← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 205

Sashe 72

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zata saka mata ba. Sai kayan ban aki da ta sake siya, towels da sababbin bathrobes, sai kayan ado na falo da kitchen. Aka gyara gidan har aka gama gyaran Omar baya nan suka yi turaren wuta suka koma gida. Bayan sallar i'sha Mama ta tarar da Nayla ta shirya cikin abaya ba a mai kyau da tsantsi, tayi mata kyau dan gyaran jikin da aka yi mata ya kar eta. Mama ta kalle ta ta ce, "To driver zai mayar dake, Abba ya ce kar wanda ya yi miki rakiya daman ai ke ka ai kika zo. Nasiha an yi miki tun ba yanzu ba na san duk kin ri e, abinda ana ce miki kawai ki bar komai ya wuce kamar baki dawo gida kin zauna ba, ki ajjiye komai ki yi facing zaman aurenki. Sai kin yi ha uri, duk soyayyar film ko ta littafi da ki ke tunani ba ita zaki gani ba, za ki ga daidai misali wacce ta isheki ki fa awa duniya mijinki yana sonki. Sannan kin zauna dashi kin san halinsa, sai ki yi ha uri akan wasu abubuwan dan aure an ha uri ne Nayla. Allah ya baku zaman lafiya ya orar da zaman ku har mutuwa, Allah ya sa ki gaji iyayen ki." Nayla ta amsa da amin. Ummimi da Mama suka rakata har mota, a lokacin Abbas yake ajjiye motarsa a wajan. Mama ta ce, "Abbas anwarka zata koma gidan mijinta, ayi mata nasiha." Ya yi murmushi ya ce, "ban da rashin ji." Dariya suka yi gaba aya ya shiga ciki ita kuma ta shiga motar suka tafi. ofar gidan aka ajjiye motar ta fita ta bashi ku in napep sannan ta ce ya kai motar gidan Hajja ya ajjiye. Ya amsa mata da to ita kuma ta bu e gate in gidan ta shiga. Sabuwar motarsa tana ajjiye a wajan, Nayla ta kalla ta yi murmushi tana mamakin motar dan ita dai ta san tana da tsada sosai, ta girgiza kai sannan ta wuce zuwa cikin falon. hamshi falon yake yi sosai, ta yi murmushi ta wuce ciki ta ajjiye jakarta da laptop in da take hannunta. akin ta kalla komai yana nan sai dai an canja komai hatta bedsheet Salma ta canja mata. Ajiyar zuciya tayi ta kalli agogo ta ga tara na dare ta kusa sai ta rasa abinda zata yi. Frame in da Salma ta ajiiye mata ta gani ta bu e, hoton Tiger ne babba mai shegen kyau, ta bu e baki ha oranta sun fito waje. Ajjiyewa tayi domin a akinsa take son kafawa. Zama tayi ta kira Didi a waya tana bata labarin ta dawo, Didi ta dinga murna da addu'a Nayla na ta murmushi. Kitchen ta shiga tana sake kallonsa kamar wacce ta shekara bata nan, yana nan yadda yake dan daman ta san babu abinda zai ta a a gidan. Tunani take yi ta yi girki ko kuma ta yale girkin dare ya yi?. Noodles ta aukota ta kalli bayanta taga kayan miya, irish potatoes da plantain a ajjiye, ta san dai aikin Salma ne ita bata bar komai ba, koda ta bari ai ya ci ace ya lalace. Nan da nan ta dafata ta sai hamshi take yi ta samu flaks mai kyau ta zuba yadda baza ta huce da wuri ba. Tana gamawa ta wanke hannu kenan ta ji motsin shigowa, ta fito ta tsaya cak tana kallonsa yana shigowa yana amsa waya. Yadda yake maganar ta gane da Didi yake waya kafin ta ga ya kashe wayar. Kallon falon ya yi ya ce, "waye ya shigo gidan nan?." Murmushi tayi da alama Didi bata fa a masa ba kenan. Fitowa tayi daga inda take ta tako ta ce, "Sannu da zuwa." Cak ya tsaya ya ago idanunsa ya kalle ta suka ha a ido tayi murmushi ta saukar da kai asa. Zuba mata ido ya yi na wani lokaci kafin ya janye idanunsa dan shi a tunaninsa gizo take yi masa. Nayla jin shiru sai ta kalle shi ta ce, "YaMar!." Lumshe ido ta ga ya yi ya bu e, ya kalli inda take ya tsayar da idonsa yam akanta yana so ya tabbatar itace ko kuwa gizo take yi masa. Nayla ganin kallon da yake mata ya yi yawa ta sauke ido asa tana kifta idanu da turo baki gaba. Ajiyar zuciya ta ji ya yi amma bai ce komai ba. Waya ta ga ya saka a kunne yana cewa, "na fa a miki gidan nan akwai aljanu, yanzu ba muryarta ka ai nake ji ba" ya jiyo yana kallon Nayla ya ce, "ita nake gani a gabana a tsaye, kuma dan rashin kunya irin na aljani ko tsorona ma bai ji ba kallona ma take yi." Nayla ta yale da dariya ganin da gaske bai auka ita in bace ya auka aljana, ganin yadda take dariya ya saka bai ji ma abinda Didi ta ce ba. Sai da ta kira sunansa da arfi sannan ya ce, "ina jinki." Shiru ta ga ya yi sannan ya ce, "wai da gaske