Sashe 41
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba ta kashe gas in ta auki tukunyar gaba aya ta tafi da ita. Didi ta bita da kallo ta ce, "in sha Allah komai ya kusa arewa Nayla." KRB3P020 Ranar ma haka suka yini suna hira, Omar tunda ya fita bai dawo ba babu wanda ya damu da ya dawo ko ya zauna. Ranar Nayla ce da kanta ta gyara akinsa, ta canja bedsheet in duk da taga alamun an ta a wanke shi, ta yiwa akin turaren wuta sai hamshi ya ke yi. Tayi mamakin tsaftar sa domin akin tsaf ko kayan nan da maza suke tarawa shi babu, komai neat har da aramin dustbin a gefe da kuma tsintsiyaa ajjiye. Toilet in ma haka yake komai yana mahall insa hatta towel da bathrobe suna ajjiye a inda aka ajjiye su. Bayan ta gama aikin Didi ta dinga tsokanarta ita kuma kunya take ji. Da yamma ta shirya cikin abaya ba a wacce ta haskata matu a ta fito falo ta kalli Didi ta ce, "Didi bara na je wannan store in na baya, akwai abinda zan siyo zan je dashi aiki gobe." Didi ta ce, "ma sha Allah Nayla, wannan kyau haka? Wanda bai sanki ba sai ya sauka bakya jin hausa ai." Dariya tayi sosai ta ce, "kai Didi, kamar wata ke." "Amma dai kin fad awa mijin na ki zaki fita ko?." Nayla ta ce, "ya bani damar zuwa ko ina ai, tunda ya ce naje duk inda nake so kar na sake tambayarsa." Didi ta ce, "haka ne. Sai kin dawo." "Yanzu zan dawo Didi, da afa ma zan je bazan hau mota ba. Ina so ma na bada motar car wash zan kira Bashir ya kai ta" ta fa a tana fita daga falon. Wajan mintina talatin da fitar sai gashi ya shigo ko sallama bai yi ba. Didi ta auka Nayla ce sai da ta juyo ta ganshi ta ce, "A'a sai yanzu?." Ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya yi shiru amma bai daina kallonta ba. Didi da mamaki ta ce, "meye na kallon?." Girgiza kai ya yi ya auke idonsa daga kanta, ya sake juyowa ya ya kalli Didi ya ce, "ki fa awa wannan yarinyar kar ta sake fita koda ofar gidan nan ne." Didi da mamaki ta ce, "wacce yarinya kenan?." Wani irin kallo ya yiwa Didi na kin san wacce make nufi ai, sai ta ce, "To baka fa i suna ba ta ya zan gane ta ne?." Ya ce, "koma dai wacece, ki sanar da ita kar na sake ganin ta fita." Didi ta ce, "Wai Nayla ka ke nufi? To akan me zaka hana ta fita?." A lokacin Nayla ta bu ofar ta shigo tana cewa, "Didi har na dawo, shiyasa na tafi key in gate saboda kar na tashe ki bu e gate." Kallon ta ya yi ya ce, "ke! Kar na sake ganin ko da wasa kin fita daga gidan nan." Nayla ta bishi da kallon mamaki kafin tayi magana Didi ta ce, "ba kai ka ce ta dinga zuwa duk inda zata je ba?." "Ai ban ce ta dinga yawo a kan titi ba!." "To in bata yi yawo a kan titi ba a kan me zata yi yawo? Wai me take damunka ne Omar don Allah?. Kai ka bata damar fita kace ta fita duk lokacin da take so, dan ta fita sai ya zama fitina kenan?." Nayla a sanyaye ta ce, "kai ka ce na je ko ina babu ruwan ka." Wara idanu ya yi akanta kamar tayi masa allura ya ce, "yi min shiru a wajan nan!." Didi ta ce, "ba gaskiya ta fa a ba? Ba haka ka ce in ba?." Omar a fusace ya ce, "To yanzu na canja, na canja yanzu!. Kuma dole abi abinda na ce in ba haka ba baza a ga daidai ba wallahi!. Kar na sake ganin ta fita" ya juyo ya kalle ta ya ce, "kar na sake gani kin fita, na soke maganar da nayi a baya, duk inda zaki je ki tabbatar kin sanar dani, in ba haka ba ranki in ya kai guda dubu aya bayan aya sai na ata su wallahi." Didi ta ce, "Ikon Allah, me ya kawo wannan canjin kuma?." aramin tsaki ya yi ya ce, "oho kuma" Ya kalli Nayla da idanunsa bai ce komai ba kawai ya fita. