Sashe 58
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ki kwana biyu? Me Omar ya yi miki da ki ka koma?. Kar ko oye min komai Nayla, in kuma na zo gidan to." Nayla ta ce, "ki yi zamanki Didi, kina fama da kan ki bai kamata kina zirga-zirga ba." "To fa a min gaskiya Nayla, kin saka gabana sai fa uwa yake yi." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Babu abinda ya yi min Didi, hasali ma ni ko magana bata ha a mu dashi ba." Tana ji Didi ta sauke ajiyar zuciya, kafin ta yi magana Nayla ta ce, "Kawai zaman auren na mu ne ya zo arshe, na fa a masa ya kar i numberta a wajanki ya turo min sa on saki ba lallai sai ya rubuta ba." Didi ta sauke numfashi ta ce, "Kin yi daidai Nayla, kin yi abinda ko wacece a matsayinki abinda ya kamata tayi kenan. Ki yi ha uri Nayla! Ki yi ha uri!" Didi ta fa a muryarta na sha ewa. Nayla ta ce, "Didi meye na bani ha uri kuma?." "Nayla ban san me zan ce miki ba, kin auke ni tamkar Yayarki, Hajja ta auke ni jikarta, kun yi min komai a rayuwa amma da abinda zan saka muku kenan. Nayla...." Sai Didi ta kasa magana saboda kukan da ta ji ya taho mata sai kawai ta yanke wayar. Nayla ta damu sosai, ta kira Didi bata auka ba ta kalli Salma ta ce, "Kuka fa na ji Didi tana yi Salma." Salma taja tsaki ta ce, "Ai dole ta yi kuka, wannan ani nata ya zamar mata adangaren bakin tulu, ta karshi ta kar tulu, ta bar shi ya ata ruwa. Ana murna an rabu da targa e sai karaya ga ta samu." "Hmmm" Nayla ta ce kawai bata ce komai ba. Salma ta yi arin sake kawar mata da damuwa suna ta hira har Ummimi ta shigo suna labari. Mama ce ta shiga akin bayan sallar azahar ta ce, "Nayla kina da ba uwa." Kafin Nayla tayi magana Didi ta bayyana a akin fuskarta cike da damuwa. Nayla ta mi e tsaye ta ce, "Didi sai da ki ka fito don Allah? Ki daina takurawa kanki fa,ki duba yanayin da ki ke ciki mana." Didi ta ri e hannunta ta ce, "Nayla fitowar ce ta zamar min dole, dole nazo na same ki." Zama suka yi a kan gadon, Didi ta kalli Mama da take tsaye ta ce, "Mama don Allah ayi ha uri da abinda ya faru, wallahi ban san ma tana gida ba sai azu da muke yin waya. Don Allah ku yi ha uri, Nayla bata cancanci zuwa gida a irin wannan yanayin daga gare mu ba, don Allah Mama...." Mama ta dakatar da ita ta ce, "Haba Aisha, wannan magiyar ta meye haka?. Mu da ke duk an zama an uwa, kallon jikar Hajja mu ke yi miki meye na wannan magiyar haka?. Kuma ai naga ba laifi aka yiwa Nayla in ba balle ki ce zaki bada ha uri." Didi ta yi murmushi ta ce, "Mama na san halin Omar kamar yunwar cikina, wata ila wani abun ya yi mata da ta kasa jurewa." Mama ta ce, "Nayla ta ce babu komai kawai ta gaji ne tana son ya saketa ta auri wanda ya ke sonta, tun farko ya nuna baya son auren nan ban san dalilinsa na kar ar auren ba. Dan baya so ai baza ka yi masa dole ba, itama kuma yanzu ta ce bata so kinga an huta kowa baya so sai a rabu lafiya. Don Allah ki daina wannan magiyar haka, Ummimi zo ki kawo mata abinci" ta fa a tana fita Ummimi tabi bayan ta. Didi ta sauke kai asa cikin sabuwar kunya da nauyi Mama, da ace ana canja mutum ya dawo yadda ka ke so tabbas da ta canja Omar. Ta ri e hannun Nayla ta ce, "Nayla na san a zama ki da Omar ya yi miki abubuwa marasa da i, bai auki auren ku da mahimmaci ba balle ya baki mahimmaci kamar ko wacce matar aure. Ina baki ha uri akan hakan, ba wai a madadinsa nake baki ha uri ba, Ina baki ha uri ne saboda laifin da yayi, matsayina na ar uwarsa ya zama dole na bada ha uri akan laifinsa. Ki duba yanzu yadda Mama ta tarbe ni, har nan akin aka kawo ni saboda ba a auke ni matsayin ba uwa ba, ar gida ce ni zan iya shiga ko ina. Mama ta hana ni bada ha uri ta ce nima jikar Hajja ce, ta kuma ce azo a kawo min abinci. Nayla ta ya zan ji da i ace an uwana wanda mu ke ciki aya dashi yake wula anta jinin Hajja na ji da i a zuciyata?" Ta fada muryarta na rawa saboda hawayen da ya taru a idanunta. Nayla ta ri e hannunta ta ce, "Didi ni baki min komai ba, Shima kuma bai yi min komai ba, na yanke hukunci ne saboda ya ce har abada bazai so aurena ba. Kin ga in na zauna dashi ni zan cutu, shiyasa na yanke wannan hukunci ko da bazai min da i