Sashe 7
Kiran Rabo Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi dariya ya kalli Jalila da ta shigo ya ce, Jalila an dawo? Na auka ke zaki yi zaman aki ai. Dariya tayi suka gaisa da Abiy sannan suka fita ita da Jalil. Abinci Abiy ya auka wanda Mama ta zuba masa ya fara ci. Bai ce komai ba abincinsa yake ci hakan ya saka Mama ta ce, baka ce min ya mu ka baro Nayla ba. Abiy ya kalle ta kafin ya auke kai ya ce, na san ai tana cike da farin cikin auren wanda take so. Mama ta ce, hmmm bari kawai. Duk abubuwan nan da suka faru amma Nayla aunarsa take yi kamar ta busa masa rai. A gaban idanun mu da yayyen mahaifiyarta aka kira shi jiya aka zauna dan aji ta bakinsa. Babban an Hajjan nan da suke cewa Daddy ya ce indai har ya furta baya son zama da Nayla za a warware auren dan baza su bata wanda ba ya son aurenta ba. Yaron nan dan wula anci duk an taru ana jiran sa amma ya shafe mintina talatin bai zo ba, kuma da yazo ana tambayarsa yana bawa mutane amsa ta rainin hankali. arshe idanun wanda ake kira da Daddy ya kalla ya ce shi baya son Nayla ai bai ce a aura masa aure da ita ba, kuma bai ce yana bu atar aurenta ba. In ma yana da ra ayin auren to wata ba Nayla ba. Ni abinda yafi tsaya min a rai da ya ce wacece Nayla, yana nufin bai ma santa ba fa kenan Abiy. Abiy kallon Mama yake yi ta cigaba da cewa, Har sai da anwar marigayiya Sa adatu ta fusata ta ce kai ba fa auren sadaka aka baka ita ba ka ke yiwa mutane maganar banza. Kaga yadda ya yi mata kallon wula anci yana cewa koma meye shi ba ya sonta. Kamar fa ba iyayen matarsa ba, to ko Nayla ba matarsa bace tunda jininka ce ya cancanci ya girmama iyayenta saboda abinda ka yi masa kwanaki. Amma yaron nan bai yi ba sai zallan iskanci a cikinsa. Kaji masifa da bala in da ya dinga yi kamar wasu sa aninsa? Yana shouting yana sake maimaita baya son Nayla. Na ji da i da Jawad ko Yaya basa wajan, dan da abin fa a zai zama wallahi, yanayin yadda yake magana dole ya fusata su. Abiy ya murmusa ya ce, To ai gaskiya ya fa a, ya ce yana sonta in ne?. Haba Abiy, koda baya sonta fa ar wannan kalma a gaban iyayenta ai cin fuska ne. Ba dan Yayarsa Aisha ba wallahi sai ya saki Nayla a jiya. To itace ta ja shi waje suka tattauna sannan ya dawo rai a ace ko kallon kowa baya yi ya ce ya amince. Duk da wannan abin da ya faru ita Nayla bata so ya furta ya saketa, jikinta rawa yake yi da yake cewa baya sonta, amma yana furta ya kar i auren ta yi ajiyar zuciya. Gaskiya na ji babu da i akan abin nan na Nayla, haba don Allah, ana nemar mata anci tana zubawa mutane asa a ido?. Ai sai da na fa a mata azu, na ce ni ban ga abin so a wannan yaron ba, sai tayi dariya wai ita har yanzu son da take masa bai ragu ba Mama ta arasa fa a a fusace. Abiy ya ce, to meye na fusatar? Ki kwantar da hankalinki haka ta za Kasan ko gidan da aka kaita bai je ba har yanzu, ita da Salma suka kwana. Wannan wula alanci har ina? Kuma ita sam bata gani har yanzu haskensa take gani tana kuma sonsa, abin nan ya ta a min zuciya kamar na yi kuka wallahi ta arasa fa a murya har rawa take yi. Abiy ya yi shiru bai ce komai ba amma zuciyarsa sam babu da i da jin abinda Mama ta ke fa a, gaba aya zuciyarsa ta cushe bai ji da in abinda ya faru ba. Mama ta katse masa tunani ta ce, Yanzu batun gwajin jini ake yi, tunda kai ka auketa ka bashi ita ba a san matsayin jininsa ba, Ko yana da hiv ma waye ya sani. Mtsww! ni wallahi gaba aya Nayla ta fi bani haushi a lamarin nan, na san ana nan ana yi dani a dangi ana cewa da yake ba ni na haifeta ba na bari an yi mata irin wannan aure. Ba shiri, ba biki, babu komai an wanke yarinya kamar Nayla an kai masa ko ku in aure babu balle lefe. Duk wanda ya zarge ni shi da Allah, domin na fi su jin zafin wannan abin da ya faru. Abiy murmushi ya yi domin kuwa an zargeta in, dan an uwansa ce masa suka yi dan mahaifiyar yarinya bata raye sai ya yi mata abinda ya ga dama, kuma Mama na zuga shi da yake ba Jidda ce ko Jalila ba. Abiy ya kalle ta ya ce, To yanzu meye na wannan acin ran?. Abiy abin ne da haushi wallahi. Gidan da aka ajjiye Nayla ko mai