Sashe 49
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka yi dasu aka munafurce ni aka yi min aure ba tare da na sani ba!?." Didi ta ce, "ko a nan ya kamata ka fahimci matsayin da suke dashi a rayuwarka, tunda gashi kana zaune da auren da su ne suka kar e shi, hatta sadakin auren ba kai ne ka biya ba su ne suka bayar saboda su ne iyayenk a!" Ta fa a ido a waje itama tana kallon sa. "Saboda ke, saboda kin yi min dole ya saka nake zaune da auren nan kema kin sani, ban ce ina so ba kuma bazan ta a so ba. Har abada bazan ta a son abinda ya zo daga gare su ba cikin harda auren nan!. Ke ka yi min dole na kar a, ke kika yi min dole nake zaune a gidan nan, ke kika yi min dole nake rayuwa a cikin gidan, ke kin san ba dan ke ba babu wanda ya isa ya saka na kalli maganar auren nan ma balle na kawo shi cikin rayuwata. Ki goge tunanin sun zama iyayena dan kawai sun kar in auren da ban ce ina so ba, kuma har yanzu ban so!" Ya fa a cikin fusata yana kallon ta. Didi bata san ta tsinke shi da mari ba sai da ta ga yadda ya sake bu e ido yana kallonta idanunsa sun zama jajaye sosai. Irin fusata da fushin da yake kan fuskarsa ba dan Didi bace zai iya sha e ko waye a kusa dashi. acin rai ne yake tasowa daga asan zuciyarsa yana mamaye ilahirin jikinsa, fusata yake ji tana shiga jininsa tana zaga ko wanne lungu da sa o na jikinsa. Hannunsa rawa yake yi, hannunsa ayi yake yi, ba dan Didi ba ce da yanzu ba wannan zancen ake yi ba. Didi itama fushin ne akan fuskarta wanda bata ta a yi ba a rayuwarta, ta nuna shi da yatsa cikin rashin sanin abinda zata ce sai ta ce, "Kana bani mamaki." Shi kam ya kasa magana kallon ta kawai yake yi, wai Didi ce ta mare shi, mari akan wa anda baya so da kuma auren da aka yi masa ba tare da yana so ba. Yadda yake huci ya kasa magana kana kallonsa ka san ya gama zuwa arshen acin rai, ji yake kamar ya zaro zuciyarsa ya cillar saboda acin ran da yake ji. Idanunsa har ruwan acin rai suka tara, ya kalle ta yana nuna kansa da yatsa ya ce. "Ni ki ka mara?." Didi tayi masa banza bata kula shi ba, ya girgiza kai sai kuma ya shafa fuskarsa, ya cize baki ya naushi hannunsa guda aya. Jikinsa har rawa yake yi, cikin tsananin acin rai ya ce, "yau na tabbatar da kin fifita su a kaina! Su ki ke kallo a matsayin an uwanki bani ba!." Didi cikin wani irin yanayi ta ce, "Ban fifita su akan ka ba, abinda ka ke yi ne bana so, kuma ina so ka sani, su ne iyayenka ne ko baka so!." "Saboda auren da aka yi min ne ya saka ki ke cewa iyayena ne? Kema kin san in da ace da sani na babu wanda ya isa ya aikata hakan ko!?" Yadda muryarsa take fita ya saka ta kulle ido dan ta san ransa ya gama aci, ta san zai iya furta ko wacce kalma akan auren, ta san zata iya ji ya furta kalmar saki akan Nayla ita kuma ba haka take so ba. Baya tayi kamar zata fa i, Nayla da ta gama suman tsaye a wajan ta farfa o ta ri e Didi ta ce, "Ki zauna Didi." Kamar ta farkar dashi daga mafarki ya kalle ta cikin tsananin fusata da acin rai, hannunsa yana rawa ya ce, "Ke bana son aurenki, ban ta a ji a zuciyata ina son zama dake ba, Ina zaune dake ne saboda Didi, duk abinda nake yi a gidan nan saboda ita ne. To naga lokaci ya yi da komai zai are tunda har abin ya kai ga haka......" Ya dafe kai tare da runtse ido, ya bu e ido ya sake kallon Nayla ya ce, "A kan aurenki ta aga hannu ta mare ni, tun ina arami muke tare da ita bata ta a dukana ba koda wasa sai yau, yau in ma a kanki da wa ancan munafukan. To ina so ki san bana sonki kamar yadda bana son aurenki, kina zaune dani ne saboda alfarma, Ina kwana a gidan nan saboda dolen da aka yi min a kan ki. Tunda abin nata ya zama haka yanzu komai zai are, bazan......." Didi ta mi e tsaye da hanzari ta katse shi ta ce, "Omar ka dakata!." "Bazan dakata ba! Bazan dakata ba!. Ni kika auki hannu kika mara, tun ina arami baki ta a aikata hakan ba sai yau, tun lokacin da nake ji da tantiranci, nake zubar da jinin mutane, nake auko miki magana, ki ke yawo a kan titi kina nemana, ki ke zuwa police station belina, ki ke zuwa prison kai min ziyara, baki ta aga hannu kin mare ni ba sai yanzu. Akan