Sashe 91
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ji ana yi, ya shiga ban aki ya yi alwala ya fito ya fita zuwa masallaci. Har ya dawo bacci take yi bai tashe ta ba ya zauna dan har lokacin ba shi da wani arfin jiki yadda ya kamata. Nayla bata farka ba sai bayan sallar i'sha, da ya dawo daga sallah ya tsaya suna magana da Bashir sannan ya shigo ciki ya tarar itama ta idar da sallah tana zaune akan sallaya. arasowa ya yi inda ta ke zaune, a lokacin ta mi e ta zauna a kan gadon a hankali, shima ya zauna a kusa da ita ya ce, "Bacci ba ya yi miki wahala." Sunkuyar da kai ta yi bata ce komai ba ya ce, "Me zaki ci?." Nayla ta yi shiru bata amsa ba, ya sake maimaitawa a hankali ta ce, "Babu." Omar ya ce, "ki dai tuna." Nayla ta ce, "bana jin cin komai, amma....." sai ta yi shiru bata arasa ba, ya zuba mata ido yana kallon ta ya ce, "uhum, ina jinki." Nayla ta ce, "Ina sha'war shan fura da nono." Ya girgiza kai ya ce, "to zaki samu, ki jira na je na kawo miki...." Ta aga kai alamun to, ya sake kallon ta ya ce, "Na so abinci ki ka ce kina so, da na dafa miki da kaina, amma ki bini bashi" ya fa a yana murmushi ya tashi ya fita. Nayla ta yi ajiyar zuciya ta bishi da kallo tana mamakinsa, gaba aya ya canja mata, ya tashi daga Omar in gidan Didi ya koma mata wani daban wanda bata san shi ba, ya koma mata kamar wani ruwan sanyi, ya koma mata kamar abokin wasanta, ko yaushe cikin murmushi yake kamar ba shine kullum fuska a aure yana harararta ba. Ko dan ya saka ta jinya ne ya koma haka bata sani ba. Babu jimawa ya dawo da leda a hannunsa, ya shigo akin ya zauna ya ce, "to gashi" ya fa a yana bu e robar ya mi a mata. Mi o hannu tayi zata kar a sai ya ga hannun nata kamar yana rawa, ya dakatar da ita ya ce, "barshi ba sai kin ri e ba, zan baki da kaina." Kamar yadda ya ce in kuwa shi ya bata furar da kansa, ta sha da yawa dan ka an ta rage ya ajjiye. A sanayaye ta ce, "kai baka so?." Kai ya girgiza bai ce komai ba, Nayla ta ce, "meyasa?." Ya kalle ta suka ha a ido ta sunkuyar da kai ya ce, "Bana jin yunwa." "Don Allah ka sha, kaima baka da lafiya." "Ni waye ya ce miki bani da lafiya?." "Ni na san baka da lafiya, har maganarka ta canja kamar wanda yake mura." "Tunda baki da lafiya nima bani da lafiya, amma yanzu bana jin yunwa ban sani ba ko anjima." Shiru tayi bata ce komai ba tana wasa da hannunta, ya kalle ta sai ta suka ha a ido sai rufe ido kafin ta bu e a hankali ta ce, "Ban ga wayata ba yau gaba aya." Kan madubin akin ya kalla ya ga wayar, ya tashi ya auko mata ya mi a mata bai ce komai ba. Kar a tayi ta ga kiran Salma da na Jidda har da na Mama da Ya J. Nayla ta girgiza kai ta ce, "ana ta yi min waya" ta fa a tana ajjiye wayar a gefenta. Shiru ta ji bai ce komai ba itama haka. Shirun ya ratsa akin kafin ya ce, "Yaunzu ya jikin? Didi ta ce min na tabbatar kina shiga ruwan zafin nan kuma kina shan magani. Ki fa a min in kin samu sau i?." Nayla ta kulle ido bata ce komai ba, dan ya bata kunya musamman da ya saka Didi a maganar. Shiru ya biyo ba ya bai ce komai ba itama bata ce komai ba. A hankali ta ce, "Ya Didi ta je gida? Ka kira ta?." Ya aga kai ya ce, "uhum na kira ta, tana gaisheki." Ta aga kai bata amsa ba, ya lumshe ido ya bu e a kanta yana are mata kallo. Abin mamaki yake bashi, wai shi da wata mace yanzu babu wani sauran abinda ya rage, ya zama ita ta zama shi, ga tarin soyayayr da yake mata wacce bai san adadin yawan ta ba. In aka ce hakan zai faru a rayuwarsa zai ce arya ne, amma gashi ya faru cikin ruwan sanyi, kuma jikinsa da zuciyarsa sun kar i abun hannu biyu. ago ido ta yi jin shiru ya yi yawa ta kalle shi suka ha a ido alamun kallon ta daman ya ke yi, ta yi saurin sunkuyar da kai. Murya a asa ya ce, "meyasa baki son kallona?." Tayi shiru bata amsa ba ya ce, "meyasa." Jin ya maimaita sai Nayla ta ce, "bana iya kallon idanunka, kuma kunyarka nake ji" ta fa a tana rufe fuska da hananyenta. Murmushi ya yi mai sauti ya ce, "kunya!...." Ya sake murmusawa ya ce, "A karo na farko a rayuwata na ji wani abun kunya, ban ta a ji ba sai