Sashe 20
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mata fatar jikinta. yar ta iya samu tayi wanka ta canja kaya zuwa doguwar riga ta shan iska wacce take a tattare da roba a irji, ta saka hula ta kwanta akan kujera tana mayar da numfashi saboda zazza i ne a jikinta sosai. Bata tunanin zata iya koda dafa tea saboda yadda take bata jin da i ko ka Sallamarsa ta ji kamar ko yaushe a ciki bata fito sosai ba, ta ago ta amsa ya araso har inda take ya ajjiye key in motarta da tk ya bashi akan table in da yake kusa da ita. Ha a ido suka yi ta auke kai ya tsaya kafin yana kallon ta ya ce, "shi wannan in waye?." Babu zato babu tsammani taji maganarsa, hakan ya saka ta ago ta kalle shi ba tare da tayi tunanin ita yake kallo ba. Janye idonta tayi ta mi e zaune gabanta yana fa uwa matu a ta ce, "Colleague ina ne." Kamar bai ji me ta ce ba, yayi shiru yana zagawa da idanunsa ko ina na jikinta. Nayla ta diririrce ganin kallon da yake yi mata, murya na rawa ta ce, "Abokin aikina ne, bani da lafiya bazan iya driving ba shine ya kawo ni sai cleaner ya dawo da motar." "Shi cleaner in bazai kawo ki ba sai abokin aikin ki?." Da sauri ta sake kallon sa jin abinda ya sake fa a, fuskar nan ta sa tana aure matu a sannan babu a alamun wasa a tare dashi. Nayla gabanta fa uwa yake yi dan bai ta a tsayawa sun yi doguwar magana shida ita haka ba, ta sunkuyar da kai ta ce, "da a can zan bar motar sai daga baya aka yi tunanin cleaner ya kawo." Shiru ya yi yana kallonta ko motsin kirki baya yi, ya kafa mata ido kawai yana kallo ba tare da ya san asalin abinda yake nu usar zuciyarsa ba. Wanda ya ajjiyeta a motar kawai yake gani a idonsa, bazai ce ga abinda yake ji ba amma ya san zuciyarsa tayi nauyi sosai. Nayla da taji shiru ta auka ya fita, hakan ya saka ta kalli inda yake suka sake ha a ido tayi saurin auke kai jikinta har tawa yake yi. on Didi ya ajjiye mata ya ce, "Kar na kuma ganin hakan!" Ya fa a cikin kakkausar murya. Nayla saboda tsoro bai barta ta iya bashi amsa ba hakan ya saka shi ya ce, "sa on Didi" abinda ya ce kenan ya bar wajan. Nayla ta yi sauke ajiyar zuciya mai tsaho ta ce, "na ku uta!. Iko Allah to shi wannan mutum me ya ke nufi ne? Kishi yake yi ko me oho?." Bu e abinda ya ajjiye mata take yi tana cewa, "nima ba a son raina hakan ya faru ba ai, babu yadda zan yi ne matan office in duk sun tafi saboda matan aure ne ana sauri aje ayi girki." "Wow!" Ta furta ganin pack mai kyau ta sako mata awara manya-manya wacce taji sauce har da mayonnise da aka zuba mata. Nayla tayi murmushi ta ce, "Wayyo Allah! na huta cin komai in an sha ruwa." Sai kuma tayi murmushi ta ajjiye pack in ta ri e ha a ta ce, "wai yanzu kenan kishina yake yi?..." sai ta girgiza kai ta ce, "A'a dai Nayla, ta ya zai yi kishin ki bayan ba sonki yake yi ba?. To amma meyasa ya nuna ya ji haushi har ya ce kar ya sake gani?." Sai ta sake yin aramar dariya ta ce, "Dole Twinny ta ji labari, addu'ar da suke yi min Allah yana kar Tana zaune tana wannan tunanin aka yi kira ko addu'ar kusa da shan ruwa bata samu ba. Ruwa ta auko ta sha ta auki awarar guda aya ta ci tana lumshe ido saboda tayi mata da i. Sallah ta tayar bayan ta idar ta shiga kitchen ta ha a tea ta dawo tana sha tanacin awarar da tayi mata masifar da i. Tana gamawa ta sha paracetamol ta zauna tana hutawa. Gaba aya abinda ya faru ya i fita daga kanta, ta lura kwana biyu yana iya yi mata magana ko dan ya saba da ganin ta ne dai oho. Aiki take so tayi ta turawa ogan su amma baza ta iya ba saboda ciwon kai, tana nan zaune a wajan har aka yi i'sha ta tashi tayi sallah aka tayar da sallar tarawee. Bayan an idar da hijjabin jikinta ta fito babban falon dan ta auki alkur'anin ta da ta bari a kan table. Shigowarsa ta gani ta amsa sallamar da yake yi kamar baya so, wucewa take niyar yi ya ce, "tsaya." Babu musu ta tsaya bata juyo ba kuma bata dawo baya ba. "A kausashe ta ji ya ce, "Ni zan zo na same ki kenan?." Jin abinda ya ce sai ta dawo da baya dan daman gudun kar ta yi laifi ya saka bata dawo ba. Leda ya ajjiye mata babba mai girma sosai ya nuna ledar da hannunsa ya ce, "ki auka" abinda ya ce kenan ya wuce aki ya