Sashe 165
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"ki yi shiru, sirikina yana waya." Didi tayi dariya shima haka sannan ya auka. Ba su jima suna wayar ba ya kashe ya kalli Didi ya ce, "Abiy ya ce naje yana nema, zan je na dawo." Didi tana ta dariya tana tsokanarsa ya yi dariya ya fita daga gidan. Kamar yadda Abiy ya fa awa Omar location na gidan ya je, ya shiga har cikin gidan a lokacin an idar da sallar i'sha. A falo ya samu Abiy suka gaisa yana tambayarsa Musliha ya amsa sannan Abiy ya ce, "Omar Senator Sagir ne yazo min da wata magana, yazo azu ya same ni akan maganar arsa Narma." Omar bai ce komai ba Abiy ya ce, "Ya tabbatar min da arsa tana kwance a gadon asibiti saboda son da take maka." Nan ma Omar bai tanka ba yana jiran Abiy ya gama magana sannan ya furta abinda yake bakinsa. Abiy ya ce, "Yazo yana neman alfarmata akan na ro eka ka kar i auren Narma, saboda son da take maka tana gab da rasa lafiyarta. Shine na kira ka na ji ta bakinka, zaka iya aurenta ko dan ceto rayuwarta Omar?." Omar ya sauke numfashic a hankali ya ce, "Abiy yaje har office ya same ni azu, kuma na fa a masa ni bani da ra'ayi, nace masa bana so kuma bazan yi ba." "Amma meyasa baka so in? Naga a dai kai ma ka so ta ko? Zaka iya yin ha uri a yanzun ma ka kar eta ko dan lafiyarta." Omar kai tsaye ya ce, "Abiy in nace ban ta a sonta ba ban yi arya ba wallahi, ta shigo rayuwata ne saboda naje gidansu a fa a min maganar da Senator ya fa a min ya zama silar canjawar rayuwata. Ta shigo rayuwata ne saboda ta zamar silar da zan tashi daga can na dawo nan, kuma amfaninta ya are a wajena da rayuwata gaba aya." "Haka ne Omar, daman komai yana da sila a rayuwa, ita ta kasance silar canjawar rayuwarka. Amma ko dan saboda ta silarta canji yazo a rayuwarka meyasa baza ka amince ka aureta ba? Tana tsananin sonka, yazu haka tana asibiti a kwance saboda ta ji mahifinta yana cewa ka ce baza ka aureta ba. Kuma lokacin da iyayenta suka yi maka wannan abun ita meye laifinta? Duk da haka ta cigaba da nuna maka so bata daina ba, har tayi aure ta fito baka bar zuciyarta ba, Allah ka ai ya san abinda take ji akan ka. Omar zaka iya kar ar aurenta ko dan matsayin silar canjin ka da take dashi, zaka iya kar arta ko dan son da ta ke maka, koda kai baka sonta zaka iya zama da ita." P102 Omar bai ago ya ha a ido da Abiy ba saboda nauyinsa yake ji sosai, amma da wani ne yake masa wannan maganar ba Abiy ba da mai raba su Allah. Omar ya ce, "Abiy wallahi bani da ra'ayin ara aure a rayuwata gaba aya, ko ina da ra'ayin auren nan gaba bata daga cikin matan da zan iya aura. Mahaifinta ya hanani aurenta a lokacin baya saboda ban kai matsayin ya bani aurenta ba, a yanzu kuma yana so na aure ta saboda na kai wani mataki wanda bai yi tunanin zan kai ba. Kai tsaye zance ba saboda Allah ya bani ita ba, ya bani ita ne saboda wani buri a zuciyarsa." Abiy ya murmusa ya ce, "Haka ne Omar. Amma abinda nake so ka duba ita yarinyar bata da laifi tun asali, ko dan saboda son da take maka ya kamata ka yi wani abun. Tun farko ita bata ika ba, bata nuna maka iyayya ba, ko bayan abinda iyayenta suka yi maka bata guje ka ba, itama sai kayi mata adalci ka amince da ita. Ba mahaifinta zaka duba ba, ita zaka duba, mahaifinta shine yayi maka laifi ba itace tayi maka ba." Omar ya sauke numfashi ya ce, "Abiy kamar yadda na fa a maka bani da ra'ayin ara aure a yanzu ko nan gaba a rayuwata gaba aya. Kuma ita kawai ta zama sila ne na canjawata, har gobe ina tunawa da ita kuma ina yi mata addu'a da ta zama silar canji, dan kome na zama bazan manta da mafari ba, amma batun zan aureta ko ina sonta bai tashi ba Abiy. Shiyasa na fa awa mahaifinta gaskiya, dan ni ban iya oye abu a raina ba." Abiy yana sauraron yadda yake magana cikin girmamawa, ya san kuma zallar gskiyarsa yake fa a masa, yana tausar sane saboda halin da akace Narma tana ciki, shiyasa yake maimaita masa ya aure ta. Abiy ya ce, "Duk da haka ka yi tunani Omar, wata ila zaka iya bata gurbi a rayuwarka." Omar ya yi shiru bai ce komai ba, in ba dan Abiy in bane da ashar zai yi wallahi, baya son yana tafiya ana dawo dashi baya, ya ce baya so to a bar maganar mana lallai sai an yi masa dole. Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Abiy ba musu nayi maka ba, amma bani da bu atar tunani. Bani da bu atar ara aure gaba aya a rayuwata balle na saka ran zan aureta, In har na amince da auren ta bai kai zuciya ba, kuma na cutar da kaina na cutar da matata. Sannan mahaifinta ya samu abinda yake so, ya i ni a lokacin da yake amfani da rayuwata, yaso ni a lokacin da rayuwata zata yi masa amfani. Abiy ba kowa ne irin ka ba a duniya, ba kowa ne zai auki arsa ya bawa mutum kamar ni ba." Abiy ya yi murmushi ya ce, "in baka san me zai faru a rayuwar mutum ta gobe ba baka yanke masa hukunci Omar, dani da kai da kowa babu wanda ya san me zai faru gobe, ba ma gobe ba, fitar ka daga gidan nan babu wanda ya san mai zai faru sai Allah ka ai. Amma mutane sai su dinga yiwa mutum hisabi bayan basu san gaibu ba. Allah ya kyauta, yasa mu dace. Tunda baka so shikenan, zan sanar dasu in sha Allah." "Na gode Abiy. Don Allah a sanar dashi kar su sake takura min, a yale ni, tunda nace bana so a rabu dani. Su yiwa arsu addu'a Allah ya bata lafiya, amma batun aurena a daina kawo shi." Abiy ya ce, "To Omar zan fa a masa sa onka in sha Allah." Omar bai jima ba suka yi sallama ya tafi yana girmama arfin hali irin na Sen. Omar da ya koma bai tarar da Didi ba daman ya san ta tafi, ya shiga aki ya yi wanka ya canja kaya ya tsaya a jikin window yana kallon layin unguwar ta su, so silent as usual. Tunani ya tafi yi, tabbas maganar Didi gaskiya ce, Nayla ta sadaukar masa da komai na rayuwarta, haka zalika Abiy ya yi matu ari da ya iya bashi aurenta, duk da abin ya faru ne a cikin wani yanayi amma tabbas ya yi ari. Abinda ya faru tsakaninsa da Sanata a office yake tunawa yana mamaki, wato yanzu ne ya zama mutum yake ji zai iya bashi arsa tunda ya kai wani mataki a rayuwarsa, shiyasa ya manta da batun asiri ya yi mata take sonsa har yaje ya samu Abiy akan maganar. Jinjina arfin halin Sanata yake yi, wato ya same shi kai tsaye yace bazai yi ba shine ya zaga wajan Abiy. Bu ofar aka yi aka katse masa tunani, ya juyo ya kalli Nayla da ta shigo cikin pyjamas green riga da wando masu dogon hannu da high neck. Hannunta ri e da Musliha ta araso ta ce, "Musliha ta zo ta cewa Daddy good night." Takowa ya yi a hankali yazo yana kallon fuskar Musliha da take bacci ya sumbaceta a goshi ya ce, "Ki yi bacci lafiya Yayata" ya fa a yana shafa fuskarta cikin auna da soyayyarta. Nayla bata ce komai ba, ta gyara Musliha a hannunta ta juya zata fita ya ri o hannunta ta tsaya bata juyo ba. Shiru ya yi bai ce komai ba itama bata juyo ba, ya ri e mata hannu shi bai saki ta tafi ba kuma bai ce mata komai ba. Sai da yazo gab da ita, ya tsaya a bayanta sannan ya ce, "Babar Musliha baza ta ce min good night in ba?." Nayla bata juyo ba ta ce, "Fushi ake yi da ita ai, ta bada ha uri an i a ha ura shiyasa ta kama kanta." Zagayowa yayi ya kar i Musliha a hannunta ya kwantar da ita a kan gado, ya dawo kusa da ita ya ago fuskarta yana kallon ta ya ce, "Waye zai iya fushi dake Jidda? Ni?" Ya fa a yana nuna kansa. Nayla cikin shagwa ar da take saka shi narkewa a cikin shau inta ta ce, "To tun yaushe nake baka ha uri ka i ka ha ura, ko magana baka yi min ba sai dai ka yiwa arka, in ba fushi ka ke yi ba me ka ke yi?." "Kishi nake yi, kishinki da kishin ata nake yi ba fushi ba. Jidda kin san me naji kuwa? Kin san yadda ki ke da mahimamci a tare dani? Kin san adadin mutane da suka kira ni saboda sun ga hoton nan?. Zuciyata zafi ta dinga yi, ji nake yi kamar na dinga dukan kaina har sai na ji a jikina hakan ya yi min. Ina tsananin kishinki, na fa a miki a akan kishinki zan tashi nigeria gaba aya." Nayla ta ce, "Amma na fa a maka kuskure ne, kuma ba za a sake aikatawa ba ba sai ya wuce ba? Tunda ka san ban ta a aikatawa ba sai ka yi min uzuri ko?." Ya ri e fuskarta da hannayensa duka biyun, ya zura hannunsa a gefen kumatunta har yana ta o kunnenta ya ce, "kin fa a, amma ko yanzu hotunan basu daina yawo a duniya ba. Ana ta yabon kyaun matata da surarta, ba mutum aya ba, kuma ba biyu ba, to ya ki ke so nayi? Dariya ki ke so na dinga yi bayan wasu banzaye suna kallon ki suna jin da i?." Nayla a sanyaye ta ce, "Shiyasa na baka