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta ce, "ni dai bana ta a yi masa daidai a rayuwa." Didi ta ce, "me ya faru a wajan ne?." "Babu fa Didi, kawai yana so ya dinga yi min fa a ne shine kawai." ofar aka sake yi duk zaton su shine ya dawo sai suka ga Tk da leda a hannunsa, ya gaishe su ya ce, "gashi in ji Tiger." Didi ta kalle shi ta ce, "me ya atawa Damisar na ku rai haka? Ya shigo yana ta bala'i shi ka ai." Tk yayi ar dariya ya ce, "Babbar Yaya ai wani ne yanzu ya riga Antynmu arasowa gidan nan, ya zo ya samu Damisa a tsaye yake fa a masa shi dai yana sonta. Ana haka sai gata tana tahowa, shine ran maza ya aci. In kinga fa an da yake yi yanzu da ya fita sai ya baki tsoro" ya arashe fa a yana dariya. Didi ta murmusa ta ce, "fushi yake yi mai hujja." Tk dariya ya yi ya fita bai sake magana ba. Ita dai Nayla tana tsaye har lokacin bata zauna ba, Didi ta jawo hannunta ta zauna ta ce, "Ke ashe kasuwa ki ka yi shiyasa ran mijin naki ya aci har ya soke fitar ki ko na." Nayla a sanyaye ta ce, "wallahi Didi ban san shi ba." Didi ta ce, "haba meye na wallahi Nayla?. Kawai ya ganki yaji kin yi masa bai auka kina da aure ba shine kawai." Nayla ta ce, "kuma Didi ai bana saka kaya half niked ko?." Didi ta ce, "bakya sakawa Nayla, kina shigar mutunci irin ta masu mutunci." "Da na sani ma ban fita ba, abinda na je nema ma ban samu ba." Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Didi ta ce, "na ce miki Omar kishin ki yake yi kin ce ba haka ba, yanzu meye wannan in ba kishi ba?." Nayla ta ago ta ta e baki ta ce, "yadda baya sona baya so wani ma ya so ni, shine kawai dalilinsa." Didi ta yi murmushi ta ce, "na gaji da musu dake, mu je a hakan." Nayla ta ce, "Amma Didi ya ce kar na sake fita, kuma zan je aiki gobe." "Kar ki damu, ki jira ya shigo zuwa dare sai ki sanar dashi, yanzu a dokin fushin ya ke." Nayla ta girgiza kai suka cigaba da hira da Didi bata bari wani zancen kishi ya yi tasiri a ranta ba. Yau ma kamar jiya Didi ta yiwa Nayla dole na zuwa akin Omar, babu yadda bata yi ba amma Didi ta ce sam sai ta tafi, kamar zata yi kuka saboda ciwon da kanta yake yi mata, amma Didi ta ce ta sha magani in ta je can tayi bacci kan zai daina ciwo. Ita tsoro ma take ji kar ta je ya yi mata wani abun tunda ransa a ace yake kamar jiya. A hankali ta tura ofar ta shiga da sallama. Yana daga zaune a gefen gadon cikin shiga irin ta jiya sai dai yau farar singlet ce a jikinsa. Ita tsoron kallonsa haka take yi, jikinsa kwarjini yake mata bata iya tsayawa ta kalle shi shiyasa kanta yake a sunkuye. Tunda ya amsa a ciki bai ce komai ba ita kuma bata araso ba, akyar dai ta iya daurewa ta motsa amma ta kasa arasawa wajan gadon saboda yau yana zaune a kai ba kamar jiya ba da yake kan stool ba, Ita kuma ta sha maganin ciwon kai bacci take so tayi, ciwon kan ya dame ta matu Shi kam yana kallonta bai ce komai ba, tana shigowa abinda ya fara zuwa ransa wanda ya ce yana sonta. Sai ya ji wani irin abu ya daki zuciyarsa, idanunsa har ruwa suka tara saboda yadda ya ji bugun bazatar da zuciyarsa ta yi. Yana mamaki kansa yana so ya san dalilin da ya saka ya damu har haka, tun a jiya yake so ya gano dalilin me yasa ya damu da an yi posting afarta ya rasa, ga yau ma ta faru ya rasa gane abinda yake ji. Nayla arfin hali tayi ta arasa gefen gadon ta zauna a gefen da ta kwanta jiya. Sai ya zama tana daya angarne shima yana aya angaren ko wanne su a zaune yake. A hankali Nayla ta zame ta kwanta idanunta ma kawo hawaye saboda ciwon kan ya dame ta, ga hasken akin ya yi mata yawa. Ta juya masa baya hakan ya saka ya juyo ya kalleta ya ganta sanye da hijjabi kamar dai jiya. Ya jima a zaune ita kuma ta kasa baccin saboda ciwo da kuma hasken akin. Tashi zaune tayi, ciwon kai ya saka ta zare hijajbin ta ajjiye ta dafe kai da duka hananyen ta biyu tana hawaye. Kallon ta ya yi kamar zai yi magana sai ya fasa, sai ya ga ta mi e ta kashe hasken ta dawo ta kwanta a takure. Yana nan dai bai motsa ba babu kuma abinda yake yi yana zaune ne kawai. Sautin kukan ta yake ji ka an-ka an tana kiran wayyo kanta. Kamar ya share ta sai ya ga ta sake mi ewa zaune ta dafe kai. "Lafiya?" Ya furta yana kallon ta. Nayla bata auka zai yi magana ba, amma jin maganarsa sai ta ji da i a ranta cikin muryar kuka ta ce, "Kaina ne yake ciwo sosai" ta fa a muryar na rawa. Tausayi ta bashi musamman yadda muryarta take rawa, ya tuna lokacin da bashi da lafiya yadda ta dinga yi masa cikin tausayawa, hakan ya saka ya ce, "kin sha magani?." "na sha, amma ya i ya daina" ta fa a a raunane cikin zafin ciwon kan. "Sannu" ya sake furtawa can asan ma oahi. Bai sake magana ba bai kuma motsa ba, Nayla tana zaune itama amma ta ji dadi zuciyarta