Sashe 24
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kallonsa da take yi cikin rashin sanin abinda zata yi. Ashraf ya ce, Ban shiryawa zama uba ba a yanzu sai zuwa wani lokaci, bani bu atar na yi shawara dake wajan zubarwa ko barin sa ya rayu. Amma ai a jikina yake, kuma ni ce zan ji ciwo a lokacin da za a yi aborting ko?. Yanzu wanne ciwo ki ke ji? Abortion ki ka yi a Texas ba a nigeria ba, na tabbatar bakya jin ko wanne ciwo yanzu saboda sun cigaba wajan kawar da ciwo. So kar ki damu. Narma ta ce, na gaji da zama da kai, ha urin da nake yi saboda wani dalili nawa ya are, zama na a Texas ya are. Wayata da ka auke da passport ina dole ka dawo min dasu na bar asar nan. Wajan iyayena zan koma, dole a raba auren nan, bana son sa ko ka Za a raba auren da zarar na kammala abinda nake yi dake, har yanzu ban gama morar ki ba shiyasa bazan bari ki yi ciki ba. Akan me zan bar ki ki yo ciki? Kina yin ciki zai canja min halittar da nake matu ar sha awa a tare dake, ni kuma bana so abinda yake burge ni a jikinki ya gushe. Narma ta kawar da kai hawaye na sakko mata ta goge ta ce, Duk su Dad ne suka jawo min wannan damuwar, da sun bar ni da wanda nake so duk da ba haka ba. Ina son Faruk, Ina son Faruk! Ta furta a hankali tana kallon wani waje daban. Shi an daban yana sonki ne?. Yana sona, na tabbatar bazai yi abinda zai cutar dani ba. Zan bani dukkan farin ciki, zai bani abinda nake so bazai sani ni kuka kamar kai ba. Ya yi murmushi ya ce, Kina da tabbacin shima son gaskiya yake yi miki? Kina da tabbas akan yana jin sonki a zuciyarsa?. Kallon sa tayi da mamakin kalamansa, ya age kafa a ya ce, eh mana, ai ke kafin ki fahimci wanda yake sonki tsakani da Allah zaki jima wallahi, saboda da yawan mu duk sha awar ki muke yi ba so ba. Me ka ke nufi?. Abinda nake nufi a bayyane yake, nima da farko na auka Ina sonki ne sai bayan na mallakeki na fahimci ba so ba ne. Daga lokacin na fahimci wani abu da yake a tare dake ne yake burge ni ba zuciyarki ba ya fa a yana mi ewa tsaye tare da kallon ta ya ce, tunda dai kin samu lafiya zan je na same su si yi discharging na ki su ha a miki drugs mu wuce gida, bazan iya zama a nan har gari ya waye ba, kar ki manta zan dau i azumi ya fa a yana fita daga akin ya barta tana kallonsa zuciyarta a cushe babu da i kwata-kwata. *Abuja.* Ni fa shirun nan Narma yana saka ni damuwa, ya kamata a san abinda za ayi gaskiya Mum ta fa a tana kallon Dad da yake zaune shima. Najwa ta ce, gaskiya Mum shirun ya yi yawa, ko a waya ba a samun ta sai dai in ka kira shi. Wanne irin zaman lafiya ne wannan da zai saka ta daina amfani da waya? Kowa ya san Yaya da social media, kwana biyu har cigiyarta ake yi saboda tashin ganin update inta. Mum ta kalli Dad ta ce, Ka ji ai, ya kamata a san abinda ya kamata ayi gaskiya. Ni na gaji da shirun nan ban amince lafiya lau suke ba wallahi. Zan sake komawa domin na gano halin da take ciki. Dad ya ce, ni kaina shirun nan ya dame ni, Narma babu waya, babu social media ai kamar babu rayuwarta ne. Gaskiya akwai abinda yake faruwa. Mum ta ce, bara na kira shi, su na san yanzu dare ne sosai ta fa a tana aukar waya ta kira wayar Ashraf. Ashraf ya auka daga can angaren ya ce, Mum barka dai. Mum ta ce, Barka Ashraf, ina Daughter take?. Ashraf ya ce, Bacci take yi, bata jin da i ne muka je asibiti aka bata magani. Amma yanzu bacci take yi. Mum ta ce, me yake damunta haka?. babu komai, ciwon kai ne. Ina wayarta?. Cewa take yi bata bu atar amfani da waya shiyasa kwana biyu gaba aya ba a jinta. Ta ajjiye wayar gaba aya ta daina amfani da ita kwata-kwata. In ta farka ka tabbatar ka kira ni ka ha a ni da ita, bazai yu ta ajjiye waya a daina jin ta gaba aya ba. Ka kira ni video call in ta farka. Ashraf ya ce, To Mum in sha Allah. Daga nan ta yanke wayar ta kalli Dad ta ce, gaba aya hankalina ya kasa kwanciya da wannan Ashraf in, Ina ganin kamar akwai abinda yake yi mata shiyasa ko yaushe in aka kira sai ya dinga kawo excuse. Anya bazan tura Najwa zuwa can?. Dad ya ce, ki jira ayi waya da ita in, in akwai damuwa sai a tura ta, in babu kuma shikenan. Mum bata ce komai ba Dad ya ce, Na san Ashraf bazai yi abinda zai cutar da ita ba, yana