Sashe 23
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
take ta maimaita lafiya lau take, Ina jin wannan takaicin abin har zuciyata, ina jin zafin abin nan har ohon zuciyata. A haka ma bata samu shiga a wajansa ba har yanzu, har yanzu ko kallon arzu i bata ishe shi ba, har yanzu baya kallon ta matsayin matarsa ya jingine ta a gefe kamar wacce aka kai masa ita ajiya, amma sai wani lafiya lau take maimaitwa. Nayla kamar ba ni na raine ta ba, ka duba Jidda da mijinta suna nan suna ibada, gaba aya dangi ana nan ana ibada amma ita banda ita, kuma hakan bai dame ta ba. Allah wadaran naka ya lalace Mama ta fa a tana kuka. Abiy ya murmusa akwai bai ce komai ba ya tashi ya fita daga aki. Mama ta goge hawayenta da ta tabbatar ya shiga ta ce, Nayla zama da Omar ai ko bakya so. Allah na tuba ka yafe min ina asa mai tsarki ina arya ta fa a tana tashi tayi alwala ta saka babban hijjabi ta fita itama. Nayla kuwa bayan sun gama waya Abba ne ya kira ta, shima tambayar da yayi mata kenan ta amsa da lafiya lau. Bayan ta kashe Maman Kano anwar Abiy ta kira ta, bayan ta gama da ita Mama Sa adatu, bayan ta gama Baba. Har Daddy da suke tare da su Hajja a saudia sai da ya kira ta amsar da ta bawa su Jidda ita yake basu. Ajiyar zuciya tayi bayan ta gama amsa wayar ta ce, Nayla ar gatan dangi, kowa kirana yake ya ji lafiyata. wasa gate in ta ji ana yi a tsorace ta tashi ta saka hajjisbi ta je ta bu Mama Sa adatu ta gani ta rungume cikin murna ta ce, Mama sannu da zuwa. Mama ta bita da kallo ta ce, Duk da mun yi waya hankalina ya kasa kwanciya wallahi, kina lafiya?. Nayla tayi dariya ta ce, lafiya lau nake Mama ta fa a tana kulle gate in suka shiga ciki. Mama ta bita da kallo ta ce, Amma yanayin ki bai gwada lafiya ki ke ba, kalle ki fa. Nayla ta zauna kusa da ita ta ce, Mama tun jiya daman bani da lafiya, stress na aiki ga azumi ya saka min zazza Ayya sannu, amma dai babu abinda ya same ki ko? Mun yi waya da su Yaya ya ce na taso nazo na duba ki. Da Abbas zan turo sai na ce bara na zo da kaina, ni kaina hankalina ya kasa kwanciya duk da mun yi waya sai nake ji kamar ba lafiya ki ke ba. Nayla ta ce, lafiya ta lau wallahi Mama. Mama ta ce, na ga alama. Amma ya aka yi abin ya faru jiya? Su waye haka suke son cutar dake har gida?. Wallahi Mama ban sani ba. Shi bai fa a miki ba?. Tunda ya fita ma bai dawo ba. Amma naga an ce ya kai su gaban hukuma an za a hukunta su, hakan da yayi daidai ne da bai auki hukunci a hannaunsa ba. Nayla tayi shiru bata ce komai ba. Mama ta ce, yanzu me ki ke so?. Nayla ta kwanta a kafa arta ta ce, Babu komai Mama. Mama ta ri e ta tana shafa kanta a hankali cikin tausayinta da auna. Ita kuma Nayla ji take kamar ta kanta a jikin mahaifiyarta yake, shafa kanta da Mama take yi ya saka bacci ya auke Nayla. Motsawa Mama tayi sai Nayla ta bu e ido Mama ta ce, kwanta ki huta zan tafi gida, gobe ki zo mu sha ruwa gaba aya. Idanunta a lumshe Mama ta tashi fita amma zuciyarta babu da i bata so ta tafi ta barta. Nayla ta jima tana bacci har biyar na yamma, sai da ta farka tayi sallar la asar ta fara lazumi saboda lokacin amsa addu a na ranar juma (Lokacin amsar addu a na bayan sallar la asar a duk ranar juma a, lokaci ne mai matu ar falala kuma addu a bata da hijjabi a wajan Allah. Duk abinda aka ro a a wannan lokaci Allah ya amsa sai dai a jira lokaci. Lolacon amsa addu ar yana farawa ne bayan sallar la asar zuwa magriba, babu wanda ya san ta amaiman arfe nawa lokacin yake shiga, abinda malamai suka sanar damu bayan sallar la asar zuwa magriba a tsakanin haka lokacin yake farawa. Allah ya bamu iko ya amsa mana bu atar mu amin.) Tashi tayi ta dafa tea kamar ko yaushe tana tunanin bayan tea me zata dafa ta ci? Ita in tana azumi bata iya cin abu mai nauyi shiyasa sai ta rasa abinda zata ci. Irsh ta gyara ta soya, ta soya wai duk ta ajjiye. Dawowa tayi ta zauna ta cigaba da addu a a wajan har aka yi sallar magriba sannan ta yi sallah ta ci abinci ta sha magani. Kamar ko yaushe bai shigo ba sai bayan sallar tarawee, ta shigar da kaya kitchen ta fito kenan ya shigo. Kallon ta yayi ya auke kai ita kuma ta ce, an sha ruwa