barta a wajan. Nayla ta auki ledar ta shiga zuwa aramin falon da ta saba zama dan ta fi sakewa a can. e ledar ta yi ta fito da laces masu shegen kyau guda uku, sai atampa guda uku, sai veils masu shegen kyau da tsada gida uku, ba i da milk da blue kalar lace guda aya, sai kuma takalma afa uku. Nayla kallon kayan take yi kawai tana murmushi a zuciyarta na jin wani farin ciki na mamaye ko Ina. Farin ciki ya gama mamaye zuciyarta, ji take yana zaga jininta yana shiga ko wanne lungu da sa o sa jikinta. A bayyane ta ce, "shine ya siya min kayan sallah? Kenan ya kar e ni matsayin matarsa? Allah na gode maka, Allah na gode maka da ka ke kar ar addu'ata." Ita ka ai take surutai tana fito da kayan daga cikin ledar. Hannu na rawa ta shiga WhatsApp zata kira Salma voice call ta bata labari sai kuma ta dakata saboda kiran Didi da ya shigo. Da murmushi ta auka suka gaisa Nayla ta ce, "Didi an kawo min awara mai da in gaske, gaskiya na gode sosai ita kawai na ci. Daman yau na dawo da zazza i daga wajan aiki." "Amma dai kin samu lafiya ko?." "Eh ya sauka, daman gajiya ce." "Allah ya ara lafiya." "Amin Didi. Na gode sosai." Didi ta ce, "kar ki damu Nayla. Yau ya kawo min ziyara ya kuma kawo min kayan sallah, ki ta ya ni yi masa godiya Allah ya ara arzu i." Nayla ta yi murmushin jin da i da annushuwar da take jin zuciyarta ta ce, "Amin Didi. Nima yanzu aka ajjiye min nawa, kaya masu kyau Didi naji da i sosai." Diid ta ce, "To ya yi min ma balle ke matarsa? Allah ya cigaba da daidaita ku kawai, amma na fa a miki daman tun a baya da zarar kun saba shikenan komai ya are. Yana da matu ar wahalar sabo ne kawai, amma da an saba wallahi sai kin yi mamakinsa, dan gani zaki yi kamar an canja shi gaba aya." Nayla ta yi murmushi cikin gamsuwa da abinda Didi tace dan itama ta fahimci haka. Didi ta ce, "A taya ni godiya." Nayla tayi murmushi Didin ma haka kafin ta ce, "Amma zaki samu inki dai ko?." "Didi bani da tailor a nan Kano ai, da dai akwai wanda zai kai min Kaduna ne tailor na ko ana e gobe sallah zai inka min. To nan ban san kowa ba." Didi ta ce, "Ko Salma ki tambaya ta ha a ki da nata, ni na san nawa inkinsa bazai miki ba, kin saba da na ku na manya." Nayla tayi dariya ta ce, "Haba dai Didi, in dai ya iya inki ai shikenan." "Ki tambayi Salma in zai miki sai ki bashi, in bazai miki ba sai na tambayar miki nawan in za a samu." Nayla ta ce, "in sha Allah." Didi ta ce, "kinga tallan companyn na ku ake yi a arewa, azu nake yi masa maganar yake raina min hankali. Wai wanne talla? Na ce ban sani ba." Nayla tayi dariya mai sauti ta ce, "bai sani in ba ai Didi. Tsakani da Allah ni da Bashir muka tsara komai na je tashar muka yi komai ba tare da ya sani ba. Kuma da yake ba kallon tv yake yi ba shiyasa bai san ma ana talla ba." Didi taji wani da i ya mamaye mata zuciyarta, kana jin maganarta ka san taji da in maganar Nayla ta ce, "Yanzu Nayla da kan ki ki saka aka yi tallan nan kuma ke kika oye masa?." Nayla ta ce, "Don Allah kar ki fa a masa, kin san halinsa ya ce na daina shiga harkarsa, in ya san ni na bada advert in bazai ji da i ba arshe ma ya ce a daina haskawa. Ni kuma nayi tsakani da Allah saboda kayan nasa suna da kyau sosai, advert shine zai saka su zaga ko ina a san da company." "Amma ku in da kika kashe da yawa, kwanaki naji ana zancen tallah nan ana kashe ku i sosai." "Babu komai Didi, duk cikin cigaban mu ne ai." "Allah Sarki! Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya biya ki ya saka soyayyarki a zuciyar Omar." Nayla tayi murmushi ta ce, "Amin Didi, Don Allah kar ki fa a masa." Didi ta ce, "ya kamata ace ya sani, ai abin arzu i ne ai." "A'a don Allah, na fa a miki ne ma saboda kar ki sake yi masa zancen bana so ya fahimci ma ana yi tunda ba kallon tv yake yi ba." Didi ta ce, "Shikenan Nayla bazan fa a masa ba, Allah ya biya ki ya baku zaman lafiya na har anda." "Amin Didi. Yaushe zaki zo?." "Ai sai cikin sallah in sha Allah." "Ina so nazo kafin azumin nan ya fita." "Allah ya kawo ki." Nayla ta ce, "Amin ya rabbi." Didi ta ce, "ki fa isar da sa ona, ki ce na ce ina godiya sosai." Tayi ar dariya ta ce, "a'a Didi ba da ni ba." Didi ta