Sashe 159
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya jikin ta?." Omar ya ce, "kanta yana ciwo sosai, sun ce jininta bai sauka ba tana ukatar hutu sosai, yanzu ma abinci aka ce taci." Mama ta ce, "to ai an taho da ruwan zafi, daman na san dole za a bu aci ta sha koda tea ne" ta kalli Ummimi da take gaban Babyn tana yi mata hoto ta ce, "Ummimi ke ta a kike yi ni ga tawa ar bata jin da i, ha o mata tea tasha sai ta shayar da ita. Mi o min ita." Mama ta fa a. Ummimi ta kawo mata babyn sannan ta ha a mata tea in kamar yadda Mama ta ce ta bawa Nayla. Nayla ta ce, "Mama shima ko iftar bai yi ba har yanzu, nace ya je yaci abinci ya i." Mama ta kalli Omar da yake duba waya ta ce, "Omar baka ci abinci ba? Maganar arfe tara na dare ake yi fa yanzu?. Ummimi maza yi serving insa da abincin da na taho dashi, wannan ai ba daidai bane, in rashin abincin ya saka ka fa i fa?." Omar ya ji wani irin banbara wai, wai wata mace ce bayan Didi da Nayla da suka damu ya ci abinci har take cewa kar ya fa i. Sai yaji girman matar ya sake aruwa a idanunsa, dan bayan Didi ds Nayla bashi da mai damuwa dashi. A hankali ya ce, "Babu komai, zan je gida yanzu." Nayla cike da shagwa a ta ce, "Allah Mama in ya je ba ci zai yi ba, to waye ma zai masa girkin..? na san shi ya gaji ba yi zai yi ba, don Allah zauna ka ci ka ji!" Ta fa a tana kallon sa kamar zata yi kuka. Mama ko a jikinta da yanayin da Nayla take yi masa magana ta kalle shi ta ce, "babu inda zaka je ai, Ummimi ki zuba masa har tea in ya sha." Omar ya kasa magana yana jin yadda take magana cikin bada umarni, to ya zai yi mata? Kamar babar matarsa take dole ya yi abinda ta ce. Ya kalli Ummimin ya ce, "iya tea in ma ya isa." Tea in ya kar a ya koma ya zauna daga can arshen akin ya zauna dan gaskiya bazai iya fita ya bar Nayla ba. Mama ta saka aka bawa Nayla dafaffen naman rago da aka shi da romo mai yaji ka an ta ce ta ci. Ta kuwa ci in amma ta fi shan ruwan, ta ajjiye bayan ta gama ta ora mata Babyn a cinya ta ce, "To bismillah, ki shayar da ita yunwa take ji itama." Nayla kamar zata yi kuka ta kalli Omar da ya kalle ta, suna ha a ido yayi mata wata inkiya da ido yana sipping tea da yake hannunsa yana ifta idanunsa. Dariya ta kama Nayla, amma sai ta auke ido daga kansa ta kalli Mama ta ce, "Mama ai ban iya ba." Shigowar Jidda akin ya hana Mama magana, ta taho ta rungume Nayla ta auki Babyn tana kallonta ta ce, "kin ci amanata." Nayla ta ce, "yi ha uri." Suka gaisa da Mama dan ita bata ma ga Omar ba dan yana can arshe sai ka kula zaka ganshi dan akin yana da girma. KRB3P097 Nana haleema Mama ce ta nunawa Nayla yadda zata shayar da ita, Nayla ta yi yadda tace sai zuba shagwa a take yi ita zafi take ji, ita ta gaji waye-waye. Duk aga idon da zata yi ta kalle shi sai sun ha a ido, da sun ha a ido kuma sabuwar inkiya zai yi mata wacce ita dashi ka ai suka san me hakan yake nufi. Mama bata yaleta ba sai da ta tabbatar yarinyar ta oshi sannan ta kar eta aka kwantar da ita. Jidda hoto ta dinga yiwa yarinyar ta tura family group insu. Omar bai jima ba sai ya fita, fitarsa Jidda ta gani dan bata san yana nan ba. Mama ta saka Nayla ta yi wanka ta saka doguwar riga wacce Mama ta taho mata da ita ta kwanta a kan gadon bacci ya sake auketa. Duk suka fito waje saboda ta samu ta yi baccin yadda ya kamata. Omar sai da ya koma ya ga kiran Didi WhatsApp call, ya yi murmushi ya kirata ta ke tambayar mai jego ya ce ya barta asibiti. A gaggauce ya shirya shima, ya yi wanka ya canja kaya ya dawo asibitin dan bazai iya zaman gidan ba sam. Washe gari ranar sallah, ji yake ko sallar ma bazai iya zuwa ba, amma ganin Mama na kula da ita sosai sai ya je ya dawo daga masallacin kai tsaye ya dawo asibitin. Da yake asibitin ku i ne akwai ma'aikata suna ta aikinsu, ya shiga akin Nayla da sallama a nan yaga jama'a sun aru harda wa anda bai sani, abinda ya bashi mamaki ganin dangin mahaifiyarsa, ya bisu da kallo dan ya san aikin Didi ne. Gaisawa kawai suka yi ya fito ya zauna sai ga Mama Saroot da Mama Zainab sun fito suka kalle shi a ra e suka ce, "Omar an samu aruwa, Aisha ce take sanar damu, Allah ya