azu da Didi take min bayani akan arnar da na yi a jikinki. Sai na ji nauyinta sosai, amma daga nan komai ya wuce." Kalamansa ya sake bata kunya sosai, ta runtse ido cikin kunyarsa da kuma kunyar Didi da kunyar abinda ya faru. Bai lura da yanayin ta ba ya an yi murmushi ya ce, "Ni fa a kanki na aikata abubuwan da ban ta a aikatawa ba a rayuwata. Tunda ki ka shiga rayuwata abubuwa suke ta faruwa dani wanda basu ta a faruwa ba sai a kan ki kawai." Ta ago a hankali ta kalle shi ya aga gira ya ce, "Na lissafa miki?." Kai ta aga alamun eh, ya matsa kusa da ita ya ri e hannunta cikin kasalalliyar murya ya ce, "ke ce mace ta farko da Didi ta ta a yi min fa a a gabanta...." Ya dakata da maganar saboda ar dariyar da Nayla tayi alamun ta tuna. Bata yi magana ba sai auke kai da tayi ya ce, "Da gaske kece ta farko, ni ba a yi min fa a a gaban kowa musamman baki. Abu na biyu kuma na ce zan auki mataki a kanki akan hakan amma sai na kasa aikatawa, amma da wata ce ba ke ba har abada bazata sake marmarin zuwa gidanmu ba, kin dan waye Tiger a baya ba sai na fa a miki ba. Abu na uku; a kanki Didi ta ce na fita na bata waje, hmm...! lokaci daga Abuja na dawo, ko sannu da zuwa bata ce min ba. Na ji haushinki sosai, ina mamakin meyasa ki ke shiga rayuwata ne har haka?. Na uku; a kan ki ta ce min ina shirme, kuma ke ce ki ka yi min korar shai anu ban auki mataki ba." ar dariya Nayla ta sake yi tunawa da abinda ya faru, sai ya dakata da maganar yana kallonta ganin tana dariyar da ta auki hankalinsa. Ya yi shiru bai ce komai ba, ta kalle shi suka ha a ido ya ce, "Kuma tun farko kece wacce Didi take yawan saka ni a lamarinta, haka kawai in ki ka shigo ki ka fita sai ta fara labarinki, sai na ji haushi na ce wai wannan wacece ne da zata wace min Yayata?. Ke ce mace ta farko da ki ka fara bani kyauta na kar a har na yi amfani dashi, kin bani kyutar azurfa gata a hannuna, kin bani kyautar turare har yanzu na kasa arar dashi saboda son da nake masa, kin bani kyutar riga wacce da ita na kwanta a asibiti a jiya." Hannunsa ta kalla ta ga azurfar kuwa tana nan, ta ora hannu a kai ya ri e hannayen nata ya ce, "Kece mace ta farko da na fara jin nauyi da girman iyayenta a duniya, a gaban Abiy na kasa samun sukuni, nauyinsa ya rufe min idanu, na rasa abinda nake ji. Ke ce mace ta farko da ki ka fara kirana da Yayaaaa!" Ya an sauke numfashi ka an ya ce, "Ya ilahii......!har yanzu na kasa manta lokacin da mu ka je g danku, ki ka ce Yaya Omar Allah ya kiyaye hanya, a daidai lokacin hawaye ya sakko daga idanunki kuma kina murmushi. Kin tuna?." Wasu hawayen ne a idanunta, ta aga kai alamun eh ba tare da ta kalle shi ba ya ce, "kina lissafawa dai? Ni na ata a lissafin." Bata bashi ba amsa ba ya ce, "kece mace ta farko bayan Didi da na ci abinda ta sarrafa, Didi ta fa a min lokacin da ki ka dafa awara na ci har naji tayi min da i. Jidda ke ce mace ta farko da na kar i aurenta, ke ce mace ta farko da na zauna da ita a gida aya, kece mace ta farko da na ke shiga lamarinta har na saurereta. A kan ki na fara jin kishi tun ban san ina sonta ba, ke ce mace ta farko da na kwana a gado aya da ita, ke ce mace ta farko da na damu akan rashin lafiyarta, ke ce mace ta farko da na ji a raina in wani abun ya same ki bazan ji da i ba" ya sauke ajiyar zuciya ya matse hannayenta, ya sake yin asa da muryarsa sosai ya ce, "Ban ta a karya rantsuwa ba, in na rantse na rantse kenan bana canjawa, shiyasa ban cika yawan rantsuwa a rayuwata ba, dan babu halitttar da ta ta a karya min rantsuwa. Ke ce mace ta farko da rantsuwar ta karye ta dalilinki. Ke ce mace ta farko da na ji a raina in na rasa ta bazan iya rayuwa ba, ke ce mace ta farko da na furta mata kalmar ina sonki, ke ce abu na farko da na ce na bar shi amma na kasa bari, ke ce ta farko da nake tsananin auna, nake ji kamar na mayar da ke zuciyata. Ashiqaty!" Ya furta can arshen ma ogwaro yana kallon idanunta. Shiru ya sake yi yana kallon ta, zuciyarsa na cigaba da antayo kalamai kan harshensa ya ce, "Ke ce ta farko da na san meye so a kanta, na banbance