← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 205

Sashe 94

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

tabbatar ta gama sannan ya shiga ciki, yana shiga hasken akin ya kashe ya arasa ya kwanta a kusa da ita. Jawota jikinsa ya yi, sai ta motsa zata bar jikinsa ya kai bakinsa kusa da kunnen ta ya ce, "Jidda ki nutsu! Na fa a miki babu abinda zan yi miki, don Allah ki nutsu, ki daina jin tsoro." Ta ame shi a jikinta cikin rauni ta ce, "ka yi al awari?." Ya yi pecking in ta a kunnenta ya ce, "Na yi al awari Jidda. Ki nutsu kin ji?." Ta aga kai alamun to ta gyara kwanciya a jikinsa tana lumshe ido. Bayan wasu kwanaki. KRB3P055 Dad yana zaune a hakimce yana waya rai a ace yana cewa, "Ai kawai ba sai ka zo ba, magana ce da zamu yi ta a waya. Auren Ashraf da Narma bana bu atarsa kwata-kwata, gwara ka saka shi ya sake ta hakan zai fi." Daga cikin wayar gwamna ya ce, "A'a Shatima, ba haka ya kamata a yi ba, ka bari na shigo Abuja mu tattauna in ya so sai mu tsayar da magana. Yanke hukunci a waya ai bai yi ba." Sen ya ce, "ni na nemi ayi auren nan kuma yanzu na nemi ya saketa. Ashraf ya yi disappointing dina, I trust him, that's why na auki auren Narma na bashi without any event or something related to marriage, amma sai ya dinga wu alanta Narma, har ya kai ga ya saka an yi aborting Babynta. Ai kawai auren nan ya are, itama bata so, gwara ka saka shi ya sake ta kawai." Gwamna ya ce, "bai kyauta ba gaskiya, Amma ina so mu zauna mu yi magana sosai, a ganina abin zai fi akan mu tattauna a waya." "Kana jina? I don't want to our relationship to fall apart because of our children's marrige. That's is why I just want to him to divorce her." Gwamna ya ce, "gaskiya ne, shikenan Sen zan turo shi zuwa anjima zai sake ta in sha Allah. Ka bawa Narma ha uri." Dad ya ce, "kar ka damu, wannan abinda ya faru ba zai ta a friendship in mu ba." Sallama suka yi Dad ya kashe wayar ya kalli Mum da ta shigo a lokacin ta zauna ya ce, "Zai turo shi in anjima zai kawo divorce paper ta Narma." Mum ta yi murmushi ta ce, "hakan shine daidai. Mun samu Narma ta dawo hayyacinta bazan so na sake rasa ta ba." Narma ce ta sauko daga sama, Dad ya kalle ta ya ce, "Zo nan Narma." Ba musu ta arasa inda yake ta zauna. Da farin ciki akan fuskarsa ya ce, "Yau Ashraf zai kawo divorce paper inki." Murmushi ta yi a yangance ta ce, "glad." Dad da mamakiya ce, "ahh....! is that all you have to say? Ina tunani zan ga fuskarki with so excitement sai na ga akasin haka." "Dad you pushed me into this marriage knowing I don't love him, yanzu kuma auren yana arin arewa, What did you expect me to say Dad?." Dad ya ri ota ya ce, "Haba Narma, na auka wannan duk ya wuce kuma, yanzu mu yi facing abinda zai faru nan gaba bayan ya sake ki. What country are you planing to go for your phd?." Narma ta yatsine fuska ta ce, "Dad, I'm not ready for a phd right now, In fact I'm even not interested in further studies. My masters digree is sufficient for my career goals." Mum ta ce, "but why Narma?." "Kawai Mum, i'm not interesting." "Amma zaki iya karatun zai ebe miki kewa." Narma ta ce, "bana so." Dad ya ce, "is okay." Narma ta cigaba da danna wayarta bata ce komai ba tana ji suna