← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 205

Sashe 14

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata komai ba itama tunda ya yi mata warning shikenan ta daina yi masa magana. Ta gaji da kula shi yana shareta ko ya harareta wani lokacin harda tsaki, ga tsoronsa da take ji shiyasa tunda ya hanata kula shi ta hanu har aka shiga watan ramadan. Yau an kai azumin ramadan na uku kenan, kuma ya yi daidai da kwana goma sha bakwai da tarewar Nayla a gidan Omar. Tana nan kamar yadda ta ke, bata mayar da jikinta ba kuma bata rame ba. Tana nan kamar yadda aka kawo ta da ar rama da kuma damuwa. Dan zaman shirun ma damunta yake yi, sai dai ta danna waya ta gaji, ta yi karatu ta gaji, ta yi bacci ta gashi abinda take yi kenan a gidan. Gaba aya zaman damunta yake yi shiyasa bata da walwala ko ka Tana zaune a falo sun gama waya da Twiny da take asar saudia ta je umrar azumi. Wayar ta ce tayi ara ganin sunana Yaya J sai ta auka da hanzari tana murmushi. Kafin ta yi magana ya ce, Ina gate in gidanki. Kamar an yiwa Nayla albishir da aljanna, ta mi e da sauri ta saka hijjabi ta fita ta bu e gate in ya shigo yana kallonta da murmushi. Yaya J ta fa a tana rungume shi cike da murnar ganin an gidansu. Dariya ya yi ya ce, Nayla kin kasa girma har yanzu, ke fa matar aure ce ya fa a yana rabata da jikinsa amma ta ri e hannunsa gam tana kwantar da kanta a kafa arsa. Sannu da zuwa Yaya J. Yauwa Nayla. Hannunta na cikin nasa suka arasa falon ta zauna shima ya zauna ya ce, parlour gidan nan na ki ya yi kyau Nayla, ya burge ni. Nayla tayi dariya ta ce, Ina yini Yaya J. Lafiya lau Nayla, ya ibada?. Alhamdu lillah Yaya J. Ya hanya?. Jawad ya ce, Alhamdu lillah. Da yake tun jiya ina Kano ba yau na shigo ba. Nayla ta ce, shine ba ka zo ba tun jiyan?. Ya murmusa ya ce, gashi ai na zo yanzu. Yanzu mu ka gama waya da Twiny. Eh, ita kwanan ta biyar da tafiya ma ai ko?. Nayla ta aga kai alamun eh Jawad ya ce, Abiy fa? Kun yi waya?. Nayla a sanyaye ta ce, na kira shi na yi masa Allah ya kiyaye, yanzu ma ma san sun sauka ko?. Jawad ya ce, Da yake Egypt airline suka hau kin san yana da wahalar sha ani, sai sun yi transite Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, Allah ya kiyaye. Ya bita da kallon tausayi a zuciyarsa, amma a bayyane ya ce, Amin Nayla. Ya ciro takarda daga aljihun ya ce, Ga takardar canjin wajan aikinki, na saka wata abokiyar aikin ki tayi komai da komai. Yanzu ki yi signing a wannan takardar zan bayar a kai can Kaduna in, gobe in Allah ya nuna mana sai ki je branch in da yake kusa da gidan governor ki kai wannan takardar ki yi signing shikenan. Nayla farin ciki ya mamaye mata zuciya, ko babu komai zata rabu da zaman ka aicin da yake damunta wani lokacin. Biro ya bata da kansa ta saka hannu ya kar a ya ce, zan bayar a kai can Kaduna in, wannan kuma sai ki tafi da ita goben. Ta kar i wacce yake mi o mata ta ce, To Yaya J, na gode sosai. Na ji da i wallahi. Murmushi ya yi ya ce, zan cire miki hanci keda kin gode in ai. Ga key in motar ki da nayi alqawari, gata can a waje an zo miki da ita, akwai laptop inki da iPad inki a ciki. Akwai kayan ki da Mama ta bani da dai abubuwan ma dai suna cikin motar. Nayla ta auki key in da ya ajjiye kusa da ita cikin tsananin farin ciki ta ce, na gode Yaya J Tana fa a sai kuma ta fara hawaye. Jawad ya yi tsaki ya ce, Allah zan yi tafiyata, ya zaki dinga yi min kuka kuma?. Ta goge idanunta ta ce, To Yaya J na daina ta fa a tana goge idanunta. Babu abinda ki ke so?. Babu komai. In kawai ko meye ki fa a min. Kuma aikin gidan nan bai yi miki yawa ba kuwa?. Nayla ta ce, za a kawo min house maid daga Kaduna, sai Mama ta dawo. Jawad ya ce, meyasa sai Mama ta dawo? Yanzu aikin baya yi miki yawa?. Ta ce, Ina iyawa. Kin tabbatar?. Eh Yaya j. Gaskiya ki yi magana ko gidan Hajja ne a kawo miki housemaid, har wani aiki ki ka iya da zaki iya gyara gidan nan?. Bayan wannan falon akwai wani, sannan ga bedrooms. Gaskiya ki yiwa Hajja magana ko wacce zata dinga zuwa tana taya ki ta koma ne ki samu. Nayla ta aga kai ta ce, To Ya J. Kuma kaga gwara ma ta gidan Hajjan, damaan ni bana son mai