Sashe 112
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
irin da i ya mamaye zuciyar Narma, ta cigaba da tuno mafarkin tana kallon kanta a madubi. Cikin tsananin farin ciki ta ce, Oh my god! Ta furta da arfi cikin jin da in mafarkin da ta yi. ofar aka yi, ta kalli wacce ta shigo ta ga Mum ce da Najwa. Mum ta tako da sauri ganin tana kallon kanta a madubi tana murmushi. Ta ce, Narma me ya faru?. Narma cikin farin ciki ta ce, Mum i had a dream. Mum da mamaki ta ce, A dream!?. Yes Mum. Nayi mafarki na ga Faruk ina, guess what ? Mum har mun yi aure ta fa a da farin ciki har tana tsalle. Ta sauke ajiyar zuciya ta ce, Mum he hug me, he kissed me, and we sleept together on bed. Mum ina cikin farin ciki sosai, hakan yana nufin zan zama matarsa ko Mum?. Mum ta sauke numfashi ta kalli Najwa da take bakin ofa bata araso ba, ta kalli Narma ta ce, Mafarki ba gaskiya ba ne, kar ki bari wannan mafarkin ya yi tasiri a zuciyarki. Narma ta ata fuska ta ce, Mum! Wannan mafarkin gaskiya, hakan zai faru koda bakwa so. Zan zama matarsa har na haifa mishi baby. Mum ta ce, Alright. Ki kwanta yanzu, ki daina wannan shirmen. Narma ta girgiza kai ta ce, Mum a wannan karon bazan ta a rabuwa dashi ba, zan yi ya i da ko meye zai raba ni dashi wajan na mallake shi. Babu halittar da zata raba ni da Faruk koda shi da kansa ne!. Najwa sai a lokacin ta ce, Sis Please! Ki koma ki cigaba da mafarkin, da alama mafarkin ya fi saka ki farin ciki. Good night ta fa a tana barin akin. Mum ta kalli Narma ta ce, ki kwanta Narma. Ba bacci zan yi ba. Me zaki yi?. Zan kalli Kdrama. Da mamaki Mum ta ke binta ds kallo, rabon da taga tana kallo har ta manta. Ta girgiza kai ta ce, Really!. Narma ta ce, Yes Mum, ina cikin farin ciki sosai, a jikina nake jin zan mallaki Faruk a matsayin mijina ta fa a tana jawo laptop ta kunna ta hau kan gado ta fara kallo. Mum ta bita da kallo kafim ta kashe mata hasken akin ta fita tana mamakin wannan asiri da Tiger ya yiwa arta. Narma bayan Mum ta fita waya ta auka ta kirw number Omar amma kamar ko yaushe bata shiga. Ajiyar zuciya ta yi a bayyane ta ce, dole na samo new sim card, ina son magana dashi da gaggawa. Ta shiga gallary tana kallon hoton da ta ta a yi masa, tayi kissing hoton tana zooming bakinsa tayi kissing bakinsa ta ce, I know you love me Faruk. I know you feel what I'm feeling for you. I'll get back to you very quickly. Very soon, you'll kiss me in reality, not just in dreams. Ina sonka! Ta fa a tana shafa fuskarsa. Misalin arfe aya na dare tana kwance a jikinsa a cikin blanket yana shafa kanta a hankali. Ta gama guje-gujen kunyar ta gashi, dan ta san baya so ta ce kunya take ji dole take daurewa. A sanyaye ta ce, "YaMar na tashi da azumi gobe?." Da sauri ya bu e ido ya kalle ta cikin arancin hasken akin ya ce, "Azumi?." Ta aga kai alamun eh ya ce, "A'a, ban zo nan dan ki yi azumi ba." Kamar zata yi kuka ta ce, "Amma YaMar na saba da azumin nan, in ban yi bana jin da i, Ka bari na yi goben ka ji...!" Ta arasa fa a a shagwa Ya girgiza kai ya ce, "A'a baza ki yi ba fa." "To meyasa?." "Za a dinga karya shi ne da gangan." "To in ka san ina azumi ai....." "Shiiii! Jidda baza ki yi azumi gobe ba, ki bari sai lokacin da naga zan iya barin ki sai ki yi. Amma nan kusa ki daina kawo maganarsa." Zata yi magana ya hanata ta hanyar ha e bakinsa da nata ya cigaba da nuna mata auna. Da safe da ta farka ta tarar dashi yana press up, tana daga zaune a kan gadon ta kalle shi ta ce, "Rouhii nima zan yi." Ya kalle ta ba tare da ya tsaya ba ya ce, "ba zaki iya ba." Cikin shagwa a ta ce, "ni dai ina so." Ya dakata ya kalle ta ya ce, "zo." Ba musu ta sakko daga kan gadon, kafin ya yi magana sai ta ce, "na hau bayanka ka yi dani?." Kallon ta yake yi sai ya aga mata gira. Da sauri ta arasa bayansa ta kan bayansa ta ce, "in na allaka babu ruwana" ta fa a tana dariya. Dariya ya yi ya ce, "in kin alla ni in ke zaki yi jinya" ya fa a yana cigaba da abinda yake yi tana zaune a bayansa. Dariya take yi cikin farin ciki ta ce, "kuma baka gaji ba? Ina da nauyi fa." Ganin ya yi mata