← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 205

Sashe 106

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Omar shine a zanen addarar Nayla, kawai kin zama silar aurensu ne Mama, wallahi ko babu goyan bayanki sai ta auri Omar saboda shine mijinta. Mama meyasa ki ka yi gaggawa baki bari Allah ya yi ikonsa ba? Meyasa ki ka shiga lamarin ubangiji..?. Tunda mahaifinta yana yi mata addu'ar samun miji na gari na tabbatar da Nayla bazata ta a yin kuka a gidan mijinta ba, saboda wannan miji na garin da yake ro a mata shi Allah ya bata." Ya ri e hannunta duka biyun ya ce, "Don Allah Mama ki bar wannan tunanin daga zuciyarki, ki manta dashi, ki goge shi daga zuciyarki, indai da gaske kin yafe in to ki bar Nayla ta yi rayuwarta a inda Allah ya ajiiyeta. Don girman Allah Mama kar ki sake aikata wani abun da zai saka Nayla zubar hawaye, ke uwa ce a gare ta, jin wannan maganar babban abin kunya ne a garemu, in dangin mahaifiyarta suka ji labari kamar mun auki wu a mun cakawa kan mu ne Mama. Kamar yadda Abiy ya fa a, Jawad yana son Salma ar uwar Nayla da aure, in maganar nan ta je kunnen danginsu abin bazai yi da in ji ba. Muna ro on ki don Allah ki bar wannan tunanin ya wuce, in ma akwai wanda yake zuga ki wallahi ba hanyar arzu i yake kai ki ba Mama. Ki yi ha uri, tunda kin yafe a bar shi an yafe in komai ya wuce don Allah." Mama har lokacin bata ce komai ba tana jin duk abinda yake fa a. Ahmad ya tashi ya kalli su Jawad ya yi musu alamun da su fita su yaleta, ai kam duk suka fita har Jidda da saukarta a Kaduna kenan ta ji abinda yake faruwa. Mama da kallo ta bi su har suka fita ta rufe ido kawai tana tunani kala-kala.
Chapter 106 · 0% Book details