← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 205

Sashe 134

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kalle ta ya amsa da amin yana murmushi yana cigaba da bata labarin abubuwan da suka faru a can. Da daddare suka je gidan Didi aka kai mata tsarabar ta ita da Marmerh, a can suka zauna har goma na dare sannan suka dawo gida. Wayarsa tana hannunta ta ji shigowar message wayar tayi haske, ta kalla ta ga number ce sannan ga abinda aka rubuta nan tana iya gani ta notification. Gabanta ya fa i ganin kalaman soyayya da na ban ha uri, da hanzari ta danna message in ya bu e a nan ta ga messages in da yawa alamun ba yau aka fara ba. Bi ta dinga yi tana karantawa tunda ka an-ka an ake rubutowa har ta zo kan wanda aka turo a lokacin. A lokacin Omar ya shiga akin, ya bita da kallo ganin yanayin ta ya canja ga kuma wayarsa a hannunta, ya kalle ta ya ce, "Ya dai?." Ta kalle shi ta ce, "Yaushe ta fara yi maka messesges babu labari?. Ya kalle ta da mamaki ya ce, "Wacece?." "Narma!." Ya an yi jimmm alamun mai tunani kafin ya ce, "Wacece ma haka?." Ta zuba masa ido jin yana raina mata hankali ta ce, "budurwar ka." "Kin sake atar dani, na san sunan Narma amma na manta wacece." Zuba masa ido tayi tana binsa da kallon kana raina min hankali mai cike da tuhuma. Shi kuwa Omar tunani ya tafi kafin ya ce, "ohhh wai ar sanata? daman itace take damuna da message?." Ran Nayla ya aci jin yana mata wata tambaya ta rainin hankali ta ajjiye wayar ta ce, "Ashe ka gane wacce nake nufi, in ma itace take maka messages in ai ka sani." Ganin zata fara kuka ya zo kusa da ita ya auki wayar yana duba messages in ya yi tsaki ya ce, "Ban ta a bu ewa ba balle na san wacece, da ya shigo nake goge shi a notification shikenan." Ta kalle shi hawaye cike a idonta ta ce, "Har yanzu tana sonka daman?." "Yanzu meye na kukan? Daga ganin messages sai ki fara kuka....uhum?." "Kana ganin irin kalaman da take fa a maka, itace wacce ka fara so, zata dawo gare ka, zaka aureta, haka fa take cewa" ta fa a kukan ta na yin arfi. Ya tsuguna a gabanta, ya jawo ta jikinsa yana shafa bayanta ya ce, "ni ba dan kin karanta ba ban ta a bi ta kai ba, kuma mantawa nayi shiyasa ban fa a miki ana yi min messsge ba. Ki daina kukan nan shine bana so." Nayla ta ago ta kalle shi shima ita yake kallo ta ce, "Don Allah kar ka bata amsa ko sau aya, in ka kulata mutuwa zan yi." Ya ri e fuskarta ya ce, "ki auka ban santa ba, ban ma ta a ganinta ba, kuma in na kula ta ai zaki gani, tunda wayata ko yaushe tana hannunki kuma babu inda na ce kar ki bu e a cikinta. Duk inda ki ke so ki shiga ki duba ki gani in na ta a yi mata magana, yadda zuciyata ta kasance mallakinki, gangar jikina ta zama ta ki, babu wani abu nawa da zai kasance sirri a gareki. In kina kokwanto ki auki wayar ki duba Jidda." Ta koma jikinsa tana kuka ta ce, "na yarda da kai, kawai ina kishi ne, zuciyata zafi take yi." "Ki yi ha uri" ya furta a hankali a kunnenta yana shafa kanta zuwa bayan ta ya ce, "ki yi shiru." Kukan ta daina ta ago ta auki wayar ta yi deleting messages in duka ta jefa number a block, ta shiga whatsApp insa ta nemi number ta ga kuwa messages in da aka yi dan bai ma ta a bu ewa ba, ta yi blocking bayan ta goge su duka. Ajjiye wayar ta yi ta dafe kai tana ajiyar zuciya. Ya bita da kallo ya ce, "hankalin ki ya kwanta?." Ta aga kai alamun eh kafin ta ce, "in ta kira kar ka auka ka ji?." Murmushi ya yi ya ja hancinta ya ce, "To." Zama ya yi kusa da ita ta kwantar da kanta a kafa arsa ta ce, "ina kishinka Rouhii, ina kishinka sosai. Kar ka kula ta don Allah, ka daina kulata ka ji!." Murmushi ya yi bai ce komai ba, Allah na tuba banda rigima irin ta Nayla shi bai ga abin kishi da Narma ba, ita bata san in ya wuce waje baya dawo baya ba ne shiyasa. Cikin aramin lokaci aka cigaba da modernizing kayan Omar da kayansa da yayi order, kaya suka sake yin kyau sosai in aka saka a kwali aka baka baza ka ce made in nigeria bane, saboda komai yayi kamar kayan asar waje. Tunda ta goge messages in Narma bata sake gani ba, duk da bata bincika masa waya duk da ya bata damar hakan amma bata yi, kawai messages take dubawa taga zata gani amma babu sai hankalin ta ya kwanta. Cikin