Sashe 25
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ji babu da i ganin Abbas, amma sakewar da ya yi yana janta da hira sai ta manta ta saki jiki aka sha ruwa tare. Bayan an gama aka zauna ana ta hira cikin zumunci ana tsokanar juna kafin lokacin i sha ya yi a ha u ayi sallah gaba aya har tarawee tare aka yi. Bayan an idar ne Abba ya kalle ta ya ce, Hauwa Ina fatan baki da damuwa ko?. Nayla tayi murmushi ta ce, babu komai Abba, babu abinda yake damuna. Ko a gidan auren na ki babu matsala?. Babu komai Abba. Haka ake so, Allah ya orar da zaman lafiya a tsakani. Ta amsa da amin aka cigaba da hira. Ta shi tayi ta ce, dare yayi har tara tayi, bara na wuce. Abba ya kalle ta ya ce, Zaki iya tafiya ke ka ai ko na ha a ki da driver in yaso ya hawo keke napep ya dawo?. Nayla tayi dariyata ce, zan iya Abba, ai garin da jama a sosai tunda azumi ne. Abbas cikin tsokana ya ce, in fa baza ki iya ba ki fa a, na san ki da shegen tsoro. Dariya ta yi sosai ta ce, Nayla Kaduna kenan Ya Ab, Naylan Kano ai bata da tsoro. Wata daga cikin cousins inta anwar Abbas wacce suke kira Ummimi ta ce, saboda Naylan Kano tana auren Tiger ko?. Kallon ta Nayla tayi kafin Nayla tayi magana ta kuma cewa, Eh mana, matar an daba ai babu ita babu jin tsoro, ke da har gida aka shiga aka kusa kashe ki kuma kika cigaba da zama lafiya, kema ai kin zama jan wuya matar Tiger Sai fara ar fuskar Nayla ta gushe gaba aya saboda rashin jin da in maganar, ta san gaskiya ta fa a amma bata ji da in abinda ta ce ba ko ka an. Abbas ganin ta canja alamun rashin jin da i sai ya kalli Ummimu ya ce, Zama matar an daban ma matsayi ai ne, wata ta zama mana in ta isa, ko ba haka bane Nayla?. Murmushi tayi ganin tayi murmushi sai ya ce, mu je na raka ki mota ki wuce gida dare yana yi. Sallama ta yiwa su Abba tana ji suna yiwa Ummimi fa Nayla kuwa tana shiga mota suka rabu da Abbas bayan sun yi sallama da al awarin zai kawo mata ziyara ta wuce gida. Tana zuwa ofar gidan ta tarar da yaran sa su uku a tsaye suna ta waige-waige kamar masu neman wani abun. Ta tsayar da motar dan yanzu sune suke shigar mata da ita gidan, ko basa nan a waje take barin motar da sun zo zasu shigo su kar i key su shigo da motar gidan. Nayla ta fito daga motar bayan ta auko jakarta da wayarta da snacks in da ta taho dashi daga gidan Abba. Bash ne ya araso wajan ta ya ce, Antyn mu ina kika shiga tun azu muna neman ki? Gaba aya hankalin mu ya tashi, na kira ki sau babu adadi ban same ki ba. Hankalin Damisa ya tashi sai fa a yake yi. Nayla da mamaki ta ce, na je gidan Yayan Mamana ne, a can na yi iftar. Amma antyn mu da sai da kin sanar dashi ko a waya ne, ya tayar da hankalin kowa, ya ce in ba a nemo ki ba akan mu zai wuce. Nayla mamaki ya cika zuciyarta jin wai ya tayar da hankali, kafin ta yi magana Tk ya ce, kuma an kiran ki bakya auka. Nayla ta ce, Ina can cikin an uwa wayar ma tana cikin jakata har yanzu ban auko ba. Tk ya ce, Gaskiya Antyn mu kin aga mana hankali, kin san Boss ya tara ma iya da yawa tsaf wani zai cutar take, don Allah ki daina nisa haka babu sanarwa. Nayla tayi murmushi ta ce, to ku yi ha uri, in sha Allah baza a sake ba. Goje ya ce, dole mu kar i ha urin ki Antyn mu, kawo key Ba musu ta bashi ta ce, Na gode. Daga haka ta shiga cikin gidan tana mamakin meyasa ya tayar da hankalinsa dan bata dawo ba?. Tana shiga falon dashi suka ha a ido, sai ya auke kai kamar bai ganta ba amma ya amsa sallamar da tayi. Nayla ta arasa nesa dashi ta kalle shi ta ce, an sha ruwa lafiya?. Banza ya yi mata bai amsa ba. Da yake ta saba kwana biyu yana amsawa sai ta sake kallonsa taga ya wani basar kamar basarake, daman marocon jallabiyya ce a jikinsa mai zubin al yabba, ya hakimce ya ora afa kan aya sai ya koma tamkar yarima. Nayla ta ce, na biya gida Abba ne a can muka sha ruwa gaba ayan mu shiyasa ban dawo ba. ufule ya kalle ta ya ce, Wani ya damu da zuwan ki da dawowarki ne? Kin ji na ce ina kika je?. Samun kanta ta yi da yin murmushi jin abinda ya ce ta ce, a, sanin baka damu ba shiyasa ma ban fa a maka zan je tana