← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 205

Sashe 15

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunan page in ya fa a mata sannan ya ce, duk da sunan k a amfani, ig, x, facebook har da TikTok ma. Nayla ta ce, zan taya ku advert in sha Allah. Ka bani number ka saboda kayan da za akai gobe. Bai yi musu ba ya bata number sa ta yi saving ta kira shi shimaya yi saving sannan ta ce, Amma kun ta a kai advert gidan tv ko radio haka?. Bashir ya ce, gaskiya ba mu ta a ba. Ya kamata ace an kai saboda manyan mutane su gani. Ga sallah zata zo in aka yi talla yanzu abinda zai wuce yadda ake tunani. Gobe in fita zan shiga arewa24 zan ji ya tsarin sun yake, yadda muka yi dasu zan sanar dakai. Za a yi tallah a kwanakin nan koda guda biyu ne. An gama Antyn mu, hakan ma tunani ne mai kyaun. Nayla ta ce, tunda ka ce wannan kayan shi ne ya ce ka kawo, Ina son guda aya yanzu ka kawo min daga shop in amma irin wannan nake so ta fa a tana nuna irin wanda ta saka a afarta. Bashir ya ce, ai kawai Antyn mu ki auka a nan, babu irin wa annan a shago. Yin su aka yi kuma ya ce ba yanzu za a fitar dasu ba. Nayla ta girgiza kai ta ce, to na gode. Yadda mu ka yi zan yi maka waya sai a shirya wajan in zasu zo aukar video. Amma bana son Boos in na ku ya sani. Ya yi dariya ya ce, babu damuwa Antyn mu, duk da dai kwana biyu yana zama sosai a shagon amma zan san abinda zan yi. Nayla ta amsa ta ce, don Allah zaka iya shigo min da farar mota da take wajen gidan nan?. Bashir ya ce, zan iya. Ta bashi key n ta ce, na gode. Kar a ya yi ya fita ba jimawa ta ji ya shigo da ita sannan ya dawo ya bata key in tayi masa godiya shi kuma ya fita. Kallon takalma ta zauna yi sai kuma ta dinga sakawa tana yin hoto da video a afarta, ko wanne kala sai da ta saka tayi hoto kuma sosai hoton yake yin kyau a afarta. Kai da ka kalli afar ka san tana shan predicure saboda yadda farcen afar yayi haske sosai, ga wani kyau da afar tayi musamman in ta saka takalmin. Shiru tayi tana kallon takalmin ta tabbatar colleagues inta zasu siyi takalman sosai, kuma tana da friends da cousins yadda takalman suka yi kyau da wuri za a siye su. Ajiyar zuciya tayi tunawa da an gidan su gaba aya suna saudia, ita kanta ta manta rabon da tayi aramar sallah a Nigeria, ta manta yaushe rabon da ta yi azumi a Nigeria, ko lokacin da take makaranta ajjiye karatun take yi tayi tafiyarta indai ba jarabawa zata yi ba, da yake Allah ya aiko mata da addararta gashi yanzu tana yi. Ajiyar zuciya tayi tana jira dare ya yi ta je ta yiwa su Hajja sallama dan tunda ta shigo gidan bata ta a fita ba sai yanzu da ta raka Yaya J. A wajan ta bar takalman amma ta auki guda aya kamar yadda Bashir ya ce, zuciyarta na ta rawa akan aukar kar ta je tayi laifi, a haka dai ta daure ta auka. Bayan sallar la asar ta rasa abinda zata yi, gashi dai tana cikin an first ramadan with habibi amma ita first ramadan with habibiya ne ba habibi ba, dan shi ba ma shan ruwan gidan yake yi ba balle ya ci wani abu, bata ta a ganin ya bu e fridge ya auki ruwa ba, sai dai ya shigo dashi a hannunsa. Shiyasa ma bata ta a tunanin yin girki ba, dan ta san in tayi ma asara zata yi shiyasa bata wannan gangancin. Tea kawai ta dafa ta zuba a flakas, bayan ta gama ta ji tana sha awar soya osai ta wanke wake tana wakewa tana cewa, Kayan abincin nan sun yi yawa, gwara na yiwa Didi magana a bayar in ba haka ba zasu lalace. Iya ni ka ai nake ci ya zanyi dasu? Ko drink in nan ma har ya yi expire ban shanye ba. Daga haka ta gama ta marka a ta saka a fridge dan sai anjima zata soya. Sai da yamma tayi sosai sannan ta soya, bayan ta gama tayi alwala ta hau kan sallaya tana fa awa Allah bu atarta har aka sha ruwa. Ruwa ta sha sannan tayi sallah ta fito ta sha tea da osanta sannan ta yi wanka ta zauna tana jira ayi sallah i sha. A lokacin ya shigo da sallama kamar ko yaushe, ta amsa bai kalle ta ba ya kalli kayan da suke wajan ya auka ya shiga dasu aki ba tare da ya ce mata komai ba. Bai jima ba ya dawo falon ya auki ruwa ya sha ya zauna yana duba waya. Nayla gabanta fa uwa yake yi ganin ya zauna a falo bayan ya san tana zaune, sannan ga ruwa da ta ga ya auka yana sha a karo