayi miki. Mu kwana dubu a gidan nan dan baki min magana ba babu abinda zai dame ni, kema ki koyawa kan ki hakan. Kin ji ai ko?. Nayla ta aga kai alamun t eh ya ce, baki da baki?. Murya na rawa ta ce, Ina dashi. Rainin hankali ne ya saka ki ke yi min magana da kai? Ya fa a a an tsawace yana bu e idanunsa. Nayla ta tsorata ta ce, a, na ji, na fahimta. Dakyau ya furta yana auke kansa ya cigaba da abinda yake yi. Gaba aya shi an gama cutarsa, an aura masa yarinya da bai ce yana so ba, yarinyar da Didi tayi masa fa a a gabanta har wani girmansa zata gani. Tsaki ya yi a bayyane hakan ya saka Nayla ta mi e jikinta a sanyaye zata bar wajan ya ce, zauna. A zabure ta zauna ba tare da ta sani ba, dan bata yi tunanin zai yi magana ba ko ka an, ya kalle ta ya ce, na ce babu ruwanki da ni ne ban ce ki tashi ba ai, zaki iya zama na ga parlor naki ne ko?. Nayla kamar zata zubar da hawaye ta ce, nawa ne. Kujerun ma naki ne ko?. Nawa ne ta sake fa a kamar ta yi kuka. Ni ya kamata na baki waje ya fa a yana mi ewa ya fita daga gidan gaba aya. Nayla ta ce, na shiga uku, wannan mutum sam baka gane masa, Allah ka sassauta min abinda nake ji a kansa. Wannan abu ya yi yawa, daga wannan sai wannan. Wayarta ce tayi ara ganin sunan Didi sai ta auka Didi ta ce, Nayla ya ki ke?. Lafiya lau Didi, Ina yini?. a ya naji muryarki na rawa? Omar ya yi miki wani abun ko?. Bai yi min komai ba Didi. Kar ki arin kare shi, na san halinsa wallahi. Nima masifa ya gama yi min na saka an kwaso kayansa an kawo gidan. Ki fa a min abinda ya yi miki. Nayla ta ce, bai yi min komai ba Didi. Didi ta ce, ki yi ha uri Nayla, yana da wahalar sabo amma da kun sana shikenan magana ta are. Zai canja miki zaki ga ya koma miki wani Omar in da ban wanda baki san shi ba, duk da masifa da zafin rai a jininsa yake, amma dariyarsa da hira dashi zai zamar miki ko a yaushe dan na fa a miki yana da hira in kun saba. Ki yi ha uri, da kun saba shikenan komai ya