haka ta ga mail in da aka turo masa, ta karanta jikinta na rawa ta mi e tana jira ya fito daga wanka ta fa a masa, ban akin ta so shiga ta fa a masa amma sai ta fasa dan ta san bazai barta ta fito ba, sai ya gama lugwigwita mata jiki zai yaleta. Jikinta har rawa yake yi saboda murna tana jira ya fito, yana fitowa ta kwasa a guje ta afe shi ya ri e ta ya ce, "zaki fa i ki ji ciwo, lafiya?." Sauka tayi daga jikinsa ta nuna masa ta ce, "Mail aka yi maka, kalli kaga kamfanin sarrafa takalma na asar Chine su ne suke son ka basu lokaci su tattauna da kai. YaMar a kaf duniya babu asar da ta fi asar China manufacturing shoes, sun nemi zama da kai duk yadda aka yi babban alkhairi ne." ar wayar ya yi ya kalle ta ya ce, "kuma ba an damfara bane?." "Kalli ka gani mana, ba su bane. Ga stamp da logo nan sun turo maka in kana kokwanto a kai." Murmushi ya yi ya rungume ta tsam ya ce, "Alhamu lillah!." "Allah mun gode maka, Yanzu yaushe zaku zauna dasu? Ka yi reply in mail in dan a san ka gani" ta fa a jiki ta har rawa yake yi. Ya zaunar da ita ya ce, "ki nutsu tukunna." "Bazan nutsu ba YaMar, ka basu date da time da kuma venue kawai. Suna da agent a Nigeria kawai zuwa zasu yi su ha u da kai." Omar ya ce, "To wacce rana ki ke ganin za a saka?." "Friday, kaga yau tuesday ka basu friday saboda albarkar ranar. Don Allah ka yi reply dan su san ka gani." Tsayawa ta yi ta ga yana typing kuma da turanci yake rubutun, ganin tana kallonsa sai ya kalle ta ya mi a mata wayar ya ce, "Na yi daidai?." Ta Harare shi ta ce, "raina min wayo kawai ka ke yi wallahi." "Allah ki duba ki gani." Kar a ta yi tana gan, babu abinda ta canja kawai ta tura. Messages in na zuwa suka dawo da amsa yaushe zasu ha u, ko fa a masa bata yi ba ta basu date kafin ta kalle shi ta ce, "A ina zamu zauna to? Wannan hotel in da muka je ai yana da kyau, bara na rubuta sunansa." Shi kallon ta kawai yake yi ganin kamar ma ta fishi farin ciki jikinta sai rawa yake yi. Farin ciki yake ji a zuciyarsa ya samu macen da take son cigaban sa fiye da nata cigaban. Tana gama turawa ta kalle shi ta ga ya zuba mata ido yana kallo, sai ya yi murmushi ya ce, "ke ka ai tal a duniya, daga ke ba ari." Murmushi tayi ta shiga jikinsa da ko riga babu yana fara shafata ta mi e, dan yanzu sam-sam bata son wannan ala ar ta ha a su. Ko dan tana shan wahala a hannunsa wani lokacin ne oho. Ganin yana kallon ta sai ta ce, "Didi zan fa awa." Bai hanata ba ta kira Didi ta fa a mata komai. Didi ta dinga murna tana addu'a Nayla na biye mata. Shi kan ya rasa gane wacece tafi wata farin ciki a cikinsu, Nayla ko Didi?. Bayan ta gama murnar ta zauna ya kalle ta ya ce, "Jidda!." Ta kalle shi jin da yadda ya kira sunanta ta san serious abu ne, ta ce, "Na'am." Ya kafa mata idanu ya ce, "Meyasa yanzu bakya so na ta aki?." Ta sunkuyar da kai a hankali ganin yana kallonta, gaba aya sai muryar ta gushe akan fusksrta. A sanyaye ta ce, "yaushe na ce bana so?." Ya an ta e baki ya ce, "Sai kin fa a min zan fahimci hakan?." Ta kalle shi zata yi magana ya ce, "yanzu ma gashi kin bar jikina ina fara ta a ki, bayan da ba haka ki ke ba, akwai abinda ya canja ne? Akwai abinda nake gaza yi miki ne yanzu?." Nayla ta yi ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, "A'a." "To Meyasa?." Ta an yi shiru cikin rashin sanin amsar da zata bashi ta ce, "Babu komai, ka yi ha uri bazan sake ba." Ya aga kai ya ce, "Na yi ha urin, amma in da damuwa ki fa a min kar ki cuci kanki." Ta girgiza kai ta ce, "Babu komai." "Okay" ya fa a yana tashi yana shiryawa. Ita kanta abin na damunta sosai, gashi tana tsananin kewar mijinta amma da ya fara ta ata sai taji kamar za a rabata da numfashinta, komai ya tsaya mata cak har sai ta bar kusa dashi take jin da Shima a nasa angaren tunanin da yake yi kenan, me ya gaza mata har take gudunsa haka? Me yake yi mata wanda bata so da zarar ya ta a ta sai ta zabura kamar wacce wutar lantarki ja ta?. Raini ne ko kuma son da yake nuna mata ne ya jawo raini? Ko kuma dan ta ga yana bu atarta a kai a kai shiyasa hakan? Jan aji ne ko wula anci?. Juyowa ya yi ya kalle ta ya ga jikinta ya yi sanyi bai ce komai ba ya cigaba da abinda yake yi. KRB3P082
Chapter 134 · 0% Book details