Sashe 154
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ko? To ki yi aikin lada Jidda!." Nayla ta an juya kai ta ce, "Rouhii Didi fa tana tare damu, kuma lokacin sallah ya kusa." "Ashiq abinda nake so kenan, baza ki yi min ba?." "Ina so Rouhii, amma....." "Shiiii! Ki yi shiru." Shirun ta yi tana ji ya fara yamutsa ta ya fara kissing inta a haukace. Kukan Marmerh suka ji, Nayla tayi saurin yin baya sai ga Didi ta bu ofar ta fito daga akin. Nayla ta yi wiki-wiki kamar munafuka shi kansa jikinsa ya saki ya lumshe ido yana sauke numfashi, bai kalli Didi ba ya rufe ido yana shafa kansa a hankali. Didi ta araso tana kallon su, ganin yanyinsu sai ta ji wani iri, duk da bata gansu a tare manne da juna ba amma sai ta ga kamar akwai wani abun da ya saka suka yi mata shiru. Nayla saboda ta katse shirun sai ta ce, "Didi kin sha bacci, ga abinci ki ci an kusa sallar azahar." Didi ta ce, "Bacci nayi cike da mafarki Nayla, ki sake yi min godiya a wajan mijinki." Nayla ta yi murmushi Marmerh tana mi awa Omar hannu tana kiran Daddy kamar yadda Didi ta koyar da ita ce masa Daddy. Jin muryar abar aunarsa ya saka ya bu e ido, ya kalle ta ya yi murmushin arfin hali ya mi a mata hannu Didi ta bashi ita, Nayla ta ce, "Bara na kawo mana yaji, wannan shinkafar ta su babu maggi" ta fa a tana tashi ta shiga ciki ba jimawa ta dawo. Tana zama Didi ta ce, "Nayla me yake damun Omar ne? Naga ya canja." Nayla ta kalli Omar da ya kallon ta, ta kalli Didi ta ce, "Didi kin fa san halin kayan ki, babu abinda yake damun shi." Murmushi tayi kawai bata ce komai ba. Abinci suka fara ci ita da Didi kafin ya ce, "Mun yi waya da mijinki, na fa a masa inda mu ke ya ce da ar tazara da inda yake amma zai zo." Didi ta yi murmushi ta ce, "ka ce ku ne ki ka tsara tafiyar nan a haka?." Omar ya ce, "Jidda ce." Murmushi Didi ta yi, Nayla ta kalle shi ta ce, "baza ka ci abincin ba?." Ya bita da mayen kallo ya ce, "Kin bani ne?." Nayla ta ce, "baka ce ba ai." Mi a masa ta yi ya kar a yana binta da ido, ta kawar da kai kamar bata gani ba ta koma suna cin abinci da Didi tana bata labarin yadda aka tsara tafiyar. A tare suka gama ya kalli Nayla ya ce, " auko min abinda na baki." Ba musu ta tashi ta kawo masa, ku i ne na asar da suka canja tun a nigeria, ya bawa Didi ya ce, "Didi duk abinda zaki siya ki yi amfani dashi." Bata kar a ba ya ora mata a kan ciyarta ya sake bata wani ya ce, "ga na marmerh, in kuma ki ka ci ku inta Allah yana kallonki." Sai ya bata dariya ta ce, "Omar..!." Ya katse ta a kausashe ya ce, "Didi, ni na gaji da kiran sunan nan nawa da ki ke yi, ko yaushe ki ce Omar kamar ke kika ra a min sunan?." Murmushi ta yi dan ta kasa magana. A tare suka fita zuwa masallaci don yin sallar azahar, bayan sun idar suka dawo AbdilHamid ya zo suka dinga hira duk da rabi godiya take sakawa ya yiwa Omar. Omar ya ce, "To ka dawo nan da zama mana, akwai aki ai sai ku zauna tare." "Ai na riga da na biya Omar, kar ka damu." "Har na makka?." "Har shi Omar." "To ai shikenan." Omar ya fa a dan shi gaskiya yana so ya dawo in ko dan ya dauke hankalin Didi shi kuma ya samu sakewa da matarsa yadda yake so Nayla ce tayi musu booking shiga ziyara suka samu permit na shiga bayan sallar i'sha. Anan suke zaune har suka je la'asar suka dawo, da suka je sallar magriba ne Nayla ta ce baza su dawo ba sai sun fito daga ziyara. Didi sabon kuka ta fara Nayla na rarrashi a haka suka kammala suka dawo gida. Nayla ta so su fita yawo amma ya i ya ce ta gaji.