Sashe 53
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gama mamaye mata jiki. Tana sakkowa daga motar tayi baya zata fa i da sauri ta ji a taro ta an ri o hannayenta ya ce, "Subahanallah, Nayla Lafiya?." Abbas ya fa a yana kallon ta, dawowarsa daga masallaci kenan ya ga shigowarta. e ido tayi da suke lumshe ta kalle shi ta ce, "Yaya Abbas kaina, ka kaini wajan Mama, Kaina zai cire." Hannayenta duka biyun ya ri e ya ji zafi sosai a jikinta ya ce, "baki da lafiya haka?." Bata iya magana ba yana ri e da ita tana takawa a hankali har falon Maman. Mama tana zaune ta ga sun shigo, ta kalli Abbas ta ce, "wacece wannan?." Abbas ya ce, "Nayla ce" ya fa a yana arasawa inda Maman take. Ai bata jira sun araso ba ta taso ta zo inda suke ta ce, "Nayla? Lafiy? Me ya same ta?" Ta fa a tana ri e Nayla. Nayla tana jin hannun Mama a jikinta kawai ta fa a jikin Mama ta fashe da sabon kuka. Hankalin Mama ya tashi jin zafin jikin Nayla ga kuka da ta ke yi ta ce, "Nayla lafiya? Me ya same ki haka? Daga ina ki ke da magaribar nan?." Jin bata yi shiru ba sai kukan take yi ya saka Mama ta fara bubbuga bayanta a hankali tana cewa, "ki bar kuka jikinki ya yi zafi, sannu." A hankali ta fara sassauta kukan tana jan numfashi ta ce, "Mama kaina zai cire." Mama ta ce, "ba dole ba, wannan kuka da ki ke yi ga zafin jikinki ai dole kai ya yi ciwo." Zaunar da ita Mama ta yi ta kalli Abbas da yake tsaye har lokacin ta ce, "A ina ka samo ta?." Abbas ya ce, "Na dawo daga masallaci na ga shigowar motarta ta, yadda take tu in ya bani mamaki kamar tu an maye, sai na shigo gidan na samu ta fito daga motar zata fa i." Mama ta kalle shi ta ce, "Taimaka ka kira min Khalid ya zo ya bata magani da gaggawa" ta fa a tana zama a kusa da Nayla ta ri e hannunta. Khalid in ne ya shigo da sallama, Mama ko amsawa bata yi ba ta ce, "Khalid zo ka duba min Nayla don Allah, jikinta ya yi zafi." Da sauri ya araso ya ta a goshinta ya ce, "Subahanallah, Mama jikinta ya yi zafi sosai. Me yake damunta?." Mama ta ce, "Ban sani ba, ka yi mata taimakon gaggawa kawai, a samu ciwon kan da yake damunta ya sauka." "To bara na je na dawo" ya fa a yana fita Mama ta bishi da cewa, "Ka yi sauri don Allah." Mama ta kalli Abbas ta ce, "Abbas bani ruwa don Allah." Ba musu ya mi o mata ruwa ta bu e ta sakawa Nayla a baki ta ce, "Nayla bu e baki ki sha ruwa." Ta an sha ka an ta kifa kanta a kafa ar Mama tana fitar da huci mai zafi. A lokacin Khalid ya dawo ya araso ya ce, "Bara a yi mata allura kawai" ya fa a yana ri o hannunta ya tattare dogon hannun rigar jikinta ya nemi jijiya ya yi mata allurar. Tana jikin Mama a kwance har aka yi allurar bata sani ba dan gaba aya zafin da zuciyarta yake mata ya fi zafin allurar. Mama ta ce, "ka tabbatar zata samu sauki?." "In sha Allah Mama, nan da anjima ka an zaki ga ta warware. " Mama ta aga kai tana sake kallon Nayla da take jilinta har lokacin. Abbas ya ce, "Mama a kai ta aki ta kwanta, in ta samu bacci zata fi jin da i." Mama ta ce, "Khalid kira min Ummimi ta zo mu kai ta aki." Khalid ya sau sama sai ga su tare da matashiyar budurwa wacce zata yi sa'ar Jalila anwar Nayla, ta zo suka ri e Nayla zuwa akin da yake falon aka kwantar da ita. Khalid da Abbas suna bayan su, har Mama ta cire mata hijjab in jikinta da ankwalinta saboda ciwon kan, sannan aka kashe hasken akin aka kunna mata ac, ba jimawa bacci ya kwasheta dan allurar ta ratsa jininta. Tare suka fito falo Ummimi ta kalli Mama ta ce, "Mama yaushe ta zo? Daman bata da lafiya ne?." Mama ta ce, "yanzu ta shigo, ban san me yake damunta ba kuma." Khalid ya ce, "da ta farka daga baccin zata samu sau i in sha Allah, in ya so sai je asibiti a tabbatar da abinda yake damunta." "Ni na fi tunanin ko ciki gare ta" Mama ta fa a tana kallon Khalid. Khalid ya ce, "to bana ce ba, shiyasa daman na yi mata pcm saboda gudun hakan." Abbas ya ce, "ni sai nake ganin kamar tana cikin damuwa ne duba da yadda ta shigo da motar da yanayinta." Mama ta ce, "Sai ta farka zamu san abinda yake damunta. Ku je ku yi sallar i'sha ku zo mu ci abinci" ta fa a tana tashi ta hau sama Ummimi ta biyo bayanta su kuma suka fita. Omar