← Book details Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 205

Sashe 164

Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta, suka ga hawaye take yi ta zube a wajan akan guiwarta ta ce, "Dad ya ce bazai aure ni ba ko? Ya ce baya sona ko Dad?. Baya sona....haka ya ce baya sona....ya ce baya son Narma.....Narma ce baya so. Dad da ka amince dashi tun farko da yanzu nice matarsa....da yanzu nic cemu ka haihu tare.....da yanzu bai ce baya sona...." Magana take ita ka ai kamar zararriya. A guje suka taho inda take Mum ta mi ar da ita ta ce, "Narma zai aureki, bai ce bazai aure ki ba ki kwantar da hankalinki." "Mum ya ce bazai aure ni ba, ya ce baya sona, ya ce baya aunata Mum. Mutuwa zan yi, mutuwa zan yi" ta fa a tana kwanciya a jikin Mum tana jan numfashi da yar. Dad ya ri e kafa unta ya ce, "Narma zai aure ki, kar ki damu zaki zama matarsa in sha Allah." Narma ta kalli Baban ta ta ce, "Dad ka yi min alqawari ko? Ka ce zaka kasa ya aure ni. Dad kar ka karya alqawarin da ka yi min a karo na biyu, ka saka ya aure ni Dad, Ka saka ya aure ni" ta fa a tana dafe kanta saboda sara mata da yake yi. Hankalin Mum ya tashi haka Dad in, ya kalli Mum ya ce, "Mu kai ta asibiti, mu tafi asibiti." Dad ne ya uako ta aka saka ta a mota, Mum ta shiga baya shima Dad in baya ya shiga driver ya ja motar suka tafi. Kwantar da ita aka yi aka saka mata ruwa da allurai ta samu tayi bacci, amma kafin tayi baccin magana aya kawai take maimaitawa. Bayan an samu tayi baccin su Dad suna zaune wani ha aki, hankalin su a tashe likitan ya shigo. Mum da hanzari ta ce, "Me yake faruwa Dr?." Likitan ya ce, "Ta samu high blood pressure ne, sannan kamar bata cikin nutsuwar tana ta maimaita ya ce bazai aure ta ba. Da alama tana cikin damuwa sosai damuwar ce ta haifar da haka, Yanzu dai ta yi bacci, in ta farka zamu gani in jinin ya yi asa." Mum ta ce, "Dr meye abin yi?." "tana cikin damuwa sosai, na fahimci wanda take magana a kai kamar shine damuwarta. In da dama a san yaddda za a yi ya kasance da ita koda inda farka ta ganshi ne, sannan a daina tayar mata da hankali ana cewa bazai aure ta ba, in ba haka ba zamu iya rasata gaba aya." Dad ya ja ajiyar zuciya ya ce, "Dr zamu iya rasata?." "Eh Sir, dole a tabbatar da ana bata farin ciki, dan kamar ta jima a cikin damuwar ko?." Mum ta ce, "an jima kam sosai." "To a tabbatar da an nema mata abinda take so, in ba haka ba akwai damuwa sosai." Dad ya ce, "shikenan Dr." Daga nan ya fita Mum ta zauna tana kuka. Dad ya zauna a kusa da ita yana rarrashi Mum tana kuka ta ce, "we're going to lose our daughter, saboda soyayya muna neman rasata. Dear ka yi wani abu, ka yi wani abun kar na rasa Narma. Ka san abinda zaka yi ya amince da auren ta" ta fa a tana ri e hannunsa tana kuka sosai. Dad cikin damuwa ya ce, "to ya zan yi? Daga wajansa na dawo fa ko abinci ban ci ba, Me ki ke so na yi kuma?." Mum tayi shiru kafin ta ce, "Ina friend inka wanda ya nemi alfarma a lokacin baya aka sake shi? Try to call him ko zai iya sakawa ya aureta. Ina cikin damuwa, jininta fa kana ji an ce ya hau" ta fa a tana sake fashewa da kuka. Dad ya ce, "shikenan, kwantar da hankalinki zan kira shi yanzun nan, Let me call him." Hannunsa har rawa yake ya auko waya ya kira Abiy, bata jima ta ringing ba Abiy ya auka ya ce, "Mai girma Sen Sagir." Sen ya ce, "Class captain, Kwana biyu ba a jinka." "Ku ne dai ba a ji, harkar za e ta gabato." "Bari kawai, abubuwa sun kwa "Allah ya tabbatar da alkhairi." "Amin Captain. Kana Kaduna ne?." Abiy ya ce, "Ina cikin Kano, jiya na shigo amma gobe zan koma in sha Allah." Dad ya ce, "Yauwa na ji da in hakan sosai, Ina son magana da kai da gaggawa, if possible ina so na zauna da kai a yau." "Babu damuwa ai, ina gida ko yanzu ma." "Okay, ka tura min location in zan zo." "Alright, babu damuwa." Daga nan suka kashe wayar. Ya kalli Mum ya ce, "Zan je na same shi face to face, kar ki damu na tabbatar ma zai iya yi masa magana ya amince." Mum ta goge hawaye ta ce, "Narma...." "Ki yi ha uri, zata samu lafiya." Dad ya rungume Mum yana bubbuga bayanta cikin rarrashi. Sun jima a zaune har Narma ta farka suka shiga akin a tare, Mum ta ri e hannayenta ta ce, "Kar ki damu Narma, zaki auri Omar kin ji?." Narma binsu take da kallo kawai kanta na yi mata mugun ciwo. Likita