Sashe 52
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sama ya cire ya saka mata sannan ya auko ta kamar jaririya ya kaiwa Hajja ita dan yaji tana kiran sunan Hajja, kuma yaji ana cewa jikar Hajja ta ata. Haka ya dinga masifa a gidan Hajja, yana cewa ta ya za a bar yarinya ta fita ita ka ai da daddare bayan an san ba uwa ce ita, aka dinga yi masa godiya da abinda yayi sai kuma hukuma ta shigo maganar akace ya auki doka hannunsa sai an hukunta shi. Sun so a kai shi prison zaman jan kunne amma Abiy ya shiga ya fita aka yale shi, ya sake yi masa godiya sosai akan abinda ya yiwa arsa. Daga wannan lokaci kuma Omar sai ya zama jan wuya kamar yadda suke masa take da sunan, dan sai ya zama babba kuma madugu a unguwar. Kullum Didi tana hanya wajan an sanda, ko nemansa tayi ta rasa da ta samu labarin an yi kame in taje yana ciki. Da farko ya fara aikin yin takalma a wajan wani mutum da Didi ta takura masa, da yake ya iya yanka fuskar takalmi in ya yi aka ha a sai ka kalla saboda kyau. Allah ya saka masa albarka ya iya aikin sosai dan sai da ya zama baban yaron mutumin saboda yadda ya ware in dai ya ga dama zai yi. Amma daga baya sai ya watsar ya cigaba da harkar abinda ya saka gaba. A cikin wannan lokaci ne suka sake canja gida suka kar i wanda yafi wancan kyau amma bai kai na su girma ba, suka sake zama ma otan Hajja sosai dan da sun an yi nisa. Ragowar ku in Didi ta fara sana'a ta kuma shiga makaranta tana NCE. Daga wannan lokaci Omar abin sa komai gaba yake yi, sai dai shaye-shaye ne baya yi, kuma bai ta a kashe rai ba amma duk wani abu da ya shafi daba Omar ya zama babba kuma Jan wuya a wannan fanni. Ku i yake samu sosai saboda an siyasa da suke amfani dasu, musamman ma shi da aka san bashi da tsoro, kowa a cikin kiransa yake yi domin a bashi aiki. Omar ya ta a zaman prison saboda fa a da akayi tsakanin yaran sa da yaran wani jan wuya kamar sa, har ya kai ga yaran sun yi kisa da aka zo duk sai aka kama su gaba aya. Su aka yanke musu hukunci life in prison, su kuma su Omar aka yanke musu hukuncin wata aya a gidan yari. Haka Didi take yawo a hanya wajan kai masa ziyara, duk ta rame saboda rashinsa, ko yaushe cikin kuka take. Sai da watan nan ta cika sannan ya fito, maimakon ya yi hankali sai kuma abin na sa ya sake yin gaba dan sai ya zama kaf arear Yakasai da ofar mata an daba iri sa na wajan basu isa su shiga area sa ba. An ta a kawowa Didi hari a kan hanyarta ta dawowa daga makaranta, Omar da ya ji labari kashe yaron ne kawai bai yi ba, amma azaba ya gana masa ita. Ya yayyake shi, ya yi masa kaca-kaca da fuska. Tun daga kansa babu wanda ya sake arin hararar Didi, sannan ko makaranta zata je akwai wanda zai saka ya rakata. Zaman sa ya kawo security sosai a unguwar, dan ba a wacen waya ko wani abu mara kyau a areasa, dan in kayi ma sai ka kamo ka kuma sai ya kai ka gaban yan sanda. Dabanci yake yi mai tsafta wacce in baka ta a shi ba babu ruwansa da kai, in kayi laifi kuma ya kai ka ga hukuma, in hukuma bata auki mataki ba to tabbas shi zai auki mataki. Zafin kai, zuciya, aurarriyar fuskarsa ya saka kowa shakkar sa yake yi, dan baya agawa kowa afa. Hatta babban yaronsa na farko da aka samu da wace waya shi da kansa ya kai shi gaban hukuma aka yi masa hukunci. Wannan ya saka suke masa take da Damisa i sabo. Omar bashi da sabo ko ka an, bashi da saurin sabo ko kusa, kafin ku saba a za a jima sosai. Yana da ri o sosai, ya kasa manta abubuwan da iyayensa suka yi masa, duk daga baya dukkan su sun nemi yafiyar su gaba ayan su amma ya kasa kar ar su a matsayin danginsa. Ita kanta Didin ta kasa sakin jiki da dukkan su, sai dai duk abinda ya tashi tana zuwa amma shi ko mutum aya ma baya ganewa a cikin su. Rayuwarsa yake yi shi ka ai daga shi sai Didi. Omar mutum ne da baya son ba o ko ka an musamman daga cikin unguwar da suke, maganar da suke ya awa akansa da Didi ya saka baya so kowa ya ra e ta sai shi ka ai. an aike almajiri bata dashi, duk abinda take so ya gwammace ya aika yaransa su siyo da dai wani ya shigo gidan. Su ma mutane da yawa tsoron shigowa suke yi dan gamuwar bata zama alkhairi. In kaga Omar yana dariya to Didi ce a kusa dashi, in ka ga Omar na hira sosai Didi ce, in ka ga Omar na