← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 205

Sashe 35

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ce na ce ya fito ya ci abinci. Nayla ta ce, a Didi, ke dai ki je da kan ki. Didi ta ce, kina matarsa baki je ba sai ni zan je na ce ya zo?. Nayla ta ce, eh gaskiya, ni bazan iya ba. Diid ta ce, to umarni nake baki matsayin yayarki, ki je ki ce masa ya zo ya ci abinci. Nayla kamar zata yi kuka ta ce, Didi ba ya cin abincin gidan nan, in na yi masa tayi wula anta ni yake yi yayi min banza ko kallona ba ya yi, ina jin babu da i shiyasa na daina cewa ga shi. Kuma ni ban ta a shiga akinsa ba wallahi!. Didi jin har tana saurin rantsuwa ya saka ta dariya ta ce, Nima ban ce kina shiga akinsa ba ai Nayla, Amma ki je ki fa a masa ma tabbatar yau bazai wula anta ki ba, Kawai ki je. Nayla tayi rau-rau da ido ta ce, Didi don Allah Didi ta katse ta ce, just go Nayla. Nayla ta an yi shiru tana tunanin ta yadda zata aikata abinda Didi ta ce, ta an sauke numfashi kana ta ce, to bara na auko hijjab. Didi ta dakatar da ita ta ce, hijjab in me zaki saka? Wajan mijinki fa zaki je. Ban saba zama babu hijjab ba, kuma ni ban ta a zuwa wajansa babu hijjab ba gaskiya. Haba Nayla, Ina ganin ki mai wayo, mai ilimi ya zan same ki da haka? Dan zaki je wajan mijinki sai kin saka hijjab?. Wuce ki je ba sai kin auko komai ba, daga baya ma tattauna wannan kato arar ta ki. Nayla ta yi ajiyar zuciya tana kallon Didi kamar ta yi kuka, tare suka fita daga falon, Didi ta nuna mata akim alamun ta je. Nayla bata da za in da ta wuce fara takawa zuwa akin Omar. Didi ta bita da kallo tana murmushi ta ce, in sha Allah kafin kwana biyun nan zan saka ki rage wani abun da ki ke yi Nayla, zan san yadda zan yi kusancin ku ya aru fiye da yanzu. KRB3P017 Arewabook@nanahaleema11. Nayla ayatul kursi kawai take karantawa a zuciyarta kafin ta sauke ajiyar zuciya ta wansa ofar a hankali. Omar yana zaune akan stool na gaban mirror ya ora afa kan aya yana ka awa kamar wani basarake idanunsa a lumshe, shi kansa bazai ce ga abinda yake damunsa ba haka nan yake jinsa uncomfortable. Yana ji ana wasa ofa amma bai motsa ba dan ya san hakan bai ta a faruwa ba tunda ya fara kwana a gidan. Mur a handle in ya ji anyi an bu e kofar tare da jin motsi alamun an shigo. e ido ya yi ya kalli wajan suka ha a ido da ita tana tsaye tana raba idanu. A hankali ta ce, YaMar Didi ta ce ka zo ta fa a murya na cracking sosai alamun tsoro ko tilastawa a yanayinta. Shi kam kallon ta kawai ya tsaya yi, she looks so good in her dress, bazai yi arya ba tayi masa kyau a idon sosai, shiyasa ya tsayar da ido yana kallonta kamar ranar ya fara ganin ta. A hankali ya janye ido ya ce, haka ake shigowa wajan mutane babu sallama? Ya fa a muryarsa a can asa sosai. Nayla ta ce , kayi ha uri, na manta ne?. Na ce kin yi laifi ne?. Nayla ta girgiza ka alamun a a ya ce, to meye na bani ha uri?. Ka yi ha ta sake fa a tana sauke kai asa. A zuciyarsa murmurshi yake yi amma a kan fuskarsa akasin haka ne. aramin tsaki ya yi hakan ya saka ta fita da sauri kamar wacce aka biyo. Didi tana zaune ta ga yadda ta fito ta araso har waige take yi. Didi ta ce, ki nutsu mana Nayla, Omar babu abinda zai miki na cutarwa. Wannan tsoron na sa da ki ke ji nake so ki rage don Allah, in ba haka ba nan gaba zai cutar da ke a zaman auren ku wallahi. Zaki zo kina dana sani dan tun farko kin ora kan ki akan matsanancin tsoronsa, shi kuma a haka zai tashi. Nayla ta girgiza kai ta ce, Didi baki san waye YaMar ba, kallon fuskarsa ma abin tsoro ne. Didi cikin tsokana ta ce, inye ka ji wani suna na masoya, YaMar! An cire harafin farko an yiwa sunan ado sai ya bada wani style mai kyau. Lallai Nayla kina shagwa a Omar. Nayla tayi dariya tana rufe fuska da hannunta kafin ta bu e ta ce, Allah Didi ni ko a gida haka nake, Ko Yaya Jawad bana cewa Yaya Jawad Yaya J nake ce masa. Haka cousins ina duk yanke sunayen su nake yi, hatta Yaya Abbas da Yaya Ab nake ce masa kafin na daina. Tunda ya ce yana sona muka daina mutunci, da muka ha u da azumi ne naga bai nuna min komai