da tsayuwar Nayla a inda yake da abinda ta ce babu abinda bai ji ba kawai bazai iya magana ba ne, ya yi matu ari da mamakin kansa da ta tsaya a gabansa yana cikin wannan yanayi ta yi masa magana bai auki mataki a akanta ba. A duniya bai ta a jin acin rai kamar wannan ba, a lokacin baya ha a auren su da ita ya fi komai ata masa rai, amma a yanzu wannan shine kan gaba. Mari fa, in ya tuna marinsa fa Didi tayi akan wa ancan wanda basu da wata daraja a idanunsa sai ya ji kamar duniyar zata juya ta kife dashi. Haka yake zaune a wajan shiru bai motsa ba kuma bai yi magana ba, sai arar fankar da take tsaye a falon take juyawa a hankali. Kiran sallah ne ya mi ar dashi cikin mutuwar jiki, rana ta farko da ya shiga ban akin kusa da falon ya yi alwala, ya jira masallaci aka tarar da Allah ya bi su a falon dan bazai iya fita ba a yanayin da yake ciki zai iya tashin Kano gaba aya. A haka ya idar da sallah ya sake zaune shiru acin rai yana nu usar zuciyarsa, yana ratsa jininsa yana yawo a sassan jikinsa. Har aka yi sallar i'sha yana wajan, a nan ya sake yin sallah ya zubawa waje guda ido abubuwan da suka faru suna sake gilma masa a idanunsa. Shi dai ya san ranar bacci sai dai arawo, acin rai hana shi bacci yake yi ko ya ya motsa sai ya tuna, balle irin wannan acin ran da ya fi komai ta a shi. Baya so ya fita ya ha u da wani ya yi masa magana dan bazai iya tankawa kowa ba, in kuwa ya bu e baki ba abin kirki ne zai fito ba, shiyasa duk sonsa da komawa gidansu ya kasa motsin kirki yana zaune a wajan kamar mai aukar karatu. Didi kuwa a gidansu mijinta ya je ya auke ta, tun a mota ya fahimci tana da damuwa amma bai tambaya ba har suka je gida. Sai bayan ta ci abinci ta huta ya zauna kusa da ita ya ce, "A yanayin da ki ke ciki saka damuwa a zuciyarki bai kamata ba Aisha, yanzu bu atar hutu ki ke yi da kwanciyar hankali ba wannan damuwar da ta mamaye fuskarki har ta nuna a jikinki ba. Don Allah ki sassautawa kan ki wannan tashin hankali, kin shiga third trimester fa, in baki samu kwanciyar hankali ba wanne a yanayi zaki kasance?." Hawaye ya sakko daga idanun Didi, AbdulHamid ya ce, "kin gani ko? Yanzu meye na kukan? Me ki ka ce min last zuwan ki awo? Kin fa a min an ce jininki ya an yi sama ka an, kin san da hakan kuma kika saka damuwa a ranki har da kuka Aisha?. Ko rasuwar da aka yi ce take ta a zuciyarki?." "Yalla ai Omar ne" ta fa a tana kallonsa da jajayen idanunta. Da mamaki ya ce, "Omar kuma? Shine ya saka ki kukan?." Didi "Damuwar Omar ce ta saka ni kuka yalla ai, Omar so yake jinina ya hau." A tausashe ya ce, "Damuwar Omar kin saba da ita tun ba yau ba, meyasa zaki bari tayi tasiri a zuciyarki a irin wannan lokacin da ki ke bu atar hutu da kwanciyar hankali?." Ta goge idanunta ta ce, "Ka san komai a tarihin iyayen mu, Omar ya i zuwa gaisuwa, nayi-nayi ya ce bazai je ba. acin rai ya ja ni har na mari shi ban sani ba." AbdulHamid ya wara idanu ya ce, "Aisha mari? Omar in ki ka mara?." Didi a raunane ta ce, "Wallahi ban san na yi ba, ban san na aikata ba Yalla ai. Magana yake ta fa a mara kan gado, in da ban katse shi ba a lokacin tsaf zai furta kalmar saki akan Nayla. Tsaf zai ce ya saketa gashi tana tsaye a wajan, na mare shi saboda na katse shi amma sai na sake tunzura shi." "Kema kin san dole ya tunzura, marinsa da ki ke yi shine ma zai saka i zuwa gaisuwar. Zai ga akan bai je gaisuwa ba ki ka mare shi, to bazai je ba." Didi ta ja numfashi ta ce, "kamar a gabanka aka yi. Ban san meyasa bakina ya furta saboda mahimmacin da suke dashi a rayuwarsa sune suka kar ar masa aure ba, Wallahi ban san na fa a ba, saboda na san furta hakan babbar kato ara ce a gare shi. Wallahi tsawar da ya yi sai da an cikina ya motsa." Duk da halin da take ciki sai da ya yi murmushi jin abinda ta ce kafin ya ce, "Ai ko nan gaba kar ki sake kuskuren marinsa, ke kin fi kowa sanin halinsa in ya shiga bacin rai, yadda ki ka yi losing control ki ka mare shi shima zai iya losing control ya mangareki. Kuma ke da ki ke neman ya je gaisuwa ina ke ina mari don Allah?." Didi ta ce, "ya ata min rai ne wallahi." "Ba yau ya saba ba, jurewar da ki ka saba yi dai ita