← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 205

Sashe 12

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

are. Nayla ta ce, haka ne Didi. Hira suka yi da Didi sosai kafin ta kashe ta tashi ta koma ciki dan har lokacin bai dawo ba. Da yamma annen Salma suka zo, Nayla ta ji da i sosai sun sha hira sai da suka yi sallar magriba sannan suka wuce gida har lokacin Omar bai dawo gidan ba. Shi kam Omar gidansu ya wuce ya cigaba da abinda yake yi, yana yi yana mita yana cewa, Gaba aya bana sakewa a can gidan, ban sani ba ko dan komai na gidan nata ne oho. Ta saka min ido, Ina yini, ga abinci, sannu da zuwa. Mtsww! Na ce mata ina son gaisuwa ne? Ko ance ina son magana da ita ne?. Gaba aya bana sonta! Ya fa a yana cigaba da yanka da sample in takalmin hannunsa sai kuma ya dafe kai. Numfashi yake saukewa a hankali ya ce, na tabbatar rashin son da nake mata ne ya saka na kasa sakewa. Narma ce ta zo zuciyarsa sai kawai ya yi tsakin da bai san dalilinsa ba ya cize baki yana cigaba da sauke numfashi a hankali. Wayarsa ya kalla yaga sunan Didi a bayyane ya ce, sarkin takura ko ne zata ce min oho. Bazai iya aukar wayarta ba duk fushin da yake yi da ita, hakan ya saka ya auka ya saka a speaker ya ajjiye a kusa dashi ya ce, Wanne dolen za a sake yi min?. Didi tayi dariya ta ce, Haba Omar Tiger, Ko gaisuwa babu?. Kwana biyu bakya bu atar gaisuwar ne. To naji. Ya amarya?. ya bata amsa a ta aice. Didi ta ce, Omar kar fa ka cutar da yarinyar nan, ha in kula da ita yana kan ka na fa a maka. Ikon Allah, me kuma akace nayi?. Babu abinda aka ce ka yi, ina tuna maka ne kawai. Duk wannan sadaukar da rayuwar tawa da nayi saboda auren ba a gani ba? Me ake so nayi kuma?. Didi tayi dariya jin wai ya sadaukar da rayuwarsa ta ce, kayi namijin ari Omar. Yanzu kana ina?. Gidan mu. Omar zaman wannan gidan fa ba naka bane, ga gidanka can da ka biya kudin hayarsa zaman me ka ke yi a nan?. Gaba aya kayan gidan nata ne, takura nake yi bana sakewa ko ka an. Ta cika saka min ido, ina kwana, ga abinci. Na ce mata ina so ne? Bana son shishshigi kema kin sani. Didi ta ce, Omar matarka ce fa, yanzu kenan ko gaisuwar baka amsawa ko?. Omar ya ce, to na saka ta ne? Da ki ke zancen matata ce ni na ce ina sonta a aura min ita ne?. Ban ta a cewa ina sonta ba, kuma har gobe bana sonta. Didi ta kwantar da murya ta ce, amma dai ba haka ka ke ce mata baka sonta ba dai ko?. Kamar tana gabansa ya wara idanu ya ce, To in na ce laifi na yi? Kaji Didi da wani abun, dan na fa a mata bana sonta ai ba arya nayi ba, bana sonta kema kin sani. Na kar a ne saboda ke, li a min ita akayi ta dole ba dan ina so ba. Didi ta ce, kar dai ka fa a mata haka, ka cigaba da ri ewa a zuciyarka har lokacin da zaka so ta Hmmm! Shine abinda yace. Didi ta ce, Ina fatan kana kula da abincinta ko?. Jaririya ce ita?. inta ne a kanka. Bani da wannan lokacin. Omar ka sassautawa zuciyarka wannan zafin kan, Ina sake fa a maka akwai ha inta a kanka kaima ka sani. Sai kuwa ta fusata shi ya ce, Sai maimaita min batun ha i ki ke yi me ki ke so nayi nata? A baki ki ke so na bata abincin ko farka cikinta zan yi na zuba mata?. Ke ki ka ce min gidansu an kaita da abinci, to me zanyi kuma? Sun nuna min ni ban isa na ciyar da arsu ba, sun nuna min bani da ku in da zan iya ciyar musu da a shiyasa suka kaita da abincinta, ba sai ta ci abincin gidansu ba ita ka ai ba? Lallai sai na kula da abincinta!?. Didi ta ce, maida wu ar Omar, abincin da aka kaita da shi daga gidansu shi ake kira da gara, a al ada ba laifi bane kuma ba anyi dan ka gaza bane al adar malam bahaushe ce. In zaka tuna kaima lokacin bikina na kar i ku i a hannun ka nima kayan abincin na siya na je dashi, bawai dan mijina ya gaza ake yi ba sai dan al adar bahaushe ace a haka.
Chapter 12 · 0% Book details