← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 205

Sashe 117

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta hanyar da zaki bi dashi ya ha ura ko da bai yi niya ba. Ina zafin kan da yake ji dashi? Duk ya tattara ya ajjiye saboda son da yake miki, dole wani lokacin ya motsa tunda halinsa ne, hali kuma baya canjawa. Masifa, tsawa, da fa an duk suna nan, yanzu sun je hutu ne saboda amarci, gashi tun amarcin bai yi nisa ba sun fara wasa ofa. Sai kin cigaba da ha uri kawai, sannan ki san yadda zaki saka ya sauke ko baya so." Nayla ta yi shiru kana ta ce, "Didi wani lokacin baka gane kansa gaba aya, yanzu zaki ganshi fari anjima ya koma ba i." Didi ta dinga dariya ta ce, "Kar ki bani kunya mana Nayla, ai na auka kin gama karanta Omar kin haddace ashe har yanzu da saura. Halinsa bazai canja ba, abinda zaki yi kawai ki koya kan ki jurewa akan halin nasa shikenan an zauna lafiya." Nayla bata ce komai ba sai ar dariya da ta yi, Didi ta bita da kallo tana murmushi kafin ta ce, "ke kar ki damu, ki jira ya dawo ki san duk yadda zaki yi ki bashi ha uri ni na san zai ha ura. Omar din har wata tsiya ce a hannunki? A waje yake Omar amma a wajanki bai wuce jaririn da zaki sarrafa shi yadda ki ke so ba. Gaba aya ya susuce a kanki, tafiyar nan da ki ka yi rasa sukuni ya yi, ya kira ni kamar zai min kuka shi wallahi gidan baya masa da i bakya nan, na ce haka zaka yi ha uri harta dawo. Yana yi miki wannan son ki kasa amfani dashi wajan saka shi ya daina fushi?." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba Didi ta ce, "ki yi amfani da hikima a matsayinki na a mace ki san abinda zaki yi wanda in kika yi kin san yana jin sa a zuciyarsa, da wannan abin zaki kama shi har ya ya daina fushin." Nayla ta kalli Didi bata ce komai ba, Didi ta ce, "ki gane inda nake nufi, kar na fito miki free ki ce bani da kunya, amma na san kin fahimci karatun yanzu." Nayla tayi dariya tare da rufe fuska da hannunta. Didi ta yi dariya ta ce, "kyayi dariya ai. Ki wahalar dashi, ki rama share ki in da ya yi. Ni bana so ki dinga yale shi wallahi, ban ce ki raina shi ba amma in ya share ki ki share shi, da afarsa zai zo inda ki ke. In shi ya tashi yanka miki wula anci bazai raga miki ba, rufe ido zai yi kamar bai san ki ba, dan haka kema kar ki raga masa." Nayla ta sake yin dariya Didi ta ce, "kar ki ce shawarar banza nake baki, na yi shiru" ta fa a tana dariya itama Nayla dariyar take yi kafin ta ce, "to Didi, zan yi duk abinda ki ka ce." Didi ta ce, "Allah na tuba fushin Omar har wani fushi ne? To akan rashin dalili ma fushi yake yi." Nayla ta yi murmushi ta ce, "Didi ban kawo miki ruwa ba" ta fa a tana tashi tsaye Didi ta ce, "Daman kina ta kuka ta ya zaki bani ruwa?." Murmushi tayi ta kawo mata ruwa ta ce, "Me zan dafa miki?." Didi ta ce, "A oshe nake daga gidan Hajja nake, da bazan biyo ba ma Hajja ce ta ce na biyo mu gaisa, biki zan je." Nayla ta ce, "Bikin wa?." "Mama Zainab ce take aurar da jikarta." Nayla ta ce, "Jika ba ma a ba?." Didi tayi dariya ta ce, "Lallai an gaishe ki, itace mai bin Baba Adamu fa dan kin ganta mai aramin jiki?." Dariya Nayla ta yi ta ce, "Gaskiya dai ma sha Allah kamar ba ita ba, amma meyasa baki fa a min ba ai da na je." Didi ta ce, "Mijinki nake tsoro, babu lallai ya bari sai dai in bai san can za a je ba. Wallahi Nayla babu abinda nake buri da ya wuce Omar ya manta da abinda ya wuce ya fuskanci danginmu amma ya i." Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Kamar yadda ki ka ce na yi masa maganar na gwada, ya ata rai ya ce in dai ina so mu yi fa a na sake maimaita masa maganar." Didi ta girgiza kai ta ce, "Babban tashin hankalina ranar da zai san wannan gidan da yake ciki na Kawu ne. Kawu ne ya bayar kyauta ya ce a matsayinsa na uba ya mallaka masa ya zauna a ciki, saboda tijara da hargaginsa ya saka na ce masa na haya ne, yanzu ya tayar da hankalinsa sai na bashi number mai gidan nan na rasa ya zan yi masa." Nayla ta girgiza kai ta ce, "ai kuwa kafin na tafi Kaduna ma sai da ya yi zancen." Didi ta ce, "Na rasa ya zan yi na fa a masa, in ya san a gidan Kawu yake kwana wallahi daga ranar