Sashe 177
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da cikin nan zaki yi dana sanin da baki ta a yi ba a rayuwarki!. Zaki ji a zuciyarki ina ma baki san mai suna Omar a duniya ba!" Ya fa a yana wara idanunsa yana nuna ta da yatsa. Nayla itama a fusace ta ce, "Ko Marmerh ba a yiwa ani ba sai ni za a ce zan haihu? Ko Didi bata da wani cikin sai ni?." Cikin tsawa da murya mai amo ya ce, "Wannan mijinta ne ya ga zai iya, shi ya ga zai iya asarar yaran da Allah ya bashi amma ni banda ni. Ki daina ha a ni misali da kowa, dan ni ra'ayin wani ba ra'ayina bane, abinda nake so shi nake yi, babu wanda ya isa ya canja ni!." Nayla kuka take yi sosai, tana jikin Didi da take zaune bata ce komai, cikin fusata da acin rai ta ce, "Ni wallahi bana so! Bazan iya sake haihuwa yanzu ba, ko wata goma ban yi da haihuwa ba a ce ina da wani cikin? Wallahi bazan iya ba! Ni zubarwa zan yi!" Ta fa a tana kuka sosai kamar wacce aka yiwa mutuwa. A fusace ya tako ya zo wajan da take ya ri o dantsen hannunta ya rabata daga jikin Didi, ya mi ar da ita tsaye yana jijigata dan ta dawo hankalinta ta kalle shi, cikin fusata da acin rai ya ce, "wallahi! Wallahi!! In ki ka yi wannan gangancin....!" Sai ya kasa arasa fa ar abinda zai ce, ya bu e mata ido cikin tsananin acin rai ya sake cewa, "Dan baki da hankali yanzu sai ki zubar min da ciki!?. Ta ijam, da ban san wanne irin hukunci zan yi miki ba, ban san wanne irin mataki zan auka a kan ki ba. Abu aya na sani; sai kin ji ina ma baki zubar da cikin nan ba, sai kin ji ina ma baki ta a sanin Omar a rayuwarki ba!" ya fa a yana sakin hannunta. Zata yi magana ya zabura kamar zai dake ta yana nuna ta da yatsa ya ce, "kina cewa tak sai ranki ya sake aci yanzun nan wallahi, in kina musu ki yi magana Jidda! Ni kuma zan nuna miki bana fa a na canja" Ya fa a cikin tsawa yana zare mata ido. Shiru tayi ta koma kan kujera ta zauna tana kuka mai ta a zuciya. Didi duk bata ji da in abinda yake faruwa ba, tausayin Nayla take ji dan wannan shine ga mari ga tsinka jaka. Ta daure ta ce, "To Omar iya wannan tsawar da ka ke yi mata ma ai cikin sai ya zube da kansa, ka nutsu mana, ka san dole zata ji babu da i, kwata-kwata Musliha watan ta nawa da za a ce tana da ciki?." Ya kalli Didi ya ce, "in ma bata yi wata aya ba bai dame ni ba, ai tun farko na fa a mata ko wata aya ne Musliha bata yi ba ta samu wani cikin ina maraba dashi, amma dan rainin hankali cikina zata ce zata zubar? Dan shirme da zalla rashin hankali an da Allah ya bani zata salwantar min?. Hmmmm! wallahi da ta yi wannan gangancin da baza ta sake marmarin tuna ta zubar da ciki ba a rayuwarta. Ta zubar min da ciki!" Ya maimaita yana kallon Nayla. Sai kuma ya kalli Didi a fusace kafin yayi magana ta ce, "Ka nutsu mana, ka yi addu'ar Allah ya inganta shi mana, sai masifa ka ke yi. Baka da tabbacin cikin zai rayu har ya zo duniya, wannan tayar da jijiyoyin wuyan da ka ke yi akai wata ila Allah bai nufa za a haife shi ba. Ka cika kawo matsala wallahi, har yanzu ka kasa tsayawa ka fahimci abu kafin hukunci." Kallon ta yake yi har ta gama magana fuska a ha e cikin kaushin murya ya ce, "Babu abinda zai samu cikina, zai inganta ya zo duniya kamar yadda Musliha ta zo duniya. Ki daina yi min fatan cikina bazai inganta ba, bana son wannan mugun bakin" ya fa a yana harararta. Sai kuma ya ja tsaki yana kallon Didin ya ce, "Da ke ake ha a biki za a kashe min ana ko? Da ke ake so a munafurce ni a zubar min da ciki ko Didi?. Har wani cemin ki ke yi wai in bazai zo duniya ba da yake kun ulla munafurci dake da ita. To wallahi in har ku ka zubar min da cikin nan daga ke har ita sai nayi shara'a da ku, kuma a inda kuka zubar dashi sai kun je kun kwaso shi kun dawo min da kayana. Allah ya hore min, zan iya rainon yara ari koda ba nawa ba ne." Didi kallon mamaki take masa jin wai sai ya yi shari'a dasu, ko wajan wanne al alin zai kai su oho masa. Har yanzu halinsa yana nan, fusata da masifa. Takawa yake yi zai bar wajan ya juyo ya sake kallon su ya ce, "Ina maimaita mu ku, aka sake aka yi wannan gangancin wallahi....sai bai arasa ba ya girgiza kai ya ce, "dukkan ku kun san bana rantsuwa