tattauanwa. Kamar yadda mahaifin Ashraf ya fa a kuwa ba jimawa Ashraf ya zo gidan da alama yana cikin garin Abuja, har cikin falon ya shigo ya samu Narma ce ka ai a zaune tana danna waya. Kallon ta ya yi itama ta kalle shi ta auke kai kamar bata ganshi ba, ya zauna yana binta da wuala antaccen kallo kafin ya ce, "Finally I've divorced you after satisfying my desires, so u have no further use for me. Here's your divorce paper" ya fa a yana mi a mata takardar sakin. Dad da Mum da suke jin abinda ya ke fa a Mum ta araso ta ce, "ya yi kyau Ashraf, har cikin gidansu ka ke zuwa kana fa a mata wannan maganar banzan? Gaskiya baka da mutunci baka san mutunci ba." Ashraf ya kalli Mum da take sakkowa daga sama, kafin ya yi magana Dad ya ce, "shikenan ko? So get out!." Ashraf ya ce, "Dad zan fita, but let me make you know one thing; in dai a kan tarbiyyar shigar da ku ka ora Narma a kai kenan babu wanda zai aureta tsakani da Allah. I married her for her physical appearance, and now I've gotten what I want. Dan na sake ta bazan ji komai ba, daman ba ita nake so ba. Da farko na auka ina sonta, sai bayan na aureta na gane ikram nake so, Narma kuma jikinta nake so da ya kasance a bayyane ko yaushe......" ya dawo da kallonsa ga Narma da take kallonsa ya ce, "Dan haka ki yiwa kan ki fa a, if not zaki ta aure kina fitowa wallahi, kowa da ya samu abinda yake so a tare dake kamar ni zai gama dake, da zarar ya gama da ke kuma saki ne zai biyo baya." Dad ya fusata sosai ya ce, "Ashraf get lost!." Ashraf ya aga hannu sama alamun surrender ya ce, "Na tafi, bye my ex wife" ya fa a yana mata bye-bye ya fita daga falon. aukar paper da ya ajjiye Mum ta yi ta karanta ta kalli Dad ta ce, "Dan wula anci har saki uku." Dad ya ce, "ai gwara haka, gwara da ya yi haka dan ya tabbatar da baza ta sake komawa gare shi ba." Ya kalli Narma da bata ce komai ba ya ce, "shikenan ko? Na raba auren da na ha a ko Daughter?" Ya fa a yana smiling. Narma ta kalle shi fuska babu walwala ta ce, "Dad do you want to me to be happy?." "absolutely my Love! your happiness means everything to me. I want you to be happy and fulfilled in life." "Please allow me to married Faruk, I'm still have strong feelings for him. If you refuse it like you did previously, it will deeply affect my happiness." Mum ta ce, "Tiger again! Narma what are you saying?." "Gaskiya Mum, ina fa ar gaskiya ne kuma shine abinda yake zuciyata" tana fa ar haka ta bar falon ta hau sama da gudu. Mum ta ce, "har yanzu bata bar tunaninsa ba fa, wai wannan wanne irin bala'i ne haka? Wanne irin asiri ya yiwa yarinyar mu?." Dad da ya yi shiru ya kalle ta ya ce, "kar ki damu, da ta sake dawowa daidai zata dawo hankalinta. Ki nutsu, kema kin san auren ta da shi ai ba abu ne da zai yu ba, itama fa a take yi amma ta san ta fi arfinsa, ba sa a aurenta ba ne." Mum ta ce, "Narma da gaske take Sen, Narma da gaske take, kana jin yadda take magana ka san daga zuciyarta ne." Ajiyar zuciya ya yi bai ce komai ba ya hau sama shima, amma yana tunani a zuciyarsa ya zama dole ya samar mata de farin ciki ko ta wacce hanya ne. Kamar yadda ya ata mata yana so ya faranta mata ta hanyar yi mata abinda take so.
Chapter 94 · 0% Book details