ba." Didi ta ce, "to ko akan wanna kalaman nan na Omar ai ya zama dole na baki ha uri, da ana canjawa mutum zuciya da na canjawa Omar ta sa." Salma ta ce, "Didi ki daina kuka don Allah, kina third trimester bai kamata ace kina saka damuwa haka a zuciyarki ba." Ta kalli Salma ta ce, "Salma Omar ne fa, Omar ne ya fa awa Nayla haka in ban damu ba ya zan yi?." "Ai ba ke kika fa ba, kuma shima dan ya fa a ai abinda yake ransa ya fa a ba wani abun ba. Kinga yanzu ta ce itama ba taso ba shikenan ba?." Didi ta yi murmushi kawai ta goge idanunta ta kalli Nayla ta ce, "Kin yi daidai Nayla, kin yi daidai da ki ka dawo gida, don Allah ki saka Daddy ya maka shi a kotu, ya saka ayi masa hukuncin da za a kai shi gidan yari ayi masa horo mai tsanani." Nayla ganin yadda Didin take magana bilha i da gaskiyarta sai tayi dariya sosai ta ce, "To Hajiya Didi." Didi ganin tana dariya ya saka ta ce, "Ba wasa nake yi ba, inda zan samu abinda zan yiwa Omar wanda zai ji a jikinsa da zuciyarsa wallahi sai na yi. To komai baya bashi tsoro, komai baya aga masa hankali abinda yake gabansa kawai yake yi. Yanzu an kar o sakin?." Salma ta ce, "A'a, Daddy ya ce zai bashi lokaci in yazo da kansa to, in bai zo ba kotu zata aika masa da sammaci. Abba ya ce babu wanda zai je nemansa, in ya damu zai zo, in ba damu ba kotu zata kira shi." Didi tana girgiza kai ta ce, "sai dai sammacin kotun ya riske shi, zuwan Omar nan ba abu ne da nake ganin zai yu ba. Amma da zai yu zan fi kowa farin ciki, daga wannan lokacin zan samu abinda nake nema wanda zai ta a zuciyarsa da jikinsa." Salma ta ce, "meyasa ki ka ce haka?." "Salma indai Omar ya zo gidan nan ko ya nemi inda Nayla take wallahi yana sonta, ni kuma da wannan son zan yi amfani wajan hukunta shi sai na tabbatar da auren ya are." Salma tayi murmushi haka ma Nayla ta ce, "Didi kina ji, yanzu mu nar zancen kawai, ki daina cewa zaki bani ha uri bana jin da i wallahi a zuciyata, ke Yayata ce, zaki ta ya ni ya in neman saki a gare shi ba bani ha uri ba." Didi tayi murmushi ta ce, "Haka ne Nayla, amma Ina tsananin jin kunyar tsatson hajja." Ummimi da ya shigo da tray na abinci ya hana Nayla magana, suka yiwa Didi dole ta ci abinci, da Salma ta lura hirar Omar na ta a Nayla shiyasa ta kawar da ita suka fara hirar duniya kamar komai bai faru ba. Driver Mama ne da kansa ya tafi mayar da Didi bayan ta gama suka yi sallama da Mama ta tafi. Fans kuna ganin zuwan Omar zai yu kuwa.....? KRB3P032 Arewabooks@nanahaleema11. Nayla haka ta cigaba da zama a gidan Mama tana samun kulawa ta musamman, ita kuma ta dage da addu'a akan Allah ya kawo mata mafitar da zuciyarta zata iya auka. Maman su Jidda ta dame ta akan yaushe zata koma sai ta ce mata ta kusa komawa. Ta cigaba da zuwa aikinta kamar babu abinda ya faru, dan ta yi arin danne abinda yake zuciyarta saboda su Mama da suke tsaye a kanta wajan kulawa kar ta dinga sage musu guiwa. Omar kuwa gaba aya ya rasa abinda yake damunsa, hatta ma'aikatansa duk sun rasa gane kansa dan gaba aya ko zuwa ya daina duk abinda ake so sai dai ayi masa waya. Duk da daman ba mutum ne mai yawan wasa ba, amma in yana cikin farin ciki da walwala ana ganewa, yadda fuskarsa ta ke a cushe da kuma rashin yin magana ya saka suka tabbatar da akwai abinda yake damun Ogan na su. Ga shagunan cikin kasuwa da ake ta shirin bu ewa an bu e, amma ba a zauna dashi ba balle a san tsarin da yake so ayi. Ya hana kowa ganinsa saboda shi kansa bai san abinda yake damun zuciyarsa ba. Ko Didi tun daga ranar basu sake magana da ita ba ko a waya, bata neme shi ba shima bai neme ta ba amma tana ransa. Har aka yi kwanaki biyar da tafiyar Nayla ya rasa abinda yake masa da i, gidan kuwa tunda ya bar gidan bai sake komawa ba yana kulle ya tare a gidansu gaba aya. Yana zaune a gida su da magriba ya yi shiru yana aikin tunani, zuciyarsa ta yi masa nauyi sosai, ya kuma san rashin magana da Didi ne ya kawo hakan, abinda yake bashi mamaki bai ta a jin nauyin zuciyarsa har haka ba, ya rasa wanne irin tunani ma ya kamata ace ya yi. Goje ne ya shigo gidan da sallama ya amsa a ciki yana kallonsa, ya ce, "Damisa ka ce zaka aiko da wannan kayan ba a