na farko da taga hakan tunda ta suka tare a gidan. Kallon sa take yi tana jin kamar bata kyautawa yadda ko gaisuwa bata ha a su, sannan kuma gashi ana azumi ko babu komai in ta ce masa an sha ruwa lafiya zata samu lada. Tunawa da batun komawarta aiki da kuma zancen son zuwa gidan Hajja ya saka ta daure ta gyara zama bata ce komai ba. Waya ya fara amsawa kamar baya son magana kafin taji yayi tsaki ya kashe wayar. Nayla ta ha iye yawu tana mamakin izzar wannan bawan Allah, da yar ta ce, Yaya Omar an sha ruwa lafiya?. yar ta iya fa ar maganar saboda yadda zuciyarta take bugawa, kwana biyu da bata bata gashi ba sai ya yi mata kyau sosai, duk da ya an rame amma ya ara yin haske gashin kansa da na fuskarsa ya sake taruwa kuma ya yi ba i sosai. Yaya Omar in da ta ce shine ya saka shi lumshe ido a hankali, bai san meyasa yake jin wani iri ba a duk lokacin da tace masa Yaya, itace kawai take ce masa Yaya bayan ita babu wata halitta a duniya da take kiransa da wannan suna. Bashi da anne mata ko maza balle yaji hakan daga bakinsu, shiyasa in ta fa a sai gabansa ya fa i. Ganin bai mata magana ba sai ma rufe ido da ya yi ya saka Nayla ta ce, Gobe su Hajja zasu tafi umrah, Ina so in an idar da sallar tarawee na je nayi mayi sallama. Sannan kuma gobe zan koma aiki. Kamar bai ji ta ba haka yayi, nan kuwa yana jin duk abinda take cewa, bai san meyasa yake jin wani abuna zuciyarsa ba indai zata kasance tana kusa dashi. Ya san kawai saboda ba ya sonta ne shiyasa yake jin hakan. Tashi ya yi zaune sosai yama kallonta bayan ya ha e yatsunsa waje aya kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya auke kai. Nayla gaba aya ji take ta gama muzanta a wajan, tayi masa magana ya yi mata banza bayan ya ji. Idonta ya ciko da hawaye saboda wula ancin da ya yi mata ya daki zuciyarta, bata ta a jin haushin abinda yake mata kamar na lokacin ba. Gata gashi tayi masa magana ya shareta bayan ta san ya ji tunda har niyar bata amsa ya yi ya fasa. Hawaye ya zubo mata akan fuskarta sai ta mi e zata bar wajan cikin sanyi jiki da sagewar guiwa. Cikin muryarsa ta ko yashe ta ji ya ce, tsaya!. Cak ta tsaya bata zauna ba ya ce, ai na fa a miki babu ruwanki da lamarina babu ruwana da lamarin ki. Dan zaki je wani gida ina ruwana? Ki je duk inda zaki je babu abinda ya dame ni, in duniyar zaki bari Allah ya kiyaye hanya bai damu Omar ba. Ki daina takura min da magana, bana son a shiga harkata in dai ba ni na shiga harkar mutum ba. In kina yi min haka zaki yi dana sani wata ran. Nayla hawaye ya sakko mata, murya na rawa ta ce, to, na gode tana fa a tayi ciki da sauri tana kuka. Da kallo ya bita ya ja tsaki tare da ta e bakinsa. Samun kansa ya yi da sake kallon inda ta bi ya ja numfashi kawai sai ya tashi ya bar gidan gaba aya. Nayla kuwa kuka ta ci sosai, tausayin kanta take ji da rayuwarta, kenan ita a haka rayuwarta zata are? A haka rayuwarta zata zauna babu wani cigaba kenan? Laifinta ne dan an bashi ita ba tare da ya sani ba? Laifin ta ne dan zanen addarar su ya zo a haka? Meyasa yake yi mata haka bayan ita matarsa ce?. Kuka take yi sosai tana jin zuviyarta na yi mata matu ar zafi, babban abin haushin kuma tana matu at sonsa har yanzu, duk abinda yake yi mata bai saka sonsa ya fita daga zuciyarta ba, azu da ta ganshi ji take kamar ta zauna kusa dashi ta dinga shafa gashin da yake fuskarsa saboda tsananin burgewa da kuma shau in so da take masa amma babu dama. Bata da wannan damar kuma bata tunanin zata samu irin damar har abada. Kiran sallar i sha da aka yi ya saka ta tashi ta goge fuskarta, ba jimawa aka tayar da sallah ta bi jam i har aka yi tarawi aka idar. Lokacin tara na dare ta kusa, da yake ta san daren azumi ne ba a rasa jama a a kan hanya sai ta saka hijjabi da cross slippers ta auki wayarta ta fito falon. Sai kuma ta tsaya tana tunanin ya kamata ace ta fita kuwa?. _Shi ya baki dama ai, ya ce ki je duk inda zaki je, ki yi tafiyar ki kawai._ da wannan tunani ta auki key in gidan ta kulle gate in ta nufi gidan Hajja tana takawa a hankali iskar bayan sallar i sha ta watan azumi na ratsa jikinta. KRB3P008 Nayla kusan ata tayi a hanya da yar ta kai kanta
Chapter 15 · 0% Book details