aikin gidan nan sai haka, wasu ananun da una kamar akurki. addararta kenan. addara da kuma rashin jin magana irin na Nayla ba. Bai ce mata komai ba ya yi shiru amma abubuwan da ta fa a sun yi tasiri sosai a zuciyarsa. Sosai yaji ransa ya aci akan lamarin fiye da tunani, ga shi Nayla ko waya bata yi masa ba, alamu ya nuna ta samu abinda take so ya za a yi ta tuna dashi. Gaba aya sai abincin ma ya fita daga ransa ya ajjiye ya dau i lemo ya sha ya tashi ya shige bedroom. Murmushi Mama tayi bayan ya shiga ta ce, Ba boka, babu malam, babu an bori, babu masu tsibbu na yi abinda nayi niya akan Nayla. Burina ya cika ta shiga gidan da zata sha wahalar raguwar aure, har gwara ni kana sona uwar gidanka ce bata sona, amma ita mijin ma baya sonta. Mu je zuwa mu gani, yanzu na fara saka maka acin rai akan auren nan na Nayla. Mu je zuwa. *Kano.* Omar da acin rai da takaici ya kwana ya tashi, ko yaransa da suka ganshi babu wanda ya iya tanka masa dan kana cewa kanzil zai wuce a kanka ko waye kai ko ya ki ke dashi. Washe gari ranar lahadi da wuri ya fita company ya je ya samu ana ta aikin takalma kamar ko yaushe, gefe aya kuma ana saka wasu a kwali saboda za a tura garin da aka ce ana so. Bashir da ya ganshi a zaune sai ya arasa ya zauna ya ce, Barka da zuwa Tiger. Daman Kai mu ke jira akwai abinda ya are ana bu atarsa da gaggawa. ago ido ya yi ya kalle shi sai Bash ya saukar da kai asa ganin idanun mai gidan nasa yana gani ka san baya cikin walwala. Atm insa ya bashi ya ce, ku je a siya, in ka dawo ka zo gida ka same ni ya fa a yana tashi ya fita su kuma suka cigaba da aiki. Gida ya koma kawai ya zauna ba tare da yana yin wani abun ba, gaba aya komai ya fice masa daga rai baya jin da in komai ba kuma ya jin da in aikata komai. Zuciyarsa babu da i haka yake ji, kamar wanda ya rasa wani abu mai mahimmaci a rayuwarsa haka yake ji. Ya kasa mantawa da batun auren nan, duk yadda ya so da ya ajjiye maganar ya kasa, ko ya ya ya motsa sai ya tuna yanzu fa yana da mata, in ya kawar da tunanin anjima zai sake dawowa cikin kansa. Tsaki ya yi a bayyane, ko a lokacin Narma bai ji wannan nauyin zuciyar da yake ji a yanzu ba. Ya karkata hakan ga acin ran da maganar ta saka masa shiyasa da ya tuna sai ya ja tsaki. Bashir ne ya shigo suka gama magana, Omarya aike shi shi kuma ya kwanta akan kujera ya rasa abinda yake masa da Bacci ne ya kwashe shi a haka sai kiran sallar azahar ya ji, ya tashi ya yi sallah yana tunanin abinda ya kamata ace ya ci. Kitchen in ya shiga yana arewa komai na ciki kallo, sai kuma ya ja tsaki ya fito ya auki ruwa yana sha cike da jin haushi. Sai kuma ya kuma tashi ya dafa shayi ya dawo yana sha ba tare da ya saka madara ko wani abun ba. Bayan sallar la asar Bashir da Tk suka shiga wajansa, yana kwance da ya gansu sai ya mi e ya ce, Ya aka yi?. Tk ya ce, Tiger kayan da aka tura Abia state ne wai basu je ba, shine nake tambaya mai motar bai yi maka waya ba?. Omar ya ce, Kamar ya basu je ba? Ni babu wanda ya kira ni ya fa a yana duba wayarsa amma bai gani ba. Tk ya ce, wanda aka turawa kayan ne ya kira ni ya ce driver bai je ba har yanzu, na kira driver a waya kuma baya auka amma bara Maganar ta katse saboda ganin kiran mai motar sai ya ce, gashi ma yana waya. Ya fa a yana auka suka yi magana kafin ya kashe ya ce, Yauwa, ya ce yanzu nan ya shiga garin zai kai masa nan da anjima ka Shiru ya yi baice komai ba. Bashir ya ce, Damisa Didi ta sanar damu aurenka. ago ido ya yi ya kalle shi sai ya sunkuyar da kai yana sosa kai ya ce, Tuba nake Damisa, babbar Yaya ce ta sanar dani shiyasa na amince da batun. Kuma ta saka har a masallaci an sanar da maganar. Da mamaki ya ce, a masallaci?. kwari Boss, dan yanzu mutanen unguwa duk sun shaida. aramin tsaki ya yi bai ce komai ba Bashir ya ce, Allah ya sanya albarka Boss, mun so ranar auren ka ayi shagali na gaske, ranar Kano ta san da zaman mu wallahi tallahi. Da ranar kaf unguwar nan sun huta siyan maganin sauro, saboda zamu yiwa unguwar haya i da ganye mai albarka Boss. Amma hakan ma normal ne, sai dai ba mu san Anty na mu ba. Bash ka