← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 205

Sashe 27

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mana kyauta, an yi mana inkin sallah kowa guda biyu da ku inki, sannan ga takalma an bamu. Kuma tsakiyar ramadan ya bada ku i ya ce kowa ya kai gidan su, sannan ga sallamar azumi da aka yi mana mai kauri, a taya mu godiya, Boss ya yi mana komai a rayuwar nan. Nayla ta an yi murmushi tana aiyyana baka san ka fini daraja a wajansa ba shiyasa ka ke fa a min haka. Ta daure ta ce, Kun gode. Kuma Antyn mu baki san wani abu ba ba, Boss fa mutane ne suke ganin sa haka, amma bala in sau in kai gare shi, sannan Kai!! Omar ya fa a cikin tswar da ta saka Bashir yin shiru yana kallonsa. Hannunsa ya juya alamun tambaya sannan ya ce, Meye na maganar!? Ya sake fa a cikin tsawa sosai. Bash ya ce, Tuba nake. Fita! Ya fa a yana nuna amsa ofa Bashir ya mi e sum sum sum ya fice. Nayla zata bar wajan ta ji ya ce, meye na biye masa kuna surutu? Bakya ganin Ina wajan? Sai an saka min ciwon kai?. Nayla jin yadda yake maganar a fusace sai ta kalle shi tana mamaki abinda ya fusata shi a cikin maganarta ko ta Bashir. Nayka ta ce, ka yi ha uri. Ta fa a ta koma ciki tana cewa, masifaffe kawai. Bata sake ganinsa ba sai gab da shan ruwa ta fito dining dan ranar a kai ta jera abinci saboda ta ci son ranta. Ta kuma yi aniyar yi masa tayi koda zai dizgata sai tayi, tana so ta samu lada tunda ramadan in ya are, babu tabbacin zata kai mai zuwa da rai. Shigowarsa ta gani yana waya kamar ko yaushe, sai da ya gama wayar sannan ta ce, Sannu da zuwa YaMar, Ga abincin shan ruwa na ajjiye maka, don Allah kar ka ce baka ci, kaga daga yau an gama azumi, don Allah! ta arasa fa a tana karyar da murya cikin shagwa a. Yadda ta ce YaMar in a ha e sai sunan ya bada wani salo mai dadi, ta cire harafin farko ta fa i na arshe, sannan ta ha e shi waje aya da Yaya. Omar abubuwa ne masu yawa suka ha ar masa a lokaci guda suka daki zuciyarsa, sai da ya runtse ido jin abun da arfi kamar an saka abu mai nauyi an daki irjinsa. Na farko bai san meyasa indai zata ce masa Yaya Omar ba sai ya ji sunan har cikin ahon zuciyarsa, bai sani ba ko dan bashi da mai fa a masa Yaya ne sai ita in shiyasa yake jin haka oho. Na biyu kuma yadda take yiwa sunan iyayi wajan fa a yana yi masa da i, duk da ta bashi dariya dan gaba aya bata iya furta harafin R ba, da ta ce Mar in sai harafin R in ya tashi kamar wani harafin daban ta fa a. Na uku yadda ta ke yi maaa shagwa a tana wani kwa e fuska ya dake shi sosai. Kallon ta yayi ya ga ta sunkuyar da kai tana jiran amsarsa ya dake ya kawar da abinda yake ji ya ce, baki fa a min ku inki ba. Nayla ta ago dan wallahi ta manta da batun ku in, ta sake mayar da kai asa tana wasa da hannunta ta ce, Na manta wallahi, amma zan yi lisaafin. _Ji ta harda wallahi, ko meye na rantsuwar oho._ ya fa a a zuciyarsa ba tare da ya furta komai a fili ba. Nayla ta ce, Don Allah YaMar ka ci abinci yau. arin wucewa yake yi ya ce, na ce ina so ne? Ba na ce babu ruwanki da lamarina ba?. Baka ce kana so ba, kyautatawa ce nake so nayi maka. Kuma kaga yau azumin arshe daga yau sai wata shekarar ga masu yawan rai. Wata ila kafin shekarar ta dawo na mutu bana duniya, ka ga ko babu komai zaka tuna ka ce ranar azumin arshe na last year ni na baka abinci, kaga zan samu lada a cikin kabarina. Don Allah YaMar ta fa a a sanyaye. e baki ya yi ya wuce ciki Nayla ta yi ajiyar zuciya cike da mamakin sa da bai yi mata masifa ba, ki cigaba da shige masa Hauwa, in ya make ki wata ran ke kika jiyo. Sai tayi dariya ta zauna akan dining din ta lumshe ido tana addu ar gab da shan ruwa. Hawaye ya sakko mata tunawa da shikenan ramadan ya are, babu tabbacin zaka kai wata shekarar gashi ka yi azumin baka da tabbacin an kar i wanda ka yi. Rauni taji a zuciyarta ta dinga hawaye tana addu a har aka yi kiran sallar magriba. Ido ta goge ta sha ruwa ta yi ajiyar zuciya ta furta, Allah ya maimaita mana. Cincin in da tayi ta auka ta saka a baki tana ci kafin ta shiga ciki da niyar yin sallah. (Addu ar gab da shan ruwa, addu a yayin shan ruwa mustajaba ce bata