ba, mun gaisa kamar yadda muke yi kafin ya ce yana sona. A daidai nan Omar ya fito yana takowa zuwa wajan da Didi take zaune. Ya ji abinda Nayla ta ce a kunnensa amma bai nuna yaji ba yana tunkaro su kamar baya son taka asa. Ganin sa sai Didi ta ce, Dan mutum ya ce yana sonki sai ku daina mutunci?. Ni ki bani labarin samarin ki. Nayla bata san ya fito ba dan bata ji motsin sa ba hakan ya saka ta yin aramar dariya ta ce, Hmm Didi nayi samari kam, wani lokacin har bana son fita saboda da yar na je na dawo ba a yi min magana ba, ni kuma na tsani magana a kan hanya. Wasu ma fa dan son iyawa da za ewa har gida wajan Abiy suke zuwa kai tsaye kafin su same ni, suka saka Abiy ya tayar min da hankali akan maganar aure. Diid ta ce, na san kuma akwai wanda ki ke so a cikin su ko?. Nayla ta kalli Didi sai a lokacin ta ga Omar da yake tsaye ya har e hannayensa a irji ya zuba mata idanunsa masu shegen kaifi yana bin ko wanne lungu na jikinta da kallo. Sai ta an ji tsoro ka an ta yi shiru bata amsawa Didi tambayarta ba. Didi ta kalle shi ta ce, ka zauna mana, ka fito ka hanata cigaba da bani labari. Bai musa ba ya zauna yana kallonta ta gefen idanunsa. Didi ta ce, Ina jin ki, kafin zuwan maganar Omar wa kika yi niyar za a a cikin su?. Nayla ta kasa bata amsa ta yi shiru bata ce komai ba. Didi ta an yi tsaki ta ce, wai dan ya fito sai ki daina bani labari? To Ina ruwan Omar shi? Kawai ki cigaba da fa a min, da wa ki ka za a a matsayin abokin rayuwarki?. Kafin Nayla tayi magana ya ce, Don Allah Didi ya isa haka, in bakya son fitowa ta meyasa ki ka saka aka kira ni? Ya fa a murya a asa yana kallonta. Didi ta ce, zan dawo kan ka ne, yanzu hira mu ke yi ai. Ya ce, A bar hirar, bana son ji. In kuma za a yi a bari na tashi. To ubana, saboda kai kawai sai mu daina hira?. Tsaki tayi ka an ta kalli Nayla ta ce, ina jin ki, waye za inki?. Nayla ta sauke numfashi ba tare da ta kalle shi ba ta ce, daman tun farko bana tunanin zan iya auren Ya Abbas, shi kuma A kausashe Omar ya katse ta ya ce, Na ce a bar hirar! An san hirar da za a yi kenan meye na kira na? Ya fa a yana kallon Didi. Didi ta ta e baki ta ce, to meye ha in ka da hirar mu? Laifi ne dan mun tuna baya?. Harara ya sakar mata ya ce, to na ce a daina!. Didi ta ce, sannu ubana, wannan bada umarni kamar kai ka haife ni?. Kawai dai mun yi shiru da maganar ba dan ka hana ba ta fa a tana harararsa tana murmushi asa- asa. Abin mamaki kamar kishi take gani a tare dashi, tabbas kishi ne, in ba kishi ba meye na damuwa dan suna hirar samarinta bayan ta san halinsa?. Murmushin jin da i tayi, in hakan ya kasance zata fi kowa murna, kuma tunda ta fahimci baya so zata san abinda zata sake yi da zata saka ya magantu. Didi ta ce, abinci na ce ka zo mu ci. Ya kalli warmers in abincin ya kalle ta ya ce, bata fa a miki bana cin abinci ba?. Tofa! yaushe ka daina cin abinci ban sani ba?. Bana cin abincin gidan nan, kema kin sani ai ko?. Yau zaka ci. Wani murmushi ya yi ya kalle ta yana age gira tare da antar da ido ya ce, dole zaki yi min?. Ban kai nayi maka dolen ba Omar?. Ya ora afa kan aya ya ce, kin kai, kawai kin je arshe ne, kin ure ni a yanzu. Dan haka bana tunanin akwai abinda zaki sake yi min dole a kai na amince na kar Didi ta ce, Balle ma ba dole zan yi maka ba Omar, darajar zuwa na gidan nan matsayin ba uwa zaka duba ka daure ka ci. Hausawa sun ce ba on ka annabin ka. an shafa kansa ya yi ya kalle ta ya ce, To bani da ra ayin cin abincin gaskiya. Didi ta ce, ka daure ka yi ra ayi kaji YaMar. Kallon ta ya yi jin sunan da ta fa a, sai ya ji bai ji abinda yake ji a zuciyarsa ba a duk sanda Nayla ta fa i sunan. auke kai ya yi ya ce, Didi bazan ci ba. Didi ta ce, Zaka ci Omar, Abinda ka ke so matarka ta girka maka kuma ka ce baza ka ci ba? Ta fa a tana tashi tana serving insa. Matarka, shine abinda ya maimaita a zuciyarsa ya kai kallonsa ga Nayla da kanta yake asa tana wasa da zoben hannunta kamar bata falon. auke kai ya yi a lokacin Didi ta mi a masa plate in ta ce, Don Allah ka kar a ka ci. Didi ni
Chapter 35 · 0% Book details