← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 205

Sashe 137

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya fa a yana mata kiss a kumatu ya tashi ya fita. Nayla tausayin kanta take ji, tana son mijinta tana kewarsa amma ta rasa abinda yake yi mata da i, ta rasa me yake damunta har ya canja ta haka. Ranar ya sakar mata fuska duk da daman bai daina yi mata fara'a ba, sai dai rashin kai hannunsa jikinta da ba yayi, kuma bai yi arin yi mata komai ba itama bata nema ba a haka dai suka yi bacci. Kamar yadda ya fa a ranar talata da safe ya hau jirgin abuja ya sauka a airport na Abuja, sai arfe aya na rana hau jirgi suka bar Nigeria. Nayla tana gidan Hajja har jirginsu ya tashi, gidan babu da i saboda babu Salma sai anwar Hajja itama kuma ta girma sosai. Zaman gidan baya yi mata da i kawai sai ta tafi gidan Mama Sa'adatu, gaba aya bata son zama a Kaduna da can zata je haka kawai bata son zuwa. A gidan Mama Sa'adatu ma bata da walwala ta fi ganewa ta ke e kanta a aki ita ka ai bata son hayaniya. Bayan kwana uku da tafiyarsa ya tura mata hotunan abinda ya faru a can da hoton da aka auka kamar yadda aka auka a Kano. Ta taya shi murna amma ko a status bata sakawa saboda mata. Amma da ta shiga X sai ta ga ana ta sake orawa ana addu'a, masu cewa ya burge su suna yi masu addu'a suna yi. Gajiya tayi da zaman ta auki mota ta tafi gidan Didi bayan ta fa a masa ya barta da yar. Da maganar abinda ya faru Didi ta tare ta itama ya tura mata hotunan, Didi kuwa an saka a status tana addu'a da fatan alkhairi. Bayan sun gama gaisawa da maganar Omar Didi ta kalle ta a nutse ta ce, "Nayla sai nake gani kamar kina da damuwa ko?." Nayla ta yi shiru kafin ta ce, "ina da damuwa Didi." Didi ta ce, "me ya faru?." Nayla ta ce, "Rouhii ne yake fushi dani" ta fa a hawaye yana sakko mata. Didi ta ce, "Nayla na rasa yaushe zaki daina ji da autanci, wannan ai aramin abu ne, zama zaki yi ke da shi ki bashi ha uri ba shikenan ba?." Nayla ta ce, "Didi bana kyauta masa ne, ina cutar dashi ni kaina na sani." Didi da mamaki ta ce, "Kina cutar dashi kuma Nayla? Ta wacce hanya kenan?." Nayla ta yi shiru tana wasa da hannunta cikin jin nauyin maganar da zata furta. Ganin hakan sai Didi ta ce, "kar ki damu in baza ki iya fa a min ba, amma ki samu ku daidaita dashi in ya dawo." Nayla tayi ajiyar zuciya ba tare da ta ago ba ta ce, "Didi haka kawai bana so ya ta a ni, in ya ta a ni sai naji kamar zan mutu. Shi kuma tunda ya fahimta ko hannuna bai sake ri ewa ba sai ana e gobe zai yi tafiyar nan" ta ago ta kalli Didi ta ce, "Wallahi ban san meyasa ba, ban sani ba ko wata cutar ce ta kama ni." Didi ta bita da kallo tana zargin wani abu ta ce, "Kuma babu ciwon kai ko zazza i?." "Babu komai, gwara ma dai jiri, ina yawan jiri sosai, in na tashi sai naji kamar zan fa i amma bana jin komai." Didi ta girgiza kai ta ce, "Da mota ki ke?." Ta aga kai alamun eh ta ce, "Bara na kire Yalla ai a waya sai mu je asibiti a fa awa likita." Cike da gamsuwa Nayla ta aga kai, Didi ta shiga aki ba jimawa ta fito da hijjabi Nayla ta auki Marmerh suka tafi. Nayla ta ce, "Akwai asibitin da Twiny take zuwa, akwai likitoci sosai bara mu je can." Can suka wuce Nayla ta ajjiye motar suka shiga ciki suka biya ku in ganin likita aka nuna musu inda zasu je. akin Nayla ta shiga ta yiwa likitan bayani ya rubuta mata scaning ya ce ta je ta yi. Tare suka je suka biya ku in da Didi aka nuna mata akin scanning in ta shiga. Ba jimawa aka gama ta fito aka kawo mata result har inda take, ta mayarwa da likitan a lokacin suka shiga akin tare da Didi. Dr ya bu e result in ya kalli Nayla ya ce, "Hawwa kina da ciki na sati hu u, duk abinda ki ke ji shine ya saka ki ke jinsa. Ba abin damuwa bane wannan yanayin da ki ke ji, daga kin fita daga first tremister komai zai wuce" ya fa a yana mi a mata takardar. Nayla kasa magana tayi ta zubawa likitan ido kawai tana kallo, kafin ta kalli Didi da take murmushi sai kuma ta sunkuyar da kai cikin kunya. Magani ya rubuta mata ya bata suka fito ita da Didi ta kasa cewa komai. Mamaki take yi wai ciki ne da ita, babu abinda take ji in ba wannan damuwar ba sai kuma jirin