shiru sai ta fara yi masa chakulkuli. Dole ya dakata ta yi dariya mai shewa bata ce komai ba. Sakkowa tayi daga bayansa shi kuma ya mi e akan guiwarsa yana kallon ta. Ya zuba mata ido yana kallon ta bai ce komai ba, ta auke kai daga kallonsa ta ce, "Shi press up in da ka ke yi me amfaninsa?." Ya mi a mata hannu ya ce, "zo sai na fa a miki." Ta ma ale kafa a ta ce, "na i wayon." Murmushi ya yi ya cigaba da abinda yake yi. arasowa tayi ta kwanta a inda yake, ta saka kanta a daidai inda fuskarsa take sauka in ya yi asa. Sai ya zama in ya yi asa bakinsa yana ta a nata kamar pecking inta. Sai da ta gaji sannan ta tashi ta ce wanka zata yi, tana shiga ban akin ya bi bayanta. Kwana biyu suka yi a hotel in ko fita bata yi ba, shine dai yake fita ya kawo musu abinci su ci su kwanta shine akwai aikinsu. Ta ji da in zaman hotel in matu a dan ya yi mata da i ta sake samun kusanci da soyayyar mijinta. Duk da wahalar da ita yake yi baya bari ta huta ko ka an, amma hakan ya yi mata da i ta san duk cikin so ne. Shima kansa ya ji da i zaman hotel in ya yi masa da i sosai ya samu farin ciki fiye da yadda yake tunani, sai yake ji ina ma kar su bar hotel in amma dole su bari saboda yana da ayyukan yi. Ranar Friday sai dare suka bar hotel in daga nan suka wuce gidan Didi. Didi ta ji da in ganin su, yadda suka canja kai da ka gansu ka san suna cikin farin ciki. Ta dinga murna ta rasa inda zata saka ranta saboda murna. Omar shima kallon ta kawai yake yi yana murmushi, yana ji da Didi Allah ya sani, yana so ya ga tana farin ciki mai yawa, yana so ya sakata dariya sosai. A lokacin ya auko aramar cover a aljihunsa ya ri e hannun Didi ya saka mata a ciki ya ce, "in kika furta wata kalma kuma ke da Allah." Didi ta yi dariya ta bu e hannunta ga cover ce irin ta an kunnen gold, ta bu e ta ga an kunne ne na gold mai madaidaicin girma. Hannunta na rawa ta auki receipt in ta bu e ta ga ku an kunnen ta kalle shi ta ce, "Omar!." "Shiii! Na ce miki kar ki ce min komai don Allah, ni ba ke na siyawa ba Marmerh na siyawa, in uba ya yiwa ar shi abu ba a magana, don Allah ki yale ni" ya fa a yana tashi ya fita. Didi ta fashe da kukan farin ciki ta kalli mijinta da yake murmushi ta ce, " an kunnen gold ne fa Yalla ai, gold fa." AbdulHamid ya yi murmushi ya ce, "Addu'a zaki yi masa na samun bu i a rayuwarsa ba kuka ba, duk abinda Omar ya samu kin san zai iya mallaka miki shi, kin cancanci ya siya miki gold in ne shiyasa ya siya miki. Kin san zai iya baki duk abinda ya san zaki yi farin ciki. Ki yi masa addu'a ba kuka ba." Didi ta kalli Nayla ta ce, "Nayla na rasa me zan cewa mijinki, na rasa me zan ce wallahi." Nayla ta ce, "ba sai kin ce komai ba Didi, iya farin cikin da kika yi shima wani abu ne. Bashi da wacce ta fiki Didi. Ke uwa ce, ke uba ce, ke awa ce, kuma Yaya ce a gare shi. In bai kyautata miki ba wa zai kyautatawa?." "Amma Nayla akwai abubuwa da yawa a gabansa, ya zai kwashe ku i ya siyo min gold?." "Tunda ki ka ga ya yi ya san abinda yake dashi ne. Don Allah ki daina kuka Didi, in kina kuka zai ga kamar baki murna ba." Ta goge idonta ta ce, "bara na je na same shi." Nayla ta ce, "A'a Didi, ki bar shi kawai kar ki gode tunda ya ce baya so." Didi ta ce, "Amma Nayla ta ya zan kasa gode masa?." "Ya san kin gode in ai, saboda haka ya ce miki shi Marmerh ya bawa, baya so ki yi masa godiya shiyasa ya ce ba ke ya bawa ba, don Allah ki yale shi kawai." Didi ta zauna tana goge ido tana sake kallon an kunnen cikin farin ciki. Nayla fita tayi kamar yadda ya fita, Didi ta biyo bayan ta suka same shi a zaune a mota da Marmerh a hannunsa. Ganin sun fito sai ya fito ya bawa Didi ita AbdulHamid ya ce, "Omar Allah ya cigaba da shiga lamarinka, Mun gode sosai." "Abokinka mai gida, har ka turo min number sa" ya fa a yana kallonsa ba tare da ya bashi waccan amsar ba. Abdulhamid ya ce, "yi ha uri na manta ne." Omar ya ce, "hmmm matarka ta koya maka halin oye- oye, tashi zamu yi daga gidan nan da lokaci ka an, bazan cigaba da zama a gidan da ake yi min alfarma ba." Didi dai tana tsaye tana kallonsa tana murmushi