sonta kuma yana aunarta sosai, kuma yana da ilimi ya san abinda ya kamata ace ya yi. Mum ta ta e baki ta ce, ashe wannan an daban ya yi aure, azu nake gani a social media wai an kaiwa matarsa hari har cikin gida. Dad shima ta e bakin ya yi ya ce, na gani nima, ai ba abin mamaki bane ko kashe matar tasa aka ce anyi, Mahaifin da bai san darajar kansa da ansa bane zai bawa wannan mahaukacin auren arsa. Mum ta ce, da mun biye ta haukan Narma da yanzu itace a wannan hali. Allah ka tsare faruwar hakan ko a mafarki. Dad ne akwai ya amsa da amin ban da Najwa da ta san da gaske Yayarta tana son sasai, ta tabbatar har gobe tana aunar kasancewa dashi da zuciyarta. ****** Nayla haka ta cigaba da rayuwa a gidan mijinta Omar, magana bata shiga tsakani su har gwara yanzu, in ta gaishe shi ko ta yi masa barka da shan ruwa yana amsawa, amma kafin ta ganshi in ma ana jimawa sai dai ta ji motsinsa kawai. angaren business ana ta kai takalma Kaduna, ana siyarwa ana kuma bada ku i kamar yadda Nayla ta tsara, ita da Bashir suke yi ba tare da ya san ma ana yi ba har lokacin. Haka ma aikatan su na wajen aiki suna siya sosai daga hannunta shima ba tare da san ana yi ba. Kasancewar aramar sallah ta gabato mutanen Kano kwasar takalma kawai suke yi, abinka da an Kano basu iya yayin abu ba, siyan takalman ake yi domin sallar bana wankan su za a yi. Daren ashirin da bakwai ga watan ramadan yana zaune yana addu a wannan dare mai matu ar falala da lada da kuma amsa addu a, addu a yake yi sosai domin shigarsa islamiyya da yake karatu online ta ara masa sani akan abubuwan da bai sani ba a baya. Ya ara ilimi ya kuma san addu i da yawa da matakan amsa addu a. Yana zaune yana jerawa Allah bu atarsa sai yake jiyo kamar sautin kuka daga falon. Katse addu ar ya yi ya taso ya fito ya shiga aramin falon da take zama ko yaushe dan ganin lafiya take kuka. Itace in kuwa take kuka amma cikin addu a, ta yi sujjada tana kuka mai ratsa zuciya babu wanda ya san abinda take fa awa wanda ya haliccita sai shi kawai. Wani irin rauni Omar yaji wanda bai ta a jin sa ba a rayuwarsa, lokaci aya zuciyarsa ta shiga bugawa da arfi ba tare da ya san dalilin da ya kawo hakan ba. Ya bita da kallo cikin wani yanayi da bai san meye ba, shi dai ya san ya tsaya yana kallon ta amma bazai ce ga dalilin kallon ba. Ba a bayyane take addu ar ba dan haka bazai ce ga abinda take cewa ba, shidai yana jiyo shashshe ar kukanta. Gaba aya sai ya rasa kuzarinsa ya kasa daina kallonta, gashi dai ba fuskarta yake gani ba amma ya kasa auke ido daga kanta. agowa ta yi daga sujjadar ta kifa kanta akan hannayenta tana cigaba da kuka. Da yar ya iya jan afarsa ya koma ya zauna akan sallayar ya cigaba da ta sa addu ar cikin rauni. Ba tare da ya sani ba ya tsinci kansa yana ro on Allah ya yaye mata duk abinda yake damunta ya bata abinda take so. Lokacin sahur ne ya yi gashi ya manta bai shigo da fruits ba kamar yadda ya saba sha, hakan ya saka shi ya taso ya fito ya kalli inda take taga tana shan ruwa. Tambayar kansa yake yi ita bata sahur ne? Bai ta a ganin ta tana cin abu ba sai dai ya ga tana shan ruwa. Bai tambayeta ba ya sha kawai ya koma ba tare da ya ce mata komai ba. Washe gari da safe da arfin guiwa ta tafi aiki, ji take kamar Allah ya amsa mata dukkan addu arta, ji take komai ya wanke daga zuciyarta kamar ta samu duk abinda ta tambayi mahaliccinta a daren jiya. arfin guiwa take ji da karsashi tun a daren jiya, shiyasa ta saka a ranta komai ya zo arshe. Tunda ta fita take bada sadaka cikin fariin ciki har arasa wajan aiki. Da wuri ta gudo daga wajan aiki ta wuce saloon a inda suke zuwa ita da Salma in tazo Kano. Gyara mata kai akayi da gyaran afa harda facial, ta bar wajan da niyar zata dawo washe gari ayi mata black henna. Maimakon tayi gida kawai sai ta wuce gidan Abba, ta san duk shekara yana ha a shan ruwa ranar ashirin da bakwai ga wata. Bata ta a zuwa ba, yawanci ko yaushe tana Kaduna ko tana Saudia shiyasa wannan karon tayi udurin zuwa tunda tana Kano. Kowa da ya ganta ya yi farin ciki musamman yadda take walwala tana ta tsokanar mutane ana dariya. Da ita aka sha ruwa dan su Mama Sa adatu duk suna wajan har Abbas. Da farko ta an