bazai sake kwana a gidan nan ba, kuma ni da na rufe maganar ya yi ta yi min masifa kenan kamar ya zane ni." Nayla ta ce, "ba sai a yi shiru da maganar ba kawai, ki samu wani ku ha a baki dashi a matsayin gidan nan na shi ne, in ya biya ku in sai ya dawo miki dasu, in yaso duk ranar da ya nutsu akansu sai a fa a masa, amma nima ban goyi bayan ya sani yanzu ba." Didi ta yi shiru bata ce komai ba, Nayla ta auki Marmerh da take bacci. Didi kawar da maganar tayi suka cigaba da hira da Nayla har aka yi sallar azahar. Nayla da ta tuna ta taho da cincin daga Kaduna ta aukowa Didi suna ci tare ya bu ofar ya shigo da sallama. Amsawa suka yi ya kalli Didi bayan ya mayar da ofar ya rufe fuska a ha e ya ce, "Hajiya Didi, saukar yaushe?" Ya fa a ba yabo ba fallasa. Ta yi murmushi ta ce, "Allah ya amsa bakin ka na zama hajiyar nan Omar. Tun azu nazo, ya aikin?." "Alhamdu lillah." "Ya yi kyau, Baka fa a min Nayla ta dawo ba." Ya kalli Nayla da take kallonsa ya auke kai ya kalli Didi ya ce, "Yanzu da ki ka shigo baki ganta ba kenan?." Tayi dariya ta ce, "na ganta mana, wannan ha e fuskar da ka ke yi na meye?." Bai kula ta ba ya auki Marmerh da take jikinta a zaune, sai a lokacin yayi murmushi bai sake cewa komai ba ya wuce aki da Marmerh a hannunsa. Didi ta kalli Nayla ta ce, "Ki je." Nayla ta bu e ido ta ce, "A'a Didi, ki yale shi kawai." Didi ta yi dariya kawai bata ce komai ba. A lokacin ya dawo ya zauna da Marmerh a hannunsa, bai kula kowa a cikin su ba Marmerh yake yiwa wasa. Didi ce suke hira da Nayla sama-sama. Sai a lokacin ya ce, "Didi na rasa me kika auke ni, sai raina min hankali ki ke yi akan gidan nan ko?. Na rantse da Allah na sake yi miki maganar gidan nan daga ranar na daina kwana a cikinsa." Didi ta yi murmushi ta ce, "yi ha uri, in sha Allah dana koma zan turo maka number." Bai ce komai ba ya ora afa kan aya kamar yadda ya saba, babu wacce ya sake kalla a cikin su balle ya yi magana. Didi dai kallonsu take yi daga shi har Nayla, kafin ta yi dariya ta mi e tsaye ta ce, "Omar bani ita na tafi, biki zan je na jikar Mama Zainab." Sarai ya ji me ta ce bazai tanka ba ne sai da ta kar i Marmerh sannan ya ce, "hadari ne a garin nan sosai, dole ne zuwa bikin?." Didi ta ce, "dole ne mana, jikar yayar mahaifiyarmu fa, kamar ni ace ana bikin Marmerh." Kai tsaye ya kalle ta ya ce, "Yayar mahaifiyarki dai, ki daina saka ni a ciki, mahaifiyata bata da an uwa."Didi ta ta e baki tana mamakin halin Omar ta ce, " arya ka ke wallahi, ko baka so Yayar babar ka ce. Biki ne ya zama dole na je." "Addini ne?." "Zai shiga cikin addini Omar, tunda zumunci ne." Ya bita da harara ya ce, "Ke ki ka ga zaki iya ai" ya fa a yana auke kai kafin ya kalle ta ya ce, "tunda ke kika saka kan ki ke ki ka sani, amma in wani abun ya samu Marmerh wallahi ban yafe ba. Ana fa a miki gari da hadari kina sake shirin tafiya, in dan ta ke ce ki je ruwa ya zane ki waye ya damu?" Ya fa a a fusace yana harararta. Didi tayi dariya ta ce, "kome zaka ce sai na je Omar, Da Nayla zan auka mu je tare." "Ta je a matsayin ta nawa?." "Matarka mana." "Ashe babu inda zata je kuwa, indai kin yarda matata ce ko gaisuwar mutuwa." Didi ta ce, "Allah ya yaye maka, ya kawo maka sau i a zuciyarka. Mutum sai ba ar zuciya kamar ta kafurai? Ai duk inda musulmi yake da yafiya aka san shi" ta fa a tana kallonsa ta gefen ido. "Sai ki kafurta ni ai, daga yau ki buga min stamp in karifi." "Ni ban ce ba." "Kima ce mana, in ke kike kar ar ibadata sai ki daina daga yau" ya fa a yana kallon ta fuskarsa a aure. Ta yi dariya sosai tana girgiza kai, ta yi kewar wannan ba ar maganar tasa nesa ba kusa ba. Ta ce, "Musulmi mai kallon gabas yana kai goshi asa da yafiya aka san shi." Bai amsa ba ya auke kai sai kuma ya ce, "ki jira na saka a kai ki, kin ci albarkacin Marmerh, da wallahi sai dai ki je da afa." Didi ta yi dariya ta ce, "na ji, na gode." Bai ce komai ba ya fita, Didi tana ta dariya ta ce, "Allah ya shirya Omar." Nayla murmushi yake yi dan dramar su da Didi burge ta take yi sosai, ya mayar da Didi itace anwa shine yayanta. Ba jimawa ya dawo, Didi ta fita
Chapter 117 · 0% Book details