na karya, kun san sauran" ya fa a yana aukar Musliha da take ta mi a masa hannu ya hau sama a fusace. Nayla ta kwanta a jikin Didi tana kuka sosai ta ce, "Ni fa sai na zubar da cikin nan Didi." Didi tana shafa bayanta ta ce, "Ki yi ha uri Nayla, ki daina kuka. Ki bar zancen zubar da cikin nan tunda mijinki baya so." "Kar ya so mana, ari in na zubar ya sake ni, shine arshen hukuncin da zai yi min. Saki ai ba a kaina aka fara ba, mata nawa ake saki a kullum?. Tunda ba aukar raina zai yi ba ai shikenan, ni sai na zubar bazan sake haihuwa yanzu ba" ta fa a a fusace. Didi ta yi dariya jin abinda ta ce, ta san acin rai ne ya saka take fa ar haka. Didi ta ce, "ki yi ha uri ki daina fa ar haka, zubar da cikin da ba na halak ba ma haramun ne balle cikin halak wanda aka samar dashi ta hanyar aure. Meye laifin cikin? Laifi ai na Omar ne ba shi ba. A kansa zaki huce ba akan cikin da Allah ya baki ba. Don Allah ki bar batun zubar da cikin nan, ki yi ha uri ki saka a ranki Allah ya yi zuwan abinda yake cikin ki duniya shiyasa hakan ya faru. Ki kwantar da hankalinki, Allah zai baki ikon rainonsa ki haihu lafiya." Nayla dai bata ce komai ba sai hawaye da take yi, wai wata bakwai da haihuwarta ace tana da wani cikin, ita ko shekara biyu bayan haihuwa ta ga mutum ya sake haihuwa sai ta ga kamar bai san ciwon kansa ba. Amma ita gashi ko shekara aya ba a yi ba ta kwaso wani cikin, gaba aya haushin cikin ya mamaye mata zuciya, Omar kuwa ji take kamar ta je ta dinga dukansa har sai ta wuce takaicinta akansa. "Ki daina kuka Nayla, ki daina kuka bana so na ji kina kuka. Sannan don Allah kar ki zubar da cikin nan, kar ki biyewa zuciya ki aikata aikin dana sani." Nayla ta sassauta kuka tana jan numfashi cikin rauni. Rarrashinta Didi ta dinga yi har ta daina kuka, ta auko mata ruwa ta bata ta sha tana cigaba da bata baki har ta ga hankalinta ya an kwanta sannan Didi ta wuce gida. Amma ita kanta ta tausayawa Nayla sosai. P111 Nayla haka ta kwana biyu bata kula Omar shima baya kulata, ta saka in cikin a zuciyarta hakan ya saka ta fara rama saboda damuwa. Sai kuma cikin ya zo mata da laulayi ba irin na Musliha ba, tafara amai ga zazza i da ciwon kai. Har lokacin haushinta yake ji itama haka, ba ya ma ha uwa da ita saboda takaici, itama bata zuwa inda yake. In ya tuna ta ce zata zubar masa da ciki sai ya ji haushin duniya ya ishe shi, sai ya ga wacce irin iyayya take yi masa da zata zubar masa da ciki? Duk aunarta da yake yi da wannan zata saka masa. Yau ma Nayla na jikin sink tana amai kanta ya yi bala'in nauyi, Musliha kuma tana gefe tana kuka tana bu atar uwarta auketa amma Nayla bata da wannan arfin. Dawowa ta yi ta kwanta a kan carpet tana juya kai ga sanyin da take ji. Bu ofar aka yi, Nayla ta san mai aikinta ce ta ce, "Salima zo ki auketa ki bata cerelec, sannan ki taimaka min da ruwa na sha kaina zai cire." Omar ganin yanayin da take ciki sai jikinsa ya yi sanyi, tausayinta ya kama shi matu a, ya tuna wayar da suka gama da Didi take sanar dashi cikin ya zo mata da laulayi sosai. Nayla jin bata yi magana ba sai ta ce, "Salima kuka take yi ki auketa, bazan iya aukarta ba. Sanyi nake ji, ki auko duvet a aki ki rufe ni." Omar ya sake jin tausayinta ya ratsa shi, ya bu e bedroom inta ya auko duvet mai nauyi da laushi ya rufa mata, ta ja shi har fuskarta ta rufe tana rawar sanyi. aukar Musliha ya yi da take kuka har lokacin ya kwantar da ita a jikinsa yana rarrashinta. Nayla jin har lokacin Musliha bata yi shiru ba sai ta mi e zaune da yar ta ce, "bani ita Salima, in ban auketa ba bazata daina kuka ba" ta fa a tana dafe kai hawaye na sakkowa daga idanunta. Rauni ya ji ya mamaye masa zuciya, tausayinta da haushin share ta da ya yi kwana biyu ya cika masa zuciya. Ganin tana mi o hannu alamun a bata Musliha sai ya kasa bata, ganin yanayin da take ciki kuma ta kasa share arta da take kuka sai ya sake jin rauni sosai a zuciyarsa, duk fushin da yake da ita ya kau daga zuciyarsa. A tausashe ya ce, "Ki kwanta, zan bata da kaina." Jin muryar Omar ta ago idanunta da suka koma jajaye suka ha a ido, hawaye ya sake sakko mata cikin rauni ta ce, "Tana ta kuka, yunwa take