ne ya shigo ganin yanayin da take ciki ya sake yi mata allurar bacci su Mum suka fito. Dad yana fita kai tsaye gidan Abiy ya wuce da ya turo masa location. Yana zuwa aka bu e masa gate ya shiga dan Abiy ya sanar da mai gadin zuwansa. Falon ya shiga da sallama, Abiy ya tare shi da fara'a suka gaisa cikin girmama juna kafin Dad ya ce, "Wajan ka nazo Captain, ina neman alfarma." Abiy ya ce, "in dai bata fi arfina ba Senator zan yi maka, alfamar me ka ke so?." Dad ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ka tuna wannan yaron Tiger da ka ta a kar arsa daga hannuna?" Abiy ya girgiza kai ya ce, "Na gane shi, ba Omar ka ke nufi ba?." "Exactly Captain." "Wani abun ya faru ne?." "Ka san a lokacin baya Narma tana matu ar sonsa, ka tuna har na ce maka asiri ya yi mata?." "Na tuna komai." Dad ya ce, "Captain ba asiri bane, Narma ta haukace tana son yaron nan kullum cikin kuka da tashin hankali take. Yanzu maganar da nake yi maka tana asibiti a kwance, Dr ya ce ta samu high blood pressure. Kuma tun a Abuja an sanar damu zata iya samu heart attack." Abiy da damuwa ya ce, "Subahanallah! Narman?." "Ita fa Captain." "Amma ba ka ce min ta auri Ashraf ba?." Dad ya ce, "Forget about him, yaron nan bashi da kirki haka ya dinga wula anta min ita. Zancen da nake maka ya sake ta har saki uku, har aborting Babynta ya yi." Abiy ya ce, "Subahanallah! Gaskiya bai kyauta ba, abu sam bai yi da i ba Senator. Ba mu yi tunanin haka daga wajan Ashraf ba." Dad ya ce, "Ya bamu mamaki sosai, kuma daman Narma bata so, mun yi forcing inta ne muna ganin in ta zauna dashi komai zai zama normal. To abin ya i yuwa har aka yi saki." "Allah ya sa haka shine mafi alkhairi." "Amin Captain. Kamar yadda na fa a maka Narma ta haukace akan yaron nan Omar, ta zama kamar mai mental illness saboda shi. Na amince da gaske take sonsa ba wasa ba, kuma yanzu a shirye nake da na aura masa ita saboda kar na rasa ta." Abiy ya ce, "To ina jinka." Dad ya ce, "Ka ganni azu daga wajansa nake, har office na je na same shi akan maganar nan amma yaro nan ya kalle ni ya ce shi bazai auri Narma ba, daman ba sonta yake ba, da magana dai kala-kala marasa da i Captain. Daman ba tarbiyyar kirki ce dashi ba, na san kuma daban bashi da kunya baya jin tsoron kowa, haka ya saka ni a gaba da kalamai na rashin kunya kala-kala. Komawa ta gida kenan ina fa awa babarta abinda yake faruwa ashe ta ji, shine ta fa a a wannan condition in aka kaita asibiti." "Kai amma abin bai yi da i ba ko ka an, lamarin ya wuce tunani tunda har ana maganar high blood pressure." Dad ya ce, "shiyasa nazo wajan ka, da nace bazan sake neman sa ba sai dai Narma ta ha ura dashi, amma na kasa saboda halin da take ciki. Bazan iya bari ta rasa ranta akan soyayya ba, na amince zan bata aurensa indai zai amince ya aure ta. Yanzu daga asibitin sallah kawai nayi na zo gidan nan mu yi magana. Captain tunda kuna da ala a dashi me zai hana baza ka yi convincing insa ya auri Narma ba?." Abiy ya yi murmushi ya ce, "To Senator ni da ba mahaifinsa ba ta ya zan iya saka shi ya auri Narma?." Dad ya ce, "ai bazai manta da abinda ka yi masa ba shima, zai iya amincewa ya aureta ta silar kyautatawar da ka yi masa. Captain ka yi min wannna alfarmar don Allah, na rasa ya zanyi ne, Narma na gab da rasa hankalinta a kansa. In ba dan Narma da take cikin tsananin ciwo da azaba ba wallahi da hakan bai faru ba." Abiy ya yi ajiyar zuciya yana murmushi dan ya san Sen bai san Nayla yake aure ba, ya kalli Dad ya ce, "To zan yi masa waya na kira shi, in yana da lokaci yazo mu yi magana a kai, in ya amince zan sanar da kai, in bai amince ba sai ayi ha uri." "Zai ma amince Captain, na gode sosai." "Babu komai. Amma da ka hana shi aurenta har kana cewa asiri ya yi mata, amma yanzu kuma kana cewa ya aureta, meyasa da ka hana shi yanzu zaka bashi?." "To ya zanyi Captain? Ai tana sonsa ne. Kuma rayuwarsa ta baya ai ba irin wannan ba ce, yanzu yana da babban matsayi, ya kai wani mataki da zai iya aurenta." Abiy ya yi murmushi yana jinjina arfin hali irin na Sen kana ya ce, "Shikenan, zan kira shi zuwa anjima in sha Allah." Dad ya godewa Abiy daga nan suka yi sallama ya tafi. A angaren Omar yana zaune shida Didi Abiy ya kira Omar. Omar ya auki wayar yana kallon Didi ya ce,
Chapter 164 · 0% Book details