Sashe 60
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
saketa." Shiru ya yi bai ce komai ba, ya kalle ta zai sake magana sai ya yi shiru. Didi ta yi murmushi ta ce, "Omar shiru ba shine abinda ya kamata ka yi, ni so make ka saukewa yarinyar nan auren ka da yake kanta ta huta wallahi." Banza ya yi mata bai kula ta ba ganin haka sai bata sake magana ba. Ido taga ya rufe ya bu e ya sake kallon ta ya ce, "ki yale ni don Allah" ya fa a yana auko waya ya kira Bashir ya ce in ya gama ya dawo su tafi. Didi ta ce, "ba fa zan yale ka ba Omar, dole na saka ka yi abinda ya kamata." Ya ta e baki ta ya ce, "kin san da haka meyasa ki ka yi min dole na kar i auren?." "Na auka zaka so ta da zuciya aya, nayi tunanin zaka zauna da ita ka ri eta amana, ka bata farin cikin da take burin samu a gidan mijinta. Amma sai na ga ba haka ba, sai na ga har yanzu baka kallon ta a matsayin matarka, in na yi magana sai ka ce ai dole aka yi maka ba so ka ke yi ba. Tunda har yanzu baka jin zaka iya kar arta matsayin matarka gwara a rabu in ya fi alkhairi." "Za a rabu in, sai sanda na yi niya babu wanda zai min dole a lokacin da ban ga dama ba" ya fa an ya oye yanayinsa. Didi ta murmusa ta ce, "Hakan ne ya kamata, ni na auka ma a ranar ka furta mata ka huta da wahala ai." Mi ewa tsaye yayi ya ce, "Magana da ke ma damuwa take ara min, dana sani ban zo ba." Didi ta mi e tana dariya ta ce, "ai na fa a maka, in dai ba abinda nace ka yi ka aikata ba baza ka dawo daidai ba, kuma ka ga daman ba idda ce a kanta ba, in ka saketa aurenta zata yi ta huta. Akwai masu sonta sosai, harda an uwanta da yake sonta kuma a gidansu take zaune." "Mtsw!" Yaja tsaki yana barin falon. Murmushi ta yi ta ce, "Allah ya sa hasashe na ya zama gaskiya" ta fa a tana biyo bayansa amma ta samu har ya fita. Da Bashir suka gaisa sannan suka bar unguwar. Omar da ya koma haka ya dinga juya kalaman Didi, bai san meyasa kalaman suka yi masa nauyi har baya so ya ji ta furta kalmar saki ba, in ya tuna da kalmar sai gabansa ya fa i ya ji a zuciyarsa bazai iya furta wannan kalmar ba gaba aya. Furzar da iska yake yi ya dafe zuciyarsa yana jin yadda zuciyarsa take bugawa, ya cize baki yana jin rauni yana mamaye masa zuciyarsa. Ya shiga damuwa sosai fiye da yadda yake tunani, haka kawai ya ji ranar a gidan yake son kwana, ya sake komawa duk da an kiran da ake yi masa a gidan. akin Naylan ya kwanta yana jin kewa mai tarin yawa a zuciyarsa, amma bai san kewar ba ce tunda bai ta a jin yana kewar wata halitta a duniya ba, ya auki hakan a matsayin nauyin zuciyarsa take yi masa, bai kawo kewarta yake yi ba ko ka Wasa-wasa har kwana biyu Omar ya tare a gidan a kuma akin Nayla, sannan ko yaushe cikin jin muryarta yake tana kiran sunansa. Ya shiga damuwa sosai wacce ta haifar masa da kasala da kuma zazza i mai shegen zafi. Kansa ya yi masa nauyi saboda ciwo, ya rame lokaci aya sai haske da ya sake yi, dan shi daman zama waje aya yana saka shi haske. Bashir ya kira a waya yana zaune a falon ya aike shi siyo magani saboda yadda yake jin zazza in na ratsa asusuwan jikinsa. Bayan ya kawo masa ya sha, Bashir ya tsaya yana ta yi masa sannu bai ta a ganin Ogan na sa a wannan yanayi ba. Bashir shi ya sanar da Didi Omar ba shi da lafiya, da daddare mijinta ya kawo ta dan ta duba shi. Da ta shiga falon a zaune ta tarar dashi idanunsa a rufe, ta kalle shi da kulawa ta ce, "Sannu Omar, ashe baka da lafiya ban sani ba." Tashi zaune ya yi sosai suka gaisa da mijinta kana ya kalle ta ya ce, "Zazza i ne kawai." Didi ta ce, "Wannan ya wuce kawai, kalli yadda ka koma fa, ka je asibiti?." Kai ya girgiza alamun a'a ta ce, "Zama ai ba naka bane, asibiti ya kamata ace ka je. Ka rame, fuskarka ta bayyana rashin lafiyarka a fili." Juyawa ta ga ya yi yana kallon falon kafin ya kalle ta ya ce, "Wai baku ji ana kiran sunana ba?." Didi ta kalli AbdulHamid kafin ta kalle shi ta ce, "ni ban ji komai ba." "To meyasa ni nake jin muryarta tana kiran sunana? Ko dai aljana ce daman?." Didi ta yalk yale da dariya ta ce, "Ko kuma aljanun ne suka ji sunan yayi musu da i suke kiranka ba." Share maganar ya yi bai ce komai ba ta ce, "Omar kwanaki na ta tafiya har ta