bada labari Didi ce, in ka ga Omar cikin rauni Didi ce, in ka ga Omar cikin damuwa damuwar Didi ce, in ka ga Omar ya yi Didi ce, in ka ga Omar ya bari Didi ce. In dai ba ita ba babu mai saka shi babu mai hana shi, sannan babu wanda ya isa ya yi masa magana balle su yi hira. Bashi da aboki ba shi da kowa daga Didi sai wayarsa dan masoyin danna waya ne. Duk wani platform Omar yana shiga, ya san ta kan social media sosai kuma tsabar shige-shige ne ya kai shi. Shekarar Didi talatin da biyar amma har lokacin bata ta a yin aure ba, duk masu zuwa ba da aure suke zuwa ba an iskan zamani ne. Dan akwai wanda ya ta a zuwar mata da iskanci. Labarin ya kai kunnen Omar ya auki yaransa aka tarafa shi suka ce sai sun sake masa kaciya. Bawan Allah ya dinga magiya yana kuka, sai da suka taso shi har gaban Didi ya bata ha uri, amma duk da haka basu yale shi ba sai da suka aske masa gashin kansa tass suka kuma yi masa alli- alli a mazaunai. Tun daga kansa in da iskanci ka ke tafe ba ka sauke shi a gidan Didi sai dai wani gidan, in kazo da wata maganar ta kirki ma sai ka tsorata, in ya dinga tsare ka da ido in ba mai gaskiyar gaske ba ne sai ka kwafsa. Didi tana sana'ar yin abinci ta siyar in an saka order kuma Allah ya saka mata albarka sosai take samun riba fiye da tunanin mai tunani, shiyasa gidan su kullum kamar gidan amarya duk abinda ta gani tana so tana siya, tun tana ajjiyewa matsayin na aure har ta kwaso su duka tana amfani dashi a ganin ta kamar bata da rabon aure a duniya. Didi kullum cikin yiwa Omar addu'a take yi na neman shiriya, kuma babu laifi akan an samu canji musamman yadda ya daina fa a sai yana da dalili mai arfi. Ko gonarsa aka shiga sai dai ya kai maganar ga hukuma wani lokacin kuma ya yi hukunci da kansa. an unguwar suna son Omar kuma basa sonsa, suna sonsa saboda zaman sa unguwar ne take da tsaro babu arayi balle masu wace. Basa son zamasa saboda babu wanda yake shiga harkarsa kuma ko waye kai kayi masa sai ya rama. A haka Didi ta yi aure da duk abinda ya biyo baya. Wannan shine dalilin da ya saka Omar ya tsani ahlin su, ya tsane su tsana mai muni. Baya girmama kowa a cikin su, baya aga kai ya kalle su ma balle su samu damar magana daga gare shi. Yana da matu ar ri o, shiyasa ya kasa mantawa da abubuwan da suka faru duk da an kwana biyu da faruwar su. Wannan kenan!. Kuna ganin dangin Omar Sun cancanci tsana daga wajansa KRB3P028 ArewaBooks@nanahaleema11. Nayla tunda ta fizgi motar a guje ta bar unguwar take gudu duk da kasancewar yamma ce akwai chunkoson abeben hawa. Sai da ta an yi nisa sannan ta ganganara kan titi ta kifa kanta akan sitiyarin motar ta saki kuka mai karfin gaske. Kuka take yi mai sauti cikin shashshe a, ciwo take ji a zuciyarta sosai, wani abu take ji ya cure a zuciyarta ya dun ule waje aya. Daga cikin zuciyarta kukan yake tasowa ba tare da ta shirya masa ba, hakan ya saka hawayen ya i tsayawa sai sauka yake wani yaka bin wani. Kalaman Omar in ta tuna sai ta ji duniyar na juya mata, tun farko ta san ba sonta yake yi ba amma bai ta a kallonta ya fa i wannan kalmar mai aci da sanya bugawar zuciya ba, kalmar baya sonta da ya furta ta fi komai aga mata hankali. Jingina tayi da kujerar tana hawaye tana sauke ajiyar zuciya irjinta ta yana agawa a hankali yana sauka a hankali. Ta jima a zaune a haka tana hawaye, kanta ya yi nauyi kamar yadda zuciyarta take da wannan nauyin. Kiran sallar da ya kara e ko Ina ya saka ta mi e zaune sosai, ta gyara zama tana kallon glass in motar ta gaba. Bata gani sosai saboda ciwon kai, ta saka gefen mayafin ta goge idanunta ta sake kallon gaba ta ta ga tana gani amma ba sosai ba. Ajiyar zuciya tayi ta ja motar a hankali tana tafiya. Allah ne kawai ya kaita gidan Mama Sa'adatu lafiya, zuwa lokacin zazza i ya gama rufeta sai sanyi da yake ratsa asusuwanta. Kanta yayi zafi ga nauyi, da yar take iya bu e ido saboda ciwon da kanta yake yi mata. Yadda take danna horn in a kasalance zai saka ka san tana cikin rauni da rashin lafiya. Mai gadin da ya bu e ya ga motarta ce sai ya bu e mata gate ta shiga ta ajjiye motar a tsakiyar gidan. yar ta daidaita kanta ta bu e motar ta fito saboda ciwon kan da ya ke barazanar tarwatsa mata walwarta, ga zazza i ya