raya." "Amin. An yi sallah lafiya?." Mamaki ya hana su magana suka zubawa juna ido, da yar Mama Zainab ta ce, "Lafiya lau, Allah ya raya abinda aka samu, ance sunanta Aisha ko?." Ya aga kai Mama ta ce, "Allah ya raya mana, yasa ta yi halin mai sunanta." Ya amsa da amin sai suka samu arfin guiwar zama a asibitin dan suna tsoron kar ya yarfa su a gaban sirikai. Sai da aka kwana biyu a asibiti sannan aka bada sallama, da kansa ya ri o hannun Nayla suka fito tana takasa a hankali Babyn na hannun Mama Sa'adatu, sai Mummy Maman su Salma. Mota suka shiga aka wuce gidan sa kai tsaye. Kai tsaye sama aka saka ta ta hau yadda baza ta sake sakkowa ba, duk wanda ya zo sai dai ya hau saman. Tana falon a zaune, bayan Mama ta saka ta yi wanka ta shirya cikin atamfa baza ka ce ita ta haihu ba. Nayla ta saka Jidda ta auko kayan Babyn ana aurawa, baby beds da baby swing aka ajjiye a falon. A ranar su Mama suka zo daga Kaduna harda Abiy da Salma da kuma Jawad da su Jalila. Farin ciki a wajan Nayla sai da tayi kuka, ta ri e Abiy dan bai ta a zuwa gidan ta ba sai yanzu. Da i take ji da ta gashi a gidanta, ta saka aka yi musu hoto shida ita duk ta ru e kamar bata ta a ganinsa ba. Bai jima ba ya tafi bayan ya bada kayan baby da kuma kayan ita kanta Naylan. Mama kuwa basu tafi ba sai dare, Salma ma sai dare sosai sannan suka tafi. Jalila kam ta ce kwana zata yi suna tare tana ri e da Musliha tana yi mata hoto. Mama Sa'adatu bayan tafiyar Maman Kaduna ta kalli Nayla ta ce, "Nayla zan koma gida yanzu, amma gobe da safe zan dawo. Zan zauna har sai an yi suna daga nan Baba Hafsatu zata zo ku cigaba da zama har ki samu lafiya." Nayla ta ce, "To Mama." "Ki kula sosai, ban da yawan zirga-zirga kin ga baki da lafiya kuma an miki inki. Wai kin aru a wajan haihuwar ne har aka yi miki inki?." Nayla ta girgiza kai tana turo baki ta ce, "A'a, kawai an yi min ne, cosmetics ne." Mama ta ri e ha a ta ce, "Gaskiya ne an da i miji, kin kyauta." Nayla ta yi murmushi Mama ta tafi aka barta da Jalila da Ummimi. Nayla falonsa ta shiga da Musliha a hannunta, ta same shi yana zaune a akan kujera yana duba waya, ganinta sai ya ajjiye wayar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Wai haka ake haihuwar a hana ka ganin matarka? Zo ki zauna" ya fa a yana tashi tsaye ya kar i Musliha sannan ya zaunar da ita. Nayla ta ce, "To ka ga ba i ake ta yi shiyasa, yanzu ma motsin ka na ji nace ko mijina ya ci abinci?." "Wa nake dashi da zai bani?." "Baka ci ba kenan?." "Ban ci ba." Nayla ta ce, "to bara na nemo maka." Ya dakatar da ita ya ce, "Wasa nake yi, har falon nan Mama ta saka aka kawo min abinci, na zama an gatanta, bata barina da yunwa." Murmushi ta yi ta ce, "Na ji da in haka." Ya zuba mata ido ya ce, "Wai ba a gama jegon ba?." "Tab ai sai nan da kwana arba'in." "Ko kuma sai an tashi duniya ba" ya fa a cikin ba ar magana yana harararta. Nayla tayi dariya ka an tace, "Allah da gaske nake." "Kedai ayi shiru kawai, amma wallahi baza ki kwana arba'in ba." "Harda wallahi?." "Kuma kin san bana rantsuwar banza ba." Ta yi dariya ta ce, " azu an kaiwa Hajja Musliha." Ya yi murmushi mai sauti yana girgiza kai ya ce, "ai gwara da aka kai mata ita." "Murmushin na meye?." "Na Hajja ne." "Da ta baka aurena?." Omar ya sake yin ar dariya ya ce, "da aka bani auren ki a gidanta." Nayla ta murmusa ta ce, "tijarar da ka yi a gidan fa?." Ya shafa fuskarsa yana tuna lokacin, ya sake yin murmushi ya ce, "ta rashin sani ne, ai ban san haka sirrin yake ba, ban san haka abun yake da ankaren za i ba." Nayla ta sake yin murmushi ta ce, "baka da kunya." an sunkuyar da kai tare da ago ido ya kalle ta ya ce, "itama mai jin kunyar tayi ciki ta haihu, kuma ba a ruwa tasha cikin ba." Nayla ta sake yin murmushi ta kwantar da kanta a kafa arsa ta ce,"Yaushe Didi zata dawo ne?." "Har sai an yi suna." "Kai amma ban jiwa Didi da i ba." Murmushi ya yi akwai suka cigaba da hira. Haka aka cigaba da kar ar ba an barka, dangin babansu Omar duk sun zo kuma suna ha uwa babu wanda yake nunawa wani abu, sai yaga dama na zai kula su, hakan ya saka gobe ma wasu suke zuwa. angaren su Umma Saroot kusan a gidan