lafiya. Lafiya. Ba zato taji ya amsa hakan ya saka ta kalle shi sai taji ya ce, jiya na ce ki rufe ofa, meyasa baki rufe ba?. Nayla ta ce, kaina ne yake ciwo shiyasa na manta ban rufe ba. Kar ki sake kuskuren barin gidan nan a bu e, duk da babu wanda zai sake shigowa. Nayla jin yana yi mata magana a tausashe ssi ta damu damar shagwa a kamar zata yi kuka ta ce, Don Allah ka daina tafiya ka barni ni ka ai, tsoro nake ji wallahi. ago ido yayi ya kalle ta jin yadda take magana kamar zata yi masa kuka. Share batun yayi bayan ya an murza goshinsa kamar yadda ya saba ya ce, Ya ciwon kan?. Nayla wara ido tayi jin abinda ya tambaya ta kasa bashi amsa sai kallon sa da take yi dan bata yi zaton zai tambaya ba. Ganin irin kallon da take masa na mamaki sai ya auke kai ya wuce ta. Motsawar da yayi zai bar wajan ya saka Nayla ta dawo daga duniyar mamaki ta ce, na ji sau Bai ce komai ba ya shiga aki ba tare da ya kalle ta ba. Nayla da i kamar ya kashe ta, ko babu komai yana damuwa da lamarin ta tunda gashi bai manta tana ciwon kai ba, lallai ana samun cigaba ta tabbatar addu ar da take yi ce Allah ya amsa mata. KRB3P012 Arewabooks@nanahaleema11. A yadda take kwance kallo aya zaka yi mata ka san bata da lafiya, idanunta a kulle yake sai juya kai take cikin ciwon kan da ya fi komai damunta a yanayin da take ciki. Ashraf ne ya shigo ganin yanayin da take ciki ya ce, Baki da lafiya, dole mu je asibiti, Ta so mu je ya fa a yana ago ta daga kwance. Jikinki ya yi zafi sosai. Cikin muryar marasa lafiya ta ce, yale ni kawai, bana son zuwa ko Ina. Sai kin je, bazai yu ki dinga zama da ciwo ba. Ina son lafiyarki ko dan na samu abinda nake so. ar da ita tsaye ya yi ya kalli kayan jikita, Riga da wando ne dogaye a jikinta na bacci ya yi tsaki ya ce, gaba aya kayan ki na banza ne baki da kayan kirki a rayuwarki. Yafa mayafin mu je ya fa a yana yafa mata mayafin. Jiri take yi hakan ya saka ya ri eta suka fito, kasancewar akwai motar da yake amfani da ita ta haya a gidan. Asibiti suka tafi aka kar e ta ganin yanayin ta babu da i, aka kwantar da ita aka fara yi mata abinda ya kamata. Yana zaune a inda aka tanada domin jira, likitan ya fito ya bishi office ya zauna ya ce, Narma Sagir. Yadda likitan ya furta Sagir in ya bawa Ashraf dariya ya murmusa ya ce, yeah. s is your friance?. Dr ya kalle shi ya ce, Your mistress?. Ashraf ya ce, s my wife ya fa a yana kawar da kai dan bai san me za a ce masa ba. s pregnant. Ashraf ya wara idanu waje ya ce, what? Ciki wata nawa kuma?. Likitan bai fahimta ba kasancewar ba hausa yake ji ba. Ashraf ya dafe kai ya ce, How many weeks?. Three weeks. Ashraf yaja tsaki cikin takaici da ba in ciki ya ce, m not ready to be a father, so abort the baby. Are you sure you re not ready for that?. Yes I m sure. And even my wife she s not ready for that. Likitan ya ce, okay. Sign here ya fa a yana bashi wata takarda shi kuma ya saka hannu babu ata lokaci. Tashi likitan ya yi ya fita Ashraf ya ce, ni ban shiryawa haihuwa ba, tana haihuwa zata daina burge ni ni kuma ban shiryawa hakan ba. Tashi ya yi ya biyo bayan sa zuwa inda Narman take, zuwa lokacin an yi mata allurar zubar da ciki, a gabansa cikin ya fara fita Narma na juya kai saboda ciwo su kuma nurses in suna ta yi mata sannu har cikin ya fita. Cikin lokaci ka an aka gama gyarata aka yi mata komai yadda ya kamata ta yi bacci. Bata jima tana baccin ba ta farka tana kallonsa, an ciwo take ji ka an a mararta, sai nauyin da kanta ya yi mata, bayan wannan babu abinda take ji a jikinta. Ha a ido suka yi ya ce, Barka da tashi. Narma ta kawar da kai tana sauke ajiyar zuciya. Nurse ce ta shigo tana tambayar ta abinda yake damunta a nan ta fahimci an zubar mata da ciki ne. Bayan fitar nurse in ta kalli Ashraf murya na rawa ta ce, you have aborted my baby Ashraf?. Ashraf ya ce, yes, saboda bamu shiryawa zama iyaye a yanzu ba, shiyasa na saka a zubar na san kema baza ki so haihuwa a yanzu ba. Narma ta ce, ka yi shawara da ni?. Ai ba sai na yi shawara da ke zan yanke hukunci. Na ga dai an nan nawa ne ko? Ni na yi silar samun sa kuma na ce bana so, meye na ki?. Narma bata iya magana ba sai