Sashe 96
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce, "Haka ne Omar, muna mutunci dashi sosai shiyasa ya yi haka." "To ban nema ba, bana so ko ka an, ni na tsani ace za a yi min alfamar a rayuwata. Nan gaba tsaf za a yi min gori, gwara maganin kada ayi kada a fara. Bani number shi" ya fa a yana auko waya a aljihunsa har lokacin Marmerh tana hannunsa. AbdulHamid ya kalli Didi alamun kin ga maganin masu arya ko kafin ya ce, "Da yake ba ya asar, amma zan turo maka number da yake amfani da ita ta whatsApp." Kallon su yake yi duka su biyun bai ce komai ba. Didi da ta san kallon na meye sai ta ce, "ka daina zuba min wannan idanunun naka don Allah, baka yarda ba ne?." Kai tsaye ya ce, "Wallahi ban yarda ba kin ji na ce wallahi, akwai abinda ku ka ulla keda mijinki akan gidan nan." Didi ta ce, "me zamu ulla baka sani ba? Kai a ulla abu ma baka sani ba ai babbar masifa ce. Babu abinda mu ka ulla, gaskiyar kenan." Omar ya ce, "to ha a ni da mai g dan." "Baka ji me ya ce maka ba ne ba? Ba ya Nigeria." "Ko?" Ya tambaya yana kallonta. Gaban Didi ya fa i dan bata son ya gano da wuri ta ce, "eh mana." Yatsunsa ya ora akan goshinsa yana an motsa su a hankali kafin ya kalle ta ya ce, "kin san me? Ni na fara tantama akan gidan gaskiya." Didi ta ce, "ka cika rigima wallahi, to me ka ke tunani bayan wannan? Ka san dai bazan cutar da kai ba" sai ta katse maganar ta ce, "Kai ni na ga kun sake bu e shago, da na gani na ce shine Omar ko labari" ta fa a tana kawar da waccan maganar. Hakan da ta yi ya saka masa zargi a zuciyarsa, ya kafa mata ido yana nazari ita kuma ta i kallonsa. Ganin ya yi shiru bai ce komai ba sai Didi ta ce, "Marmerh ce ma bata an jin da i, gobe zan kai ta asibiti." Sai kuwa ya kalle ta ya ce, "me ya same ta?." Didi ta ce, "mura take yi, kuma an yawon da muka yi ne kwana biyu." Ya dafa goshin Marmerh da take hannunsa ya ce, "kuma shine baki kai ta asibitin ba har sai gobe dan mugunta?." Didi ta ce, "Babban asibiti nake son zuwa, kuma ka ga gobe Monday." "Baki da damuwa ne in wani abu ya same ta" ya fa a kai tsaye kamar shine mahaifin yarinyar. Didi ta yi dariya ta kalli Nayla da ta daina magana ta ce, "Nayla kin koma shiru kamar ba ke ba." Murmushi ta yi kawai bata ce komai ba. Omar ya kalli Nayla ya kalli Didi sai ya ce, "Zamu tafi gida." Nayla ta kar i Marmerh a hannunsa suka fita shida AbdulHamid. Didi ta ri o hannun Nayla bayan sun fita ta ce, "Nayla ba ki ga tunda Omar ya shigo Umma ta koma aki ba?." "Na gani Didi." "Duk da daman in yalla ai yana nan ta fi zaman aki, amma yanzu saboda Omar ta koma. Tana tsoron Omar ya yi disgracing inta a gaban sirikinta shiyasa ta koma, wallahi dan ta yiwa Omar magana ya yi mata banza ko ya harareta ka an ne daga cikin halinsa. Nayla zan ora miki wani nauyi, a yanzu Omar bashi da wacce ta fiki, sannan ba shi da wacce yake so kamar ki, bashi da wacce yake ji a zuciyarsa kamar ki. Don Allah ki dinga convincing Omar akan dangin iyayenmu, ki dinga nusar dashi wannan banzar zuciyar da fushin da yake yi dasu babu inda zai kai shi sai dana sani. Yanzu Nayla a duniya muna da wanda suka fi su ne?." Nayla ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "Fuskar Umma Saroot kika kalla zaki tabbatar ita jinin mu ce, amma baya aunarsu gaba aya. Hana rantsuwa ya yi mata godiya ranar da ba ku da lafiya shima kuma ni na ce, amma duk da haka saboda ke ya yi mata godiyar. Na san ta dalilinki zai iya canjawa tunda yana sonki, don Allah ki taimaka min Nayla, wannan ne kawai burina da rage min a duniya a yanzu. Daman burikan nawa bai wuce Omar ya shiryu, ya yi aure, ya zauna dake lafiya ba. Duk Allah ya cika min wa annan, wannan burin kawai ya rage min Nayla." Nayla ta ce, "Didi anya zan iya? Kin san halinsa sarai, nima ba yale ni zai yi ba." "Ke fa mace ce, kin san ta yadda zaki je masa da maganar, kin kuma san a daidai lokacin da zaki yi masa maganar. Koda ya yi fushin dake akan maganar zai sakko saboda tasirinki a gare shi. In kina yi masa maganar yana yin fushi wata rana zai daina. in ya yi fa an yau, ya yi gobe, jibi bazai yi ba. Ina jin tsoron na bar duniya ba tare da Omar ya gyara zumuncin dake tsakaninsa da iyayensa ba, shine kawai burina a yanzu, ki taimaka ki cika min shi Nayla. Yana sonki, zai ji maganar ki sama da maganar kowa a duniya. Ba iyaye ne dashi ba balle a ce zai ji maganarsu a sama da ta ki, tunda babu su ke ce a kan gaba Nayla." Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, "in sha Allah zan gwada Didi, Allah ya bani iko." "Amin Nayla, mu je na raka ki." Tare suka fito har ofar gidan, ta kar i Marmerh ita kuma ta shiga mota suka tafi. KRB3P056 Tunda suka tafi bai ce komai ba, ta lura maganar Didi akan gidan nan ta an ta a ransa kuma bai yarda da abinda ta ce in ba. Tsaki ya yi ka an ya ce, "Didi tana raina min hankali." Daga nan bai sake cewa komai ba har suka je gida suka tarar da masu gadin gidan suna nan. To masu gadi mana, kullum suna nan sai dai in bai fita da mota ba. Suka bu e gate in ya shiga da motar ta fita ta shiga cikin gidan. i shigo ba sai da ya siyo mata kayan ciye-ciye dan ba su ci abinci ba. Ta ci ka an dan bata son cin abinci da daddare, jikinta na da saurin kar ar ki a amma bashi da saurin kar ar rama. Sai da ta gama ta tashi ta shiga aki ta yi wanka ta saka Pyjamas kamar yadda ta saba kullum, ta zauna a kan gadon tana danna wayarta. Kiransa ne ya shigo wayarta,ta auka kafin ta yi magana ya ce, "zo." Abinda ya furta kenan ya kashe wayar ta tashi ta nufi akin. Tana bu ewa gabanta ya fa i, dan tun ranar da abin nan ya faru bata sake shiga akinsa ba dan tsoron ma akin take ji. Frame in da ta ajjiye yana inda ta bar shi har yanzu, ta kalli wanda ta saka ta ga yadda ya yi kyau a akin sannan ta kalle shi. araso mana" ya furta ba tare da ya kalle ta ba. Yana lura da ita, ya san a tsorace dashi shiyasa take baya baya. Ta ta araso akin bayan ta kulle ofar. A arare ta zauna ta ce, "gani." "Ai na ganki" ya fa a yana cigaba da lissafin da yake yi. Kamar bazai magana ba sai kuma ya ce, "me ya canja ki yau?." Ta kalle shi ta ce, "me ka gani?." "Yau babu taya ni hira kin yi tafiyarki." Nayla ta ce, "na ga kamar ranka a ace yake ne shiyasa." "Ni haka na ce miki? Haka na ke acin rai cikin sau i daman?" Ya fa a yana shan ruwan da yake gefensa ba tare da ya kalle ta. Kafin ta yi magana ya ce, "kawai akwai abinda yake zuciyarki, zo ki fa a min" ya fa a yana ajjiye wayar hannunsa yana mi o mata hannu. Gabanta ya fa i sosai ta runtse ido ta bu e, ta mi a nata hannun a hankali ya ri eta ya araso da ita inda yake ya zaunar da ita a jikinsa ya ce, "fa a min, me ya canja ki yau?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "babu komai." "Ni fa bana son arya Jidda, ki fa a min abinda yake zuciyarki mana" ya fa a yana cire hular kanta ya zame ribbon in kanta gashin ya sauka a fuskarsa ya lumshe ido yana sha hamshin gashi. Nayla ta yi shiru bata ce komai ba dan tsoronsa take ji shiyasa ta kasa sakewa. Hannunsa ta kalla ta ga inda ya one da ruwan zafin har wajen ya yi ba i, ta an shafa wajan sai ya bu e ido ya kalle ta kamar zai magana sai ya share ta dan so yake ya ji ta yi magana. A irjinsa ta kwanta tana sauraron abinda ta fi auna wato bugun zuciyarsa, ta kulle ido dan itama ta ta zuciyar bugawa take yi kamar zata fashe saboda tsoro. Shirun ta ji ya yi yawa bai ce komai ba, shi kuma daga kwance gashinta da ya yi bai sake yi mata komai ba yana dai ri e da ita idanunsa suna kulle. Jin shiru bai sake yi mata wani abu ba sai ta saki jikinta, ta saka a ranta babu abinda zai faru ta ce, "a ina ka samu wannan ciwon? Na san dai babu shi a hannunka." Ba tare da ya bu e ido ba ya ce, "Ranar mu ta farko, daren mu na farko, lokacin mu na farko. A lokacin da nake arin na taimaka miki ruwan zafi ya ta a ni. Na manta akwai water heater a ban akin, hankalina ya gushe burina kawai ki dawo daidai. Na ji da i da na samu tabo, kin ga in dai zan kalle shi zan tuna da wannan dare mai cike da nisha i da ru ani." Nayla bata ce komai ba ta yi shiru dan bata da amsar da zata bashi, lallai kuwa daren ru ani, daren da ta auka a kabari zata wayi gari, bata auka zata cigaba da rayuwa kamar kowa ba. Fa in irin wahalar da ta sha a hannunsa ata baki ne, ita ka ai ta