kwashe kwana takwas a gida, yaushe zaka je ka kai mata takardar ne?." A fusace ya ce, "ni ban san meyasa ki ka damu haka ba, ki yale ni mana duk lokacin da na ga dama zan yi ai na fa a miki. Meyasa ki ke min naci a kaine? Na tsani wannan kalmar nan da ki ke fa a, bana jin da inta meyasa baza ki gane ba!?." Didi ta ce, "masifaffe, Allah ya baka ha uri, tuna maka nayi dan ka sauke abinda yake wuyanka." aramin tsaki ya yi ya kalli AbdulHamid ya ce, "Ka yiwa matarka magana ta daina bana so, ta yale ni in nayi ra'ayi zan yi ai." Abdulhamid ya ce, "To Omar." Kallon gefensa yake yi bayan ya dafe goshinsa, zuciyarsa kamar ana gasata a tukuba haka yake ji. AbdulHamid ya kalli Didi ya yi murmushi itama murmushin ta yi sannan ta ce, "Omar me ka ke ji a zuciyarta ka? Anya baza ka je asibiti ba?." Kamar jira ya ke tayi magana sai ya ago ya ce, "Nima tunanin da nake yi kenan, ya kamata naje na ga likita wannan yanayin bana lafiya bane, wata ila na kamu da ciwon zuciya." "To kai meye a zuciyar taka da zai saka maka ciwo Omar?"AbdulHamid ya fa a yana kallonsa. Omar ya kalle shi ya ce, "Komai ma akwai." Abdulhamid ya ce, "Ba sai ka je wani asibiti ba, zama ya kamata ka yi ka tuna daga yaushe ka fara jin haka, in ka tuna rana da lokacin sai ka tuna me ka rasa a lokacin wanda kafin ka fara jin wannan yanayin yana tare da kai, bayan ka rasa shi ka fara jin abinda ka ke ji. Ko da ace wayarka ce ka tuna ita ka rasa daga lokacin da ka fara jin hakan da zarar ka sake mallakar wayar zaka daina jin abinda ka ke ji, duk abinda ka binciko ka ga shine silar shigarka wannan yanayi to tabbas kana matu aunarsa Omar!, kana yi masa soyayya ba ta wasa ba, soyayya ka ke yi masa wacce baza ka iya ha uri da rashinsa ba." Omar ya zuba amsa ido yana kallonsa ko ifta ido baya yi. AbdulHamid ya ce, "in mun tafi ka zauna kayi tunanin, duk abinda ka rasa a lokacin zaka fahimci maganata gaskiya ce." Omar ya yi ajiyar zuciya ya kalli Didi da take kallonsa ta ce, "abinda ya kamata ka yi kenan, ta haka ne ka ai zaka samo maganin damuwarka." Omar a raunane ya ce, "to zan yi. Amma ina neman alfarmarki don Allah kar ki sake yi min maganar yaushe zan kai takardar saki, ki yale ni na gama da abinda yake gabana kafin komai ya biyo baya. Ta lafiyata nake yi, wannan yanayin ya canja ni gaba aya ko aiki bana iya yi. An bu e shaguna har guda hu u amma babu wanda na iya zuwa na gani saboda wannan abinda yake damuna. Rauni ba bai yi daidai da zubina ba, ni ba mutum mai rauni bane wallahi, ki bari na samo abinda ya saka zuciyata rauni in ya so sai mu yi magana. Ni nace bana son aurenta kuma ni zan raba shi." Didi ta ce, "To Omar na daina." Kai ya girgiza bai ce komai ba Didi ta ce, "ga abinci nan na kawo maka in ka ci sai ka sake shan magani, Allah ya kawo mafita ." Bai amsa ba AbdulHamid ne ya amsa da amin suka tashi suka tafi dan su bar shi yayi tunani. KRB3P033 Arewabooks@nanahaleema11. A mota AbdulHamid ya kalli Didi ya ce, "Omar bazai iya sakin yarinyar nan ba, yana matu aunarta wallahi, yana yi mata soyayyar da bai san yana yi mata ba." Didi ta ce, "na so na fahimci hakan, amma kuma in na tuna waye shi sai naga anya zai yu kuwa?. Ka duba har yanzu shi baya kawo ta cikin damuwarsa, tunda gashi ka ji ya ce shine yace baya so kuma shi zai raba. Ni ban auka yana da hankalin da ya san ko nida kai ya furtawa ya saketa ta sa ku ba, ya i furta kalmar koda wasa." AbdulHamid ya yi dariya ya ce, "yana da hankali da ilimi fa, ta ya zai aikata hakan? Saki ko baka je makaranta ba indai kana social media yadda malamai suke wayar da kai a kansa ai zaka sani. Balle ga makarantar da ki ka ce yana attending online, ko ya manta wani abun zai tuna indai yana bibiyar karatun. Ki zuba ruwa a asa ki sha, Omar yana sonta wallahi, baza ki bini bashin rantsuwa ba, Omar bazai iya sakin yarinyar nan ba." Didi ta yi murmushin jin da i ta ce, "in hakan ya kasance zan fi kowa murna da farin ciki. Amma anya Omar zai je gidansu Nayla kuwa? Har yanzu bai amince da soyayya ba fa." "Ai daman a yanzu bazai amince ba, sai ya sake ji a jikinsa sannan zai damu. Ke wacce damuwa ki ka ta a ganin ta saka shi rauni haka har da zazza i?." Didi