fa a ta bar wajan da sauri kar ya make ta, dan yanayin da yayi magana ya nuna mata kamar ba a daidai yake ba. Tsaki ya yi cike da jin haushi, ya rasa meyasa ya damu da rashin dawowarta da wuri har haka, gaba aya ya bi ya aga hankalinsa sai ka ce Didi ce ta ata. Tsaki ya sake yi ya kalli inda ta bi, ya sauke numfashi tunawa da ta dawo kuma lafiya lau take babu abinda ya same ta. Ido ya lumshe ya bu e ya tuna murmushin da tayi kafin ta bashi amsa. Gashin kansa ya shafa ya sake yin tsaki ya mi e ya bar falon. Nayla kuwa da fara a ta shiga ciki tana tuna abinda Bash ya ce mata akan aga musu hankalin da Omar ya yi, dariya tayi tunawa da ya ce in basu nemo ta ba akan su zai huce. A bayyane ta ce, kenan dai ya damu dani har haka? tayi juyi a kan gado ta girgiza kai ta ce, tunda har ka damu haka wallahi sai na saka ka magantu da kan ka, Allah ya kaimu bayan sallah ta fa a da fara a tana cigaba da murmushi. Sai a wannan ta auko wayarta daga jaka, a lokacin kiran Didi ya shigo ta auka ta saka a kunne Didi ta ce, Ya Allah! Nayla ina kika shiga Ina ta kira bakya auka? Omar gaba aya ya aga min hankali, wai baki dawo ba shi bai san inda kika tafi ba. Wani da i ya sake mamaye zuciyar Nayla ta ce, Didi ina gidan Abba fa, a can na sha ruwa gaba aya har su Mama da an gidan Baba. Amma bai sani ba ko?. Eh bai san zan je ba, daga wajan aiki na wuce. Amma da kin sani koda a waya kin sanar dashi. Didi shine fa ya ce duk inda zan je bai dame shi ba, cewa yayi naje lahira ma ai ba a kansa nake ba, shiyasa na yi tafiyata ta arasa fa a da shagwa a harda turo baki. Didi tayi dariya ta ce, ai kam ya dame shi wallahi, sai cewa ya yi yanzu wani abun yana samun ki zan fara yi masa fa a ina cewa baya kula dake shiyasa ya ke so ya san inda kika tafi. Nayla tayi dariya ta ce, To yanzu ma da na dawo ina fa a masa inda naje ko kallon kirki ban ishe shi ba, da ya gama shan hamshi sai cemin ya yi ya damu da inda naje ne. Didi tayi dariya sosai ta ce, ban ta a ganin an rainin hankali kamar Omar ba, amma zamu kama shi hannu biyu. Nayla ta yi murmushi ta ce, Didi bara na yi wanka na gaji. Daga nan suka yi sallama ta fito ta dafa ruwan zafi a kettel ta shiga dashi ban aki ta yi wanka cikin karsashi da farin ciki. Bayan ta shirya ta fito sanye da hijjabi ta auki ruwa a falo yana zaune a falon yana duba wani littafi. Tv a kunne take, ta tabbatar ba shi ya kunna ba sai dai in tun safe take a kunne dan ta kunna da safe kafin ta fita, kuma da ta dawo bata lura da tv ba. arasowa tayi zata kashe aka fara tallan company sa da ta bayar a tashar. Kallon sa tayi sai ta ga ya ago ido yana kallon tv fuskarsa cike da mamaki mai yawan gaske. Tsayar da idanunsa yayi cak ganin komai ana haskawa harda number wayarsa a cikin numbers in da aka bayar. Waya ya auka ya kira Bash yana auka ya ce, abinda ya furta kenan ya yanke wayar yana sake kallon tv in. Lokacin an gama tallan Nayla ta kashe tv a sanyaye ta san shikenan asirin ta ya tonu, fata take Allah ya raba su lafiya kar ya yi mata wani abun. A hankali ta bar wajan ta shiga kitchen ta ji an bu ofa alamun Bashir ya shigo. Yaushe aka bada talla a wannan tashar? Ya fa a tana nuna tv, Bash ya kalli ya ga tv a kashe take ya sake kallon Boss in nasu da yake kallon sa. Bash ya gane abinda yake nufi hakan ya saka ya ce, Tiger ai tun farkon watan nan aka bayar. Ya zuba masa idanu yana binsa da kallon mamaki ya ce, da izinin wa? Kuma waye ya ce ayi?. Bash ya an ru e saboda idanun Boss in nasu abin tsoro ne ya ce, Da izinin Antyn mu, itace ta ce ayi. Wace haka?. Matar gidan nan ya bashi amsa a hankali. Numfashi ya fesar ya yi masa alama da ya tafi Bash ya juya ya fita a lokacin Nayla ta dawo falon ya juyo yana kallonta. KRB3P013 Arewabooks@nanahaleema11. Nayla ganin ya juyo ya zuba mata idanu sai ta firgita jikinta ya fara rawa saboda tsoron da ya tsirga mata lokaci guda. A hankali take arin oye tsoron amma ta kasa sai da ya bayyana akan fuskarta, takawa ta fara yi da niyar barin wajan ta ji muryarsa ya ce, Cak ta tsaya jin abinda ya ce ta kulle ido ta