su da kuma kan wannan aurenta kika aga hannunki da kike rarrashina dashi ki ka mare ni ko Didi?!" Ya fa a tana kallon ta idanunsa har ruwa suka tara saboda acin rai, jikinsa rawa yake yi haka bakinsa. Jijiyoyin kansa sun tashi, duk wata kafa ta gashi a jikinsa ta bu e, fuskarsa tayi ja matu Didi ta runtse ido, saboda tashin hankali har an cikinta sai da ya motsa saboda bala'in Omar. Ta runtse ido ta ce, "Babu ruwan auren nan a cikin maganar nan, na sako shi a ciki ne saboda ka san mahaimmacin su a gare ka." "To bana son auren ai, na fa a miki tun farko ai ko? Tun kafin azo nan na ce miki bana so kuma bazan kar a ba. Amma me ki ka ce min? Dole ki ka yi min ba dan ina so ba kika jawo ni har nake zama a cikin gidan nan. Didi na gaji da dolen da ki ke yi min, bazan sake aikata abinda bana so ba saboda ke!" Ya fa a yana nuna Didi da yatsa cikin fitar hayyaci. Ya nuna Nayla hannu yana rawa amma Didi yake kallo ya ce, "Kin tuna? Kin yi min fa a a kanta, kin ce min ina shirme a kanta, kin kore ni daga falon ki akanta, kin yi min dole na kar i aurenta, kin yi min dole na zauna da ita, kin yi min dole ina saurarenta, kin yi min dole ina shiga lamarinta, yanzu kin mare ni ta dalilinta. Me zai saka ni na so ta har na so aurenta? Me zai saka ni na zauna da aurenta!?. Cewa ki ka yi in ban kar i aurenta ba babu ni babu ke shima duk a kanta. Didi ko aljanna zan samu ta hanyar zaman aure da ita na yarda ta wuce ni, ai rahamar Allah tana da yawa, hanyar rabo tana da yawa zan samu a wani kiran rabon ba sai ta dalilin aurenta ba!?." Didi ta dafe kai ta arasa zata ri e shi ta ce ta ce, "Omar ka saurare ni...." Ya fizge jikinsa ya ce, "bazan saurareki ba, na gama saurarenki Didi, na gama sauraren maganar ki akan abinda bana so har abada. Wallahil azim bazan ta a son abinda ya fito daga hannunsu ba ciki harda auren nan da ita kanta!. Komai ya zo arshe, komai ya lalace Didi, komai ya are!" Ya fa a can asan ma ogwaro yana kallonta dan jijiyar kansa har harbawa take yi. Didi dafe kai tayi ta zauna ta fara rawar jiki saboda yadda kanta yake sarawa. Nayla kuwa ta gama amewa a wajan tun daga kan maganar da ya kalle ta ya fa a, jikinta ya gama yin sanyi zuciyarta ta gama karyewa a lokacin. Hawaye ya gama wanke mata fuska, jikinta ya gama mutuwa gaba aya. Shiyasa ta kasa koda motsi, da yar ta iya ta ri e Didi tana ganin yadda jikinta yake rawa sosai. Shi kuma dakatawa ya yi da maganar ganin yanayin Didi ya canja, ransa ya riga ya kai arshe wajan aci, huci kawai yake yi kamar kumurci. Kallon ta yake yi kawai amma ya kasa ce mata komai saboda wutar acin rai da unar zuciyar da take ruruwa a zuciyarsa. Wai Didinsa ce ta mare shi, mari akan kuncinsa kuma saboda wa anda ya fi tsana a duniya. in ya tuna hakan sai sai ya ji kamar ya kurma ihu. Ji yake kamar ya bankawa gidan wuta, da shi da Didin da Nayla duk su mutu a huta. "Didi!" Nayla ta fa a a sanyaye tana daga tsaye. Didi bata motsa ba sai rawar jiki da take yi ta ce, "Didi mu je asibiti, baki da lafiya" ta fa a hawaye na sake zubo mata. Didi ta ce, "Nayla ri e ni mu fita." Nayla ta du a ta ri eta, ta saka hijjabinta da yake gefe ta ri e hannunta suka fita daga falon har lokacin yana tsaye. Nayla ta bu e gaban mota Didi ta shiga, ita kuma ta arasa gate in ta bu ofa tana duba su Bashir, ganin babu kowa a cikin su wanda zai bu e mata sai ta bu e da kanta ta shiga motarta fita ta bar shi a bu Didi ta ce, "Nayla mu je gidan mu kawai." "Didi baki da lafiya." "Ciwon kai ne kawai, mu je gidan mu Nayla, akwai key in gidan a hannuna." Da yake babu nisa ba jimawa suka araso. Nayla ta ajjiye motar ta ri e Didi har gidan ta bu e mata ta shiga. Gidan yana nan yadda yake ko ura babu sosai dan yana zama a ciki sosai. A kan kujera Nayla ta zaunar da ita, ta auki ruwa ta bata tasha ta ce, "ki sha ki kwanta ki huta Didi." Didi ta yi ajiyar zuciya tana kallon Nayla da fuskarta ta tayi ja tana tuna abinda ya faru. Didi ta sunkuyar da kai bata ce komai ba tana shan ruwan. Ajiyar zuciya ta yi bayan ta sha ruwan tana kallon Nayla, ta jingina da kujera bata san me zata ce mata ba.