da take ji ba, ashe daman ana iya yin ciki babu laulayi?. Didi kamar tafi Nayla farin ciki, ta kasa oye muryarta sai addu'a take yi. Suna shiga mota ta ce, "da na iya tu a motar ai da bazan bari ki tu a ba wallahi. Alhamdu lillah, burina a duniya yana ta cika, zan ga a ko ar da Omar zai haifa." Nayla ta kifa kanta akan sitiyarin motar tana jin kunyar Didi mai tsanani. Didi tayi dariya ta ce, "shi yana can yana fushi bai san abinda yake so ne ya samu ba, dole na yi masa babban albishri." Nayla ta ago da sauri ta ce, "Don Allah Didi kar ki fa a masa, ki bari ya dawo." Didi ta ce, "To ai da ki ka shiga wajan likita ya kira ni wai bakya aukar waya na ce bakya jin da i muna asibiti, duba wayarki zaki ga kiran." Kamar jira yake yi tana kallon wayar kiransa na shigowa ta auka kafin ta yi magana ya ce, "Jidda Didi ta ce min bakya jin da i an je asibiti, me ya same ki? Kina lafiya dai ko? Me suka ce yana damunki?. Ki yi magana mana, na kira Didin bata auka ba." Nayla jin ya rikice yana jero mata tambaya sai ta ce, "malaria ce aka ce tana damuna." "Amma da sau i dai ko? Kwantar dake suka yi ko ruwa aka saka miki?." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Babu komai fa Rouhi, magani kawai suka bani." "In akwai damuwa ki fa a min, kuma meyasa baki fa a min baki da lafiya ba har ki ka ce min kin tafi gidan Didi? Kin san baki da lafiya ina ke ina aukar mota?. Sannan ba na ce duk inda zaki je ki dinga bari a kai ki ba? In aka sake arin cutar dake fa?. Meyasa ki ke yi min haka ne Jidda?." Jin ya fara yi mata fa a sai ta ce, "Ka yi ha uri." "Wannan ai ganganci ne, kin san baki da lafiya sai ki auki mota ki bar gida? Meyasa baza ki ha ura ba?. Na hana ki fita ke ka ai amma bakya ji, yanzu da wani abun ya same ki fa?." Nayla ta ce, "to ai nace ka yi ha uri." Ya yi tsaki ya ce, "ina Didi?." Nayla ta ce, "gata" ta fa a tana bawa Didi wayar. Didi ta kar a tana ji kamar ta sanar masa amma tunda Nayla ta ce bata so gwara ta yaleta ta fa a masa. Ya ce, "Didi don Allah ki kula da ita, kin tabbatar zata iya driving?." Didi ta ce, "Gaskiya nima bana so tayi, bara na kira Tukur ya zo nan ya tafi da motar." Tsaki ya yi akwai ya kashe wayar, Didi ta kalli Nayla tana dariya ta ce, "A haka ma bai san ciki ne dake ba." Nayla ta yi murmushi, Didi ta kira Tk tayi masa kwantace ya ce gashi nan zuwa. Suna zaune a motar ba jimawa ya zo, Nayla ta fita ta koma baya ya shiga motar ya ja suka tafi. KRB3P084 Nana haleema. Sai da aka sauke Didi a gida sannan aka wuce da Nayla gidan Mama. Da suka je ya ajjiye motar ya bata key ya koma a napep ita kuma ta shiga ciki. A falo ta samu Mama da Abbas da Khaleefa, Mama ta bita da kallo ta ce, "har kin dawo?." Nayla ta ce, "eh Mama, jiri nake ji" ta fa a tana zama kafin ta gaishe da su Abbas. Mama ta ce, "Sannu, rana ce ta saka ki jiri, dan yau ta bu e sosai, kuma kamar bazata bu e ba saboda hadarin da ya ha azu." Nayla ta mi e ta shiga ciki takardar hannunta ta fa i bata sani ba. Khaleefa da yake kusa da ita ya auka yana cewa, "Nayla kin yarda da takarda." Nayla ta shiga ciki bata ji shi ba. Ganin hoton scaning a sama sai ya ja hankalinsa ya bu e takardar, ya kalli Mama ya ajjiye bai ce komai ba. Mama ta kalla ta ga alamun takardar scaning ce ta ce, "A'a Nayla bata da lafiya? scaning taje daman?" Ta fa a tana bu ewa tana ganin abinda yake jiki. Murmushi ta yi ganin abinda yake rubuce a jiki, a lokacin Nayla ta dawo tana cewa, "Mama na yarda takarda......" Maganar ta tsaya ganin result in a hannun Mama. Mama ta mi a mata ta ce, "gata nan." A sanyaye ta kar a ta koma ciki da sauri cikin jin kunya. Mama bata ce komai ba suka cigaba da hira kafin ta tashi ta shiga wajan Nayla. A zaune ta same ta, Mama ta zauna kusa da ita ta ce, "Nayla sannu." Nayla ta sunkuyar da kai cikin kunya ta agawa Mama kai. Mama ta ce, "babu abinda ki ke so?." Nayla ta ce, "Babu Mama." "Kin tabbatar? In akwai ki fa a min kinga ba ke ka ai ba ce." Nayla sai ta kifa kanta a jikin Mama cikin jin nauyin maganar. Mama ta yi dariya ta ce, "ni tunda ki ka zo nake kallon ki kamar mai ciki, ashe shi in ne. Allah ya inganta Nayla
Chapter 137 · 0% Book details