ki ke?." Kashe wayar ta ga ya yi ya sake zuba mata ido kamar mai son tantance wani abun. Nayla da ta gama dariya cikin sanyin murya ta ce, "in baka banbance ni in ba ce ka auka kawai aljanar ce" ta fa a tana murmushi murya a sanyaye. KRB3P040 Wani irin nisha i da da i Omar ya ji yana mamaye masa zuciyarsa, nan da nan farin ciki ya bayyana har a kan fuskarsa, ya bita da kallo yana ji kamar ya rungume ta amma baya so ta ga ya za e da yawa ko ta yi masa kalla an iska. Murmushi ya yi mai bayyana farin cikin da yake ciki, ya an shafa kansa ka an yana girgiza kai ya ce, "amma an shammace ni." Nayla ta yi murmushi itama amma bata ce komai ba. Omar ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya fasa yana murmushi, ya sake kallonta cikin sanyin murya ya ce, "Yaushe haka?." Nayla taji farin ciki na mamaye mata zuciya, muryar da ya yi amfani da ita wajan yi mata magana bai ta a yi mata magana da ita ba. Ta an kawar da kai ta ce, " azu na dawo. Har dinner na shirya maka." Omar ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya fasa bai ce komai ba, yana sosa goshinsa kamar yadda ya saba. Nayla a sanyaye ta ke saboda sanin halinsa, amma tana so ta zama wayayyiyar amarya shiyasa take dakewa tunda ba ba onta bane. Ta koma inda abincin yake ta zuba noodle in a bowl ta kalle shi ta ce, "ka zauna." Ya kasa tantance adadin farin cikin da yake ji a zuciyarsa hakan ya saka shi ya zauna in kamar yadda ta ce. A hankali ta tako ta zauna ta mi a masa ta ce, "bismillah." Bai kar a ba sai kallon abinda ta mi o masa in ya yi, ya kalli hannunta da ya sha jan henna akan fatar hannun. Nayla bata yi magana ba shi kuma bai kar a ba sai kallon hannunta da yake yi. A kusa dashi ta ajjiye bata ce komai ba, ta zauna kawai tana kallon wani wajan daban tana jin kanta kamar an aure ta da igiya. Dauriya take yi kawai, amma nauyi da kunyarsa take ji sosai, tana so ta bar komai ya wuce kamar yadda Mama ta ce. Omar ikon Allah yake kallo, gata dai a kusa dashi, amma kewarta yake ji tana shiga cikin zuciyarsa, ya rasa abinda zai yi da zai ji ya gamsu da ita in ce a kusa dashi. Hannunsa ta ji akan hannunta, tayi saurin juyowa saboda abinda ta ji ya soki zuciyarta har fatar hannunta da ya ora tasa sai da ta ji. Shima kansa ya ji wannan yanayi, amma yana so ya tabbatar da ita in ce ko dai ba ita bace. "da gaske ke ce?" Ya fa a a hankali yana binta da kallon tsakiyar ido cikin wani irin yanayi. Nayla ta yi murmushi, duk da abinda take ji a jikinta saboda ha uwar hannunsu waje aya a karo na farko ta daure ta ce, "Ni ce." Sai ya janye hannunsa ya zuba mata ido ya sake yin shiru bai ce komai ba. Ita kuma kallon ne yake takura ta, sai ta kasa sakewa gaba aya ta sunkuyar da kai. Omar ya kasa auke ido daga kallonta, yana kallon ta girmama girman ikon Allah da hukuncinsa akan bawa a duk lokacin da ya so. Wai shi ne yake ji kamar ya ha iye Nayla saboda son da yake mata, shine yake jin kewar Nayla kamar ya ha a jikinsa da nata haka yake ji. Ya kasa magana kuma bai daina kallonta ba, sai da ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce "Komai ya wuce ko bai wuce ba?." Nayla sai ta yi nufin tsokanarsa da jan aji ta ce, "bai wuce ba, na zo ne kawai na kar i takardata." Murmushi ta ga ya yi bai ce komai ba bai kuma auki abincin ba, sai kuma ta ga ya tashi ya shiga aki. Nayla ta bishi da kallo ta ce, "Allah ya ara min, gashi nan ai zan jawowa kaina." Kallon indomie in ta yi ta auke ta ajjiye akan table ta tashi ta shiga aki. Zuciyarta duk babu da i ta canja kaya zuwa doguwar riga ta bacci ta dawo aramin falon kenan ya shigo. Mi a mata takardar ya yi ya ce, "gashi." Gaban Nayla ya yanke ya fa i, ta yi saurin kallonsa ta ga babu alamun walwala ko wasa a tare dashi. Murmushin da ta gani azu ya gushe gaba aya ya dawo asalin Omar in da ta sani a baya. Idanunta a waje take kallonsa saboda tsoro ta kasa daina kallon idanunsa. Murya na rawa ta ce, "meye wannan in?." Omar ya dake cikin muryarsa ta ko yaushe a kausashe ya ce, "abinda ki ka nema, na fa a miki daman bazan miki dole ba, in na tabbatar baki son zama dani zan iya abinda ki ke so, i." Nayla ta kasa kar ar takardar da yake mi o mata, hannunta sai rawa yake yi ta i ta
Chapter 72 · 0% Book details