kwana. Jawad ya ce, haka dai ya kamata. Yanzu abinda zai faru zan tashi na wuce, kin san arfe uku zai tashi, yanzu ga aya da rabi har tayi ina da sauran awa aya da rabi. Zan je gida a kai ni airport ya fa a yana mi ewa tsaye. Nayla ta ce, Yaya J Allah ya kiyaye hanya. Su Hajja ma gobe da zafe zasu tafi. Yayi dariya ya ce, kawai ki ce saura ke ka ai a nigeria kowa ya gudu ya barki. Dariya tayi ta ce, Yaya J in zaka dawo fried chicken in McDonald nake so, na bawa Twiny sa on Albaik, na baka na McDonald, Salma kuma zan bata na KFC. Dariya sosai ya ce, Duk ke ka ai? Kuma ki rasa abinsa za a siyo miki sai soyayyiyar kaza?. Nayla ta ce, ita nake son ci. Tare suka fito shi da ita suna hira har ofar gidan, ta bu e sabuwar motar irar glk ta auki laptop inta da iPad inta. Ya kalle ta ya ce, To Nayla na tafi, ki cigaba da addu ya fa a yana shiga mota ta aga masa hannu ya tafi. Gidan ta koma cike da kewa ta saka laptop inta a chaji ta dawo ta yi sallar azahar sannan ta auki alkur ani ta fara karantawa. Gate taji ana bugawa abin ya bata mamaki, ta hijjabi saka ta fito tana tambayar waye. Muryar Bashir yaron Omar taji hakan ya saka ta bu e ya ce, Antyn mu barka da rana. Damisa ne ya aiko ni na kawo wannan kayan gidan nan. Nayal ta ce, to shigo. Ya ibada?. Alhamdu lillah. Ta bashi hanya ya shiga ta rufe gate inta koma ciki. Kaya ne da yawa a leda babba ya ajjiye yana kallon falon ganin da haske sosai sai ya ce, Antyn mu zan iya yiwa kayan nan hoto a nan? Naga da haske sosai, in ban yi ba yanzu in anjima zan saka a nemo ni. Nayla tayi dariya ka an ta ce, kayi mana, babu komai. Godiya nake ya fa a yana fito da takalman daga ledar. Nayla hannu ta saka ta auki takalmi guda aya na mace ta ce, kai amma takalmin nan ya yi kyau sosai, kuma da gaske aikin kune wannan? Da hannu aka yi shi?. Bashir ya ce, warai kuwa Antyn mu. Wannan boss ne da kansa ya yi shiyasa ya ce na kawo shi nan sai na shago sun are za a fitar da su. Tun safe aiki mu keyi har yanzu. Nayla ta ce, Gaskiya ya burge ni sosai ma ta fa a tana shafa logon takalmin wanda aka rubuta Tiger da wani style mai kyau da kuma yanayin jikin Damisar. Nayla ta kalli wayar da ya auko zai yi hoton ta ce, ko na ara maka wayata kayi hoton da ita? ta fa a tana mi a masa wayarta. Kar a ya yi ya ce, Godiya mu ke Antyn mu, ga iPhone 16 ai iPhone 13 baza tayi ba. Hotuna yake yiwa takalman tana kallon dan ya iya aukar hoton sosai. Ya jima yana yi tunda suna da yawa sannan ya gama. Nayla a afarta ta saka takalmin yayi mata bala in kyau kasancewar jikinsa baki ne sai ya haska afarta sosai. Wayar da ya mi a mata ta kar a kawai sai ta yiwa afarta ta hoto ta tsaya tana kallo domin hoton ya yi kyau sosai. Bashir ya ce, Antyn mu ayi min airdrop. Ba musu ta bu e ta tura masa hotunan suka je har wanda ta auki afarta bata san ta tura ba. Kallon hoton ya yi ya kalleta ya ce, Antyn mu amma hoton nan ya yi kyau sosai. Zamu iya posting insa? Ya fa a yana haska mata hoton. Nayla ta ce, ban ma san na tura maka ba, amma babu damuwa zaka iya. Daman muna son a dinga sakawa ana auka a afar mace, to Boss in ne shi ba wasu mata ya sani ba balle a dinga biya ana yi. Na mazan ma daman da afarsa ake auka shima kuma sai ya ga dama, in ya ga dama ya saka a auka in bai ga dama ba ba za a auka ba. Amma wannan kam ya yi kyau. Nayla ta ce, kuma nawa ku ke siyarwa?. Bashir ya ce, ya danganta gaskiya, bamu cika siyar da guda aya ba, an fi siyan kwali ko guda sha biyu. Nayla ta ce, ya kamata ace kuna siyar da pieces saboda ga sallah arama nan zata zo akwai wanda zasu siya sosai. Bashir ya ce, Gaskiya ne, amma da yake muna kaiwa kasuwa da shaguna bamu cika siyar da aya ba. Amma zamu fara in sha Allah. Nayla tavce, nima ina da shop a Kaduna, ina so a ha a min masu kyau ku bawa driver da ya ke muku aiki ya kai can na tabbatar da za a siyar. Bashir ya ce, To Antyn ku duk sanda ki ka shirya. Ai gobe nake so a tura, ka ha a package mai kyau na maza da mata da na yara, zan yi waya a kar a dan na tabbatar bazai kai sallah ba ya kare. Bashir ya ce, za a yi hakan. Meye sunan platforms handle in ku ke posting?.
Chapter 14 · 0% Book details