da hijjabi a wajan Allah. Ba sai axumin farilla ba ko azumin nafila ne in aka kai a daure a yi addu a ko ya take. Akwai falala mai tarin yawa a cikin wannan lokaci, sannan addu a bata da hijjabi da ka yi da Allah ya amsa. Allah yasa mu dace ya amsa mana dukkan addu ar mu amin.) Shima ruwan ya sha sannan ya fito ganin bata falon bai neme ta ba ya fita dan yin sallah. Tana zaune tana shan tea ya dawo sai ta ga kamar bashi da lafiya dan gaba aya kamar ba shi ba, fuskarsa ta an yi ja kuma jijiyar kansa ta tashi, idanun sa sun an yi ja ka an, ga yanayinsa babu arfi sosai kamar mai zazza i. Rauni taji ya sake mamaye zuciyarta ganin ya zauna a falon ya jingina da kujera ya kulle ido. Nayla zuciyarta umarni take bata ta je ta kai masa abinci, wani angaren na zuciyarta kuma yana hanata aikata hakan. arfin guiwa ta samu ta fara ha a tea, ta tuna Didi ta ce mata yana da shan madara sosai kuma yana shan sugar. Ta ha a tea in da tosted bread ta ha a komai a tray ta tako a hankali ta ajjiye akan table in da yake kusa dashi. Yana jinta amma bai motsa ba dan kansa ciwo yake yi sosai. YaMar ga abincin. Bai motsa ba balle ya kalle ta, ta koma ta zauna tana cigaba da cin nata amma gaba aya hankalinta yana kansa har lokacin bai motsa ba. Sai ta ji abincin ya fita daga ranta ta taso tazo nesa dashi ta tsaya ta ce, YaMar baka da lafiya? Ka ci abinci sai ka sha magani. Idanunsa a kulle bai ce komai ba amma yayi mamakin yadda ta fahimci bashi da lafiya lokaci aya. YaMar! Ta sake fa a a hankali a tausashe. Idanu ya bu e ya kalle ta ganin yadda idanunsa suka yi ja sai gabanta ya fa i a rikice ta ce, YaMar baka da lafiya ko? Idanun ka sun yi ja sosai, Ciwon kai ka ke yi?. A hankali ya janye idanun sa daga kallonta ya mayar da ido ya rufe. Sallama ta ji ana yi ta kalli wanda ya shigo da alama aiken shi ya yi shiyasa ya bar ofar a bu e, ta amsa sallamar. Tk ya shigo ya ce, Sannu Damisa, ga maganin ya fa a yana ajjiye masa a kusa dashi. Kallon Nayla ya yi ya ce, Antyn mu mun ga sa o, Allah ya saka da Alkahiri. Da amin akwai ta amsa dan gaba aya hankalinta yana gare shi. Ajjiye wata ledar ya yi ya ce, Ba a samo ayaba, amma ga apple in nan. Daga haka ya fita daga falon. Maganin ya auka zai sha da sauri ta dakatar dashi ta ce, Don Allah ka sha koda tea ne in yaso sai ka sha maganin, babu abinda magani zai maka bayan tun jiya baka ci komai ba ta fa a kamar zata yi kuka tana kallonsa. _Ya Allahu! Me yarinyar nan take son mayar dani ne? Gaba aya ta shiga rayuwarta na rasa meyasa nake jin maganarta har cikin kaina._ ya fa a a zuciyarsa jin maganar Nayla har cikin zciyarsa. Nayla ta auki tea in ganin bai ce komai ba ta mi a masa ta ce, Ka sha don Allah. Ji yake kamar ya kar a ya watsa mata a jikinta, tabbas da Omar in da ne abinda zai aikata kenan, amma yanzu ya rasa meyasa yake jin abinda yake ji akan yarinyar. Don Allah YaMar ka kar Ta sake fa a a sanyaye tana sake mi a masa. Kamar wanda aka bawa umarni ya mi a hannu ya kar a kamar yadda take bashi. Da yake babu zafi sosai tunda ta an jima da ha awa ya kai bakinsa ya sha a hankali. Duk da bashi da lafiya amma tea in ya yi masa yadda yake so, ya yi mamakin yadda ta iya ha awa daidai da ra ayinsa. Nayla ganin ya shaa sai taji farin ciki ya mamaye mata zuciya, rana ta farko da ya ci sha wani abun na cikin gidan bayan ruwa. Zata iya cewa abu na farko kenan ma da ya fara amfani dashi a gidan shine mug in hannunsa. e tea in ya yi bai sake sha ba, ya rufe ido ya jinginar da kansa a jikun kujera. Nayla ji take kamar tayi kuka saboda rauni, ta zuba masa ido tana kallonsa kamar ta cire ciwon ya dawo jikinta, Abin ka da abinda zuciya take so. Kafin ta yi magana ya sake shan tea in sannan ya ajjiye. Magani ya auka ya alla ya saka a baki, da sauri ta bashi ruwa a glass cup ya kar a ya sha ya ajjiye. Kulle ido ya sake yi ya yi shiru bai ce komai ba. Nayla tea in ta auke da ruwan da ya gama sha ta kai dining ta dawo a hankali ta ce, YaMar ka ci koda irish in nan ne aka ji da i, ka ga baka ci komai ba tun jiya. Bai ce komai ba ta zauna nesa dashi tana kallo kamar
Chapter 27 · 0% Book details