Sashe 187
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suna zaune da Nayla da Marmerh da Musliha kamar ko yaushe. Omar ya yi shiru ya jingina da kujera yana kallon sa, Musliha tana kwance a irjinsa, Nayla tana zaune a gefensa ita da Marmerh da take ta game a waya. Nayla ta bishi da kallo, sai su kwashe awa aya a haka indai ba ita tayi magana ba bazai ce komai ba, ya takure rayuwarsa sosai, ya koma zaman ka aici ba ko yaushe yake yin magana ba. Gani yake kamar farin ciki da walwalarsa ta tafi, gani yake tunda ya rasa Didi murmushi ya are a rayuwarsa. Kowa ya san shi aka yiwa mutuwa, duk wanda zai yi kewar Didi a bayansa yake, shiyasa ya koma kamar ruwa ko yaushe ciki bin asa yake yana kwanciya. Shiyasa dangi da an uwa suka dage da yi masa addu'a, dan lamarin nasa sai an ha a da ro on Allah. A ranar ne ya sakko daga sama ya zauna a falo, amma kullum yana sama, saman ma a cikin akinsa. A sanyaye ta ce, "YaMar." Ya sauke kai asa ya kalle ta bai amsa ba, ta langwa ar da kai ta ce, "tun azu nake magana baka ji." Ya gyara zaman Musliha a jikinsa ya kalle ta ya ce, "Ban ji ki ba." "Ta ya zaka ji ni kana tunani?." Ya sauke numfashi bai ce komai ba. Nayla ta ce, "Ka cigaba da ha uri, kar tunani ya jawo maka ciwo. Kaga likita ya ce dole ka cire damuwa, jininka ya i dawowa normal, sannan ga ciwon kan da ka ke fama dashi. Nauyin da ka ke ji a irjinka shima ance damuwa ce, in baka yi arin kawar da ita ba zata jawo ciwo babba" ta arasa fa a a sanyaye tana kallon sa. Ya kalle ta suka ha a ido ya ce, "Kin ta a rasa wanda ki ke so Jidda?." Nayla ta kalli idanunsa ta ce, "Na rasa mahaifiyata, na rasa Didi." Yayi murmushi ya ce, "Mahaifiyarki daman baki rayu da ita ba, kai tsaye zan iya cewa baki santa ba. Baza ki orar da zafin rashin wanda ka ke so a kanta ba. Duk da mahaifiya ce, ko baka tashi ka santa ba rashinta yana ta a zuciya. Nima ban san tawa mahaifiyar ba, amma ina jin zafin rashinta a kusa dani." Nayla ta bishi da kallo ganin yana an murmushi ya ce, "Na san kina son Didi, kina aunarta sosai, zaki ji zafi da ciwon rashinta a zuciyarki. Amma baza ki orar da acin mutuwa akan Didi ba, zaki orar da zafinta ne a lokacin da kika rasa makusantanki Ya fa a tana lumshe ido tare da jan numfashi, ya sauke numfashi ya bu e ido ya kalle ta ya ce, "zaki ana zafin rashin wanda ka ke auna ne in aka wayi gari na mutu na barki, daga lokacin zaki tabbatar da ba aramar juriyar rasa Didi nake yi ba. Juriyar da nayi baza ki iya irinta ba, ko rabin jurewar da nake yi baza ki iya ba Jidda!. Yanzu duk abinda zan fa a miki baza ki fahimta ba, kina kallona a matsayin wanda ya kasa kar addara kawai, ba ke ka ai ba, kusan kowa a haka yake kallona. Na yi miki uzuri, baki san acin mutuwa ba!. Nayla ta sauke numfashi ta sunkuyar da kai, ta mayar da hawayen da suke arin sakko mata, dan yanzu ya zama mai raguwar zuciya, ko ya tayi hawaye a gabansa sai ya tayata, baya iya ri e kansa ko ka an, indai ya tuna da Didi sai ya zubar da hawaye. Saboda haka ko da taji kukan rashin Didi bata yi a kusa dashi, zata ta tashi ta kulle kanta a ban aki tayi kuka ta wanke fuska ta fito. Yana bu atar kulawa saboda har lokacin jininsa bai sauka yadda ake so ba, ga nauyin da irjinsa yake masa, ga ciwon kai da yake fama dashi kullum. Sai da ta mayar da hawayen ta ago ta ce, "Haka jarabawar Allah take, akwai zafi da ciwo da ra i. Sai dai mu yi fatan Allah ya bamu ikon cinye ta ba tare da kuskure ba." Ya lumshe ido ya ce, "Amin Jidda. Akwai ciwo, akwai ra i kam sosai. Shiyasa bana fatan ki riga ni barin duniya, in sha Allah ni zan tafi na bar ki." Nayla ta yi shiru bata ce komai ba dan muryar ta tayi rauni sosai, ta ja numfashi ta jingina da kujera tana shafa kan Marmerh da take ta game cikin nisha Omar ya sake sauke numfashi ya kalle ta ya ce, "Jidda." Ta kalle shi ba tare da ta amsa ba ya ce, "na manta ban fa a miki ba, gobe zamu tafi umrah in sha Allah, zan je na yiwa iyayena da Didi addu'a." Nayla ta girgiza kai ta ce, "Allah ya nuna mana goben lafiya." "Amin ya rabbi. Kin san meye?." Ta girgiza kai alamun a'a, ya gyara zama ya ce, "tun azu nake so na fa a miki sai na manta. Na yi mafarki da Didi cikin kyakykyawan yanayi, tana fa a min duk addu'ar da nake mata tana zuwa inda take" ya fa a yana kallonta da murmushi. Nayla ta ce, "ikon Allah, nima nayi mafarki da ita YaMar. Wai a mafarkin kana ta tafiya baka yi mata magana, sai take cemin kalle shi sai fushi yake yi akan yana gaishe ni bana amsawa, kuma fa Nayla ina amsawa ji ne baya yi, amma yanzu na fa a miki ki fa a masa ina amsawa. Bana haddace mafarki in nayi, kafin na tashi daga bacci na manta. Amma wannan har hango shi nake yi a idona." Lokaci aya fuskarsa ta washe zuwa annuri da farin ciki, ya gyara zama cikin farin ciin da ta jima bata gani a kan fuskarsa ba ta ce, "Da gaske?." Ta yi murmushi ganin shima murmushin yake yi ta ce, "Wallahi da gaske nake." Ya ri o hannunta ta matso kusa dashi ya ce, "na jima ban ji labarin da ya yi min da i kamar wannan ba, kin ga hakan yana nufin addu'ar da nake yi mata tana zuwa gareta ko?." Ta aga kai alamun eh, ya yi mata pecking inta a goshi ya ce, "Naji da i sosai Jidda." Murmushi ta yi yana kallon sa, ya ce, "Kin san ne nake ku uri a raina?." Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "Su Umma nake so na kai umrah, da Umma da Mama da Anty Aisha. Ya ki ka gani? A ha asu dasu Kawu?." Nayla da murmushin jin da i ta ce, "YaMar indai akwai dama a ha a dasu kawai, ladan da za a samu wanda zai je har kabarin iyayenmu da Didi." Ya girgiza kai cikin gamsuwa ya ce, "in sha Allah zan yi hakan. Har su Bashir nake so su je, da nayi niyar mu tafi da Bashir to in bana nan shine akan komai, ya fisu ilimi da wayewa, yana kuma saurin aukar abu in aka koya masa shiyasa nake iya bar masa komai. In muka dawo sai yaje, in ya dawo sai biyun su je su ma. an amanata ne, tun muna marasa jin magana muke tare har yanzu." Nayla da take ta murmushin jin da i ganin ya kawar da damuwar kamar ba shi ba ta ce, "Allah ya cigaba da bu a maka a rayuwarka, baza ka ta a yin baya ba saboda kyautatawa na asan ka da ka ke yi. Rashin Didi ya saka ka manta komai da ya wuce, gashi kana udirin alkhairin da ladansa zai je har inda take ya same ta." Murmushi ya sake yi yana ri e da hannunta har lokacin. Ya ce, "Haka ne Jidda. Tabbas da ace Didi tana da rai da babu dalilin da zai saka na kalle su..." sai ya girgiza bai arasa maganar ba ya canja wata ya ce, "sai mijin Didi, ina so na shigo dashi cikin harkar kasuwancina, duk da yana aikinsa amma ina so na shigo dashi mu cigaba da yin komai tare, ya ki ka gani?." Nayla ta ce, "shawara ce mai kyau, amma ka tuntu e shi ka ji." Ya girgiza kai alamun zai yi hakan. Sallama aka yi tare da shigowa falon, suka amsa a tare suna kallon wacce ta shigo. Narma ce ita da Safna, sanye da hijjabi har asa. Ta tako cikin nutsuwa zuwa cikin falon suka zauna tana kallon su tana murmushi. Narma ta ce, "Ina yini." Nayla ta amsa da fara'a tana kallon ta. Narma ta kalli Omar da tunda ya amsa sallamar ya auke kai ta ce, "Ina yini Omar, ya aka ji da ha urin Didi?." Omar ya ce, "Alhamdu lillah." "Allah ya gafarta mata, Allah yasa ta huta." "Amin ya rabbi. Na gode" ya furta a sanyaye ba tare da ya kalle ta ba . Narma ta ce, "Na so nazo tun lokacin, bana Nigeria kuma ba lafiya ce dani ba, sai da na samu sau i sannan nazo." Jin yayi shiru bai bata amsa ba sai Nayla ta ce, "Babu komai, Allah ya ara miki lafiya, Mun gode da zuwan ki." Narma ta yi murmushi ta ce, "Amin, na gode. Didi Yaya ce a gare mu gaba aya, ta yi min nasihar da ta shiga zuciyata lokaci guda, kuma nayi amfani da ita naga riba mai yawa a rayuwata. Allah ya haskaka kabarinta." A tare suka amsa da amin kafin Nayla ta ce, "bara a kawo muku ruwa." Narma ta ce, "A'a mun gode, akan hanya muke zamu koma Abuja yanzu" ta fa a tana mi ewa tsaye. Ta kalli Omar da ba ita yake kallo ba ta ce, "za a yi aurena cikin kwanakin nan, muna son design na product in ku zamu bayar as souvenirs." Omar ya girgiza kai ya kalle ta ya ce, "Allah ya kaimu, ya sanya alkhairi." Ta amsa da amin ta yi musu sallama suka tafi. Narma tana fita Nayla tayi ajiyar zuciya mai tsaho, Omar ya kalle ta suka ha a ido sai ya aga gira sama, murmushi ta yi dan ta lura a hankali ya fara dawowa Omar insa, addu'ar da ake yi akansa ta fara ratsa